TSARABAR KANO..!!

Abunda yafaru Dani zuwa na da dawowa ta



________________________
A safiyar Ranar Alhamis ne 29-8-2019 nayi Shiri tsaf na dauki jakata na nufi tashar mota dake cikin garin shinkafi domin halarta Mu'utamar Ko ince Taron karawa juna sani na wuni biyu da Shafin Nan na Ma'asumah Mai farin jini yake shiryawa Wakilan shi Wanda wannan NE Karo na biyu a  garin Kano, bayan anyi na farko a garin katsina
.
Bayan zuwana Tasha mota cikin kankanin lokaci tacika nabar garin Shinkafi da karfe 12:30 na Rana, bayan doguwar tafiya akan kwalta da motar mu keta keta iska da nufin takai cikin birnin Kano sai  muka tsaya a garin gusau  mukayi Sallah Azzahar Sannan muka Kara shillawa, Tafiyar mintuna 15 ba muyi ba dai-dai wani gari da ake cewa kwatarkwashi muka hadu da Accident sanadin Over taking da wani yayi Mana,

Bamu sarar ba sai muka ga motarmu ta keta Daji ta nufi wani makeken dutse Kuma a gefen dutsen akwai wani makeken rame a gefe Daya Kuma wasu mutanene ke saran itace , ganin motar ta haro wajen sai suka fara hailala domin sunyi yakinin inda motar ta nufo dayanmu  bazai taba rayuwa ba.

Nidai Ina gefen mota dayake motar kirar Nan CE da bahaushe ke cewa: SHARUN , Kuma gamu cikinta Kuma ta nufo wannan dutse ko rame , dukkan hankalin kowa yatashi acikin motar Wasu hailala Wasu salatin Annabi da dukkan Wasu furuci Daya fito ba bakinsu, Wasu sun dafe kansu, sun runtse idanun su suna jiran sakamako a wurin Allah. Nidai kawai ba Abunda nakeyi illah Kiran sunan imamai da Wasu Addu'o'i nima dai Ina jiran nawa sakamako.




Kwatsam sai mukaga direban cikin iyawar Allah ya juya da motar da karfi tayar motar Daya ta bigi wani Dutse ta fita, tana fita sai dayan tayar ta sunkuya da nufin mufada rame Amma Kuma Allah Bai nufa ba , karawarta gaba keda wuya muka bigi wani makeken sanadin hakan mutun Daya ya rasa ransa wasu sunsamu kariya inda mukam  muka fita sai dai buguwa da izinin Allah.


Bayan hadari Ni da Wasu Wadanda basusamu muggan raunuka ba muka chanza mota sai birnin Kano.

Munshiga Kano da daddare ana ta tsala ruwan sama Wanda a ranar tunda 12:00 aketayin su  inji Dan adaidatan Daya daukeni, dayake Wannan zuwan shine Karo na farko na shiga ta  Kano, Bayan nasauka a Kabuga na biya Dan adaidata nahau aka kaini rijiyar lemu kamar yadda Zaidu Suleman ya ceman anan zan sameshi bayan Kiran waya da muke tayi dashi har Dan adaidata ya ajiye Ni....

Nasan bakuji farin cikin danaji ba Bayan danayi katari da mutane biyu sunfito tarbana  cikin ruwan sama ga sanyi, a lokacin ne nakara yiwa Allah gdy akan baiwar Da yayimana ta zamowar mu masu amsa da'awar da  Wannan jagora Sayeed (h) yake Kira akai..

Bayan karbar jakata muka nufi masaukina Muna tafe suna dubani ko na samu rauni  kamar zasu hadiyeni akan labarin da sukaji na samun hadarin danayi a hanya, Sukace sai munje An dubani dole kafin mukarasa masauki, (Yan Uwa Kenan) Bayan karbar magani da nayi mukaje masaukin cikin raha da farin cikin haduwa da juna Muna cikin Hakan Madan (Uwar gidan) ta matsawa Zaidu Suleman Shi'a sai yakaraso gida sbd Rashin lafiyar dake damunta, Wayyo illahy ya Bata lfy Alfarmar Sayyadah ma'asumah (as), 

Ba cikin son ranshi ba yabarmu da katon Tazuru n nan Auwal Yusuf muhammad don kawai ba yadda zaiyi, ya hakura ya tafi. Auwal Yusuf Muhammad ne yaci gaba da dawainiya Dani har zuwa wayewar gari inda bayan kimtsawa muka fita filin program a ranar jumu'a 30-8-2019 domin shirye-shirye kafin baki dake Kan hanya su karaso.

