MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE
A cigaba da gabatar da zaman juyayin ashura da ake gabatarwa a fudiyya kazaure, malam magaji mai wada yace: mushrikai sun sakawa manzo Allah (s) takunkumi ne saboda abubuwa guda biyu, na farko sun so ya zamana addini ya tsaya ne iya Makkah na biyu kuma sun so su takaita addine ne ya zamana ya takaita ga wasu mutane. Malamin yaci gaba da cewa duk da wannan takurawa da manzon Allah ya gamu da ita hakan bai hana Allah tabbatar da addinin sa ba ta inda azzalumai basuyi tsammani ba
Inda yake bada misali da lokacin hijirar sa ta farko da abubuwan da suka faru na dalilin faruwar hijirar har zuwa hijira ta biyu. Har zuwa abinda ya faru a ukaza( kasuwar da manzon Allah) ya hadu da mutanen madina.
Bayan kammala gawabinne aka gabatar da saka sabuwar tuta ta Ashura wadda daliban fudiyya suke sake wa duk munasabobi, daga nan aka gabatar da sallah magaruba da insha'i akayi ziyarar Ashura aka sallami kowa.
*sakina Ahmad kazaure*
Tags:
Munasabobi