✍️ Aliyu Dahiru Aliyu
Tambayar a nan ita ce, me zai faru da Imam Hussein bai je Karbala ba? Me zai faru da wadanda suke bashi shawarar kada ya fita sun samu nasarar hakurinsa? Abu na farko da za a gane shi ne Imam Hussein bai fita Karbala don neman mulki ba. Shi da kansa ya fada cewa ba shi da bukatar mulkar mutane. To amma me yasa ya fita? Amsar guda daya ce: neman yanci da tabbatar da hakkin al’umma. Yanci shi ne matakin farko a rayuwa. Daga lokacin da baka da yanci to ka rasa rayuwarka. Don haka hakura da rayuwa a neman yanci shi ne mafi girman sadaukarwa da dan Adam zai yiwa kansa.
Da Imam Hussein bai fita neman yanci ba da tuni babu ragowar hanyar da Musulmi zai kubuta daga hannun azzaluman shugabanni da yan kasuwar addini suka kewayesu. Tare da tabbatar da cewa Imam Hussein din ya fita ma amma sai da suka kirkiro hadisan karya da suka nuna cewar ya halatta duk wanda ya fito zanga-zanga a kasheshi. Ya halatta duk wanda ya fito neman yancinsa sarkin garinsu ya kasheshi. To amma me ya faru a lokacin da Mu’awiya ya fito yakar Imam Ali? Sai munafukai suka ce wannan aikin lada ne. Na Imam Hussein hukuncin kisa, na Mu’awiya hukuncin ijtihadi!
Fitar Imam Hussein Karbala ita ta bawa ragowar Musulmi karfin yakar kowane azzalumi da yan hayaniyar wa’azi suka kewaye. Da sunan Imam Hussein mayakan Abbasiyya suka kifar da azzaluman Umawiyya. Da suka zama azzalumai kuma su ma Abbasiyar da sunan Imam Hussein aka kifar da su. Har Fadimiyya da Usmaniyya da sunan Imam Hussein aka kafasu. A haka sunan Imam Hussein ya zama “juyin-juya-hali” a dikin Musulinci. Da babu Karbala da haka zalinci zai ta tabbata babu mai iya tankawa balle har a tunkari azzalumai.
Wadanda suka kashe Imam Hussein sun dauka sun gama da tarihinsa. Amma basu sani ba cewa daga nan suka kafa tarihinsa. Shekara sama da dubu ana zubar da hawaye saboda Hussein su kuma ana la’antarsu. Sun so su gama da jinin Manzon Allah amma Allah yaki yarda har sai da ya cika haskensa ko da munafukai basa so. Kakansu Abu Sufyan ya yaki Manzon Allah, babansu Mu’awiya ya yaki Imam Ali, shi kuma Yazid ya yaki Imam Hussein. Wannan wace irin kiyayya ce?! Yanzu ina sunansu? A kowace unguwa akwai Hussein amma sai ka zaga kana neman Yazid kafin ka samu. A kowane layi akwai Ali amma sai ka gama yawo baka samu Mu’awiya ba.