Ko Ina kaduba a ranar bakine keta zuwa inajin da idona Naga mutanen
Malunfashi
Yola
Katsina 
Daura
Zariya
kazaure
Shinkafi
Kaduna
Udawa
Azare
Ningi
Kano
Niger 
Sokoto
Shinkafi
Gusau
Kai bari incema da sauransu domin bazan iya zanowa ba.... Anyi program a ranar Daren jumu'a inda mas'udu Dan Masani Shinkafi ya gabatar, Sai a ranar Assabar da safe Shugaban INTERNET FROUM Na na kasa Ibrahim daurawa ya gabatar da nasa jawabi sai Ado Isa guda sai Zaidu Suleman Shi'a sai Ammar sabo Atc sai sauran Wakilanmu...


MLM Ibrahim daurawa Yana jawabi


Mas'udu Dan Masani Shinkafi tare da mlm Ibrahim daurawa da wakilanmu sistoci


Alhammunsha ilimumuka daban daban, Kuma Alhamd ansamu kyaututuka inda wadannan kyautuka kowa yayima kowa Bakin gwargwadon karfinshi domin Kulla zumunci a tsakankanin mu,  a tanawa janibin na samu kyaututuka a takaice kamar haka:-

Na samu kyautar Zanannen Photon Imam Aliy (as da Salisu mazaje ya zana da hannun shi kuma yabani. Godiya dubu

Sai Kautar da Ado Isa guda yabani ta manya-Manyan littafai NOT BOOK goda daya yaba shafin  Ma'asumah guda biyu. Godiya dubu.

Sai Sadiq Shi'a Jega shima yabani kyautar Yadi biyar na Shadda da Kuma baiwa wannan shafin na Ma'asumah yadi goma biyar Shadda biyar yadi. Godiya dubu


Sai Cmred nazerr  sa'idu gusau daya bani Kyautar naira 1000 tare da Daukar nauyin wannan Wakar ta shafin Ma'asumah da mawakinmu yayi na abuga ta...godiya sau dubu

Abbakar ibrahim da Mas'udu Dan Masani yare da Comred nazeer


Sai Ishaq Sagir magaji ba karamin tunane yasakaba shima a kyautarshi inda yayi key walda na saka makullai Mai photon logon Ma'asumah, godiya dubu.

Abubakar Ibrahim kudan yabani kyautar wasu Muhimman littafai guda biyu masu gayar muhimmanci a garane illahy ya saka.

Muhammad Dan Sudan azare shima yaman kyautar littafi na Sayeed (h). godiya dubu

Sai Zaidu Suleman Shi'a shi Kuma na samu kyautar dater 1Gb da yayi alakawarin zai turoman dama Wasu Amma kowa yaji elert Ni har yanzu tanakan hanya. Gdy dubu

Da sauran Muhimman kyaututuka davan fadaba illahy ya Kara Arziki ya kuma Kara kusanci yabar zumunci ya nuna Mana wani lokacin.

Bayan Kammala program cikin tsari da lizami munsha ilimumuka munkoyi wasu Muhimman hanyoyin da zamuyi amfani dasu a kafar sada zumunta social media da yadda Zamu zamo nagartattun Mutane jakadu.

Munkoya mungani munji Duka.

A ranar lahadi ne aka rufe program Bayan shauki da yasa wasunmu koke koke wasu Kuma da kaduba fuskarsu badadi Kai abun zabban tausayi bamaison rabuwa Da juna, haka aka daure kowa yakama hanyar garinsu Rai Bai so ba...

