LAYYA A FATAWAR SAYYID ALI KHAMNE'I (1).

LAYY
Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai.
Tsira da Aminci su Tabbata ga Manzon Allah da Iyalan Gidansa Tsarkaka.
Salam yan uwa masu albarka.
Kamar yadda muka dauki ganin wata da kuma zakatul fidirah muka yi magana a kansu a dunkule a bisa fatawar Sayyid Ali Khamne'i (Allah ya ja kwanansa), to babu laifi layya ma mu kawo fatawoyin Ka'id din a kanta, wata kila su amfanar.

Abin da ya sa na fara wannan rubutun da wuri, shi ne ina so in kaucewa matsalar da na fuskarta a kan rubutun ganin wata da kuma zakatul fidirah, wadda kuwa ita ce sauri da kuma zallake wasu mas'aloli, wanda da na fara da wuri, to da sai sun fi kammala a kan yadda suka gabata, da fatan Allah (T) zai bani wata dama da zan sake wasu rubuce-rubuce a kansu, musamman ma ganin wata.

Kafin komai ya zama lizam mu bayyanawa dan uwa mai karatu cewa; fatawoyin Ka'id din zamu kawo a wannan rubutun, mafi yawansu mun tura masa da tambayoyi ne a rubuce, shi kuma ya rubuto mana amsa da hannunsa mai albarka, saboda haka a wajen kawo manazarta (masadir) zamu ambaci numbar tambayar ne kawai ba tare da sunan littafi ba.

ABIN DA AKE NUFI DA LAYYA
Mas'ala ta (1): Layya tana nufin mutum daga goma ga watan Zulhajji (ranar babbar salla) har zuwa sha biyu ga wata ya yanka dabba (kamar saniya) da nufin neman kusanci ga Allah (T), koda yake abin da ya fi shi ne yankan ya kasance a ranar salla. Saboda haka:
1. An fi son layya ta kasance a ranar salla.
2. Mutumin da bai samu yi a ranar salla ba, to ya samu ya zo da ita a cikin daya daga cikin kwanaki biyu masu zuwa, wato 11 da kuma 12.

3. Sharadi ne mutum ya yi niyar neman kusanci ga Allah (T) domin ibada ce. Don haka in mutum ya yi da nufin cin nama, ko kar yayansa su gani a makwafta, to ba shi da lada.

4. An fi so a yi ta ne da rana bayan ta sowa daga idi.
MAHIMMANCIN YIN LAYYA
Mas'ala ta (2): Layya tana da mahimmaci sosan gaske.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post