Bayan kowa ya watse muma muka watse muka nufi rijiyar lemu ni da Auwal m Tukur da Zaidu Suleman Shi'a da Auwal Yusuf Muhammad da Ishaq Sagir magaji da Yahayya isah (Muslim) da Shana islam da sakina Ahmad. Bayan munje sakina da Ishaq suka shiga mota guda suka shillah (Wayyo). Mukuma anan mukayi Salloli nayi wanka Suka kawomana abunci da abun sha muka kimtsa duk da bagurasa aciki...... Duk dayake Auwal yace mudan Kara hakuri mudada hakuri Kuma muci gaba da hakuri gurasa zata zo Mana a program na gaba.


Bayan Mun kimtsa misalin karfe 4:00 na ranar lahadi suka rakamu mukahau tasi har hawaye nayi sbd shauki da wadannan Jaruman Yan uwan ,sai Kabuga, MLM Zaidu da MLM Auwal Yusuf Muhammad da Alkasim da Muftahu dss muna godiya illahy ya saka da Alkhairy abisa dawainiyar da kukayi damu da bazata fadu acikin rubutuna ba , mungode Allah ya faranta da fitowar Jagoran mu.

Bayan zuwanmu Kabuga mukahau motar Malunfashi Kai tsaye domin munga yanayin dare zai Mana a hanya muka yanke shawarar Kiran mudasir muka sanar dashi.... 

Bayan munje nida Yahayya Muslim  tun a Bakin Tasha muka gansu sunzo tarbarmu shi mudasir da naseer. yababa Malunfashi, Allahu Akbar ko a wancan karon zuwana na farko ba karamin. Riritani sukayi bakamar kwai akan cokali, wannan ma karon ba Abunda zance sai dai godiya kawai...

A ranar da muka shiga Malunfashi a ranar aka fara zaman makokin imam Husaini (as) inda muka zauna har mlm Yahayya yashiga a Tamsiliyya da kuma rero waken juyayi a wajen, Bayan kammalawa mukaja girkin da Naga Asiya tazo Mana dashi abun sai Wanda yaci ga kuma biredi da tea abun dai ba'a magana mukaci mukasha muka kwanta bayan watse taro.

A safiyar litinin mukayi shooting na comedy Ukku Wanda zasu fara fitowa cikin satinnan daga ciki akwai.

*WATA YAR UWA*

*GWARGWADON BUHARIN KA GWARGWADON WAHALARKA*

*NAKOWA NE*

Sunanan Tafe.........

Bayan kammalawa dayin wasu Abubuwa muka hau mota da misalin karfe 3:30 na Rana muka nufi FUNTUA daganan mukahau motar gusau munzo gusau da misalin karfe 7:00 na dare ana magriba, Bayan saukarmu sai muka yanke shawarar mukira Comred Nazeeru gusau domin yanayin hanyar tamu da Babu kyau har munsanar dashi Kuma mukaga mota duk dayake munsamu zaman sulhu a Zamfara sakamakon acan baya idan karfe 4:00 na Rana anrufe hanyar saidai Kuma wata safiyar saboda sace-sace da dauke&dauke Amma yanzu Alhamd.

Bayan munsamu mota muka Kira nazerr muka gayamai mu mun wuce duk dayayi murna saukadin Amma naji yanayin baiji dadiba a lokacin da Zamu wuce, sai Amana afuwa mungode mlm nazeeer ai ana tare.

Mota tacika muka shillo har shinkafi da misalin karfe 9:40 na dare.
 Alhamd Alhamd Alhamd Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Daya bamu ikon tafiya lafiya da dawowa lafiya da Kuma Samun nasarar wannan program da mukayi.

Kuma Ina godiya ga dukkan Wakilan mu da mukayi musharaka dasu a wajen wannan taro Wanda sai dai muce Zamu jajantawa Wanda baizo ba illahy yayi maku albarka yabar zumunci yasa agaba muyi Su Sayeed (h) na tare damu.

Su Kuma Wadanda basuje ba sbd uzurori mabanbanta illahy ya karfafesu ya dafa musu anan gaba ayi dasu.

Illahy ya daukaka wannan  Shafin na Ma'asumah Www.maasumah.com.ng  ya yalwata kirjin wakilanshi, Alfarmar Sayyadah Zahara Ma'asumah (Sa).
Rubutawa...Mas'udu Dan Masani Shinkafi

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post