ANTUNA DA DAN IMAM HUSSAIN (A.S) ABDULLAHIR RADI A DA'IRAR SAMI NAKA

An Tuna Da Jariri Abdullahi Radi a Da'irar Saminaka





 Ma'asumah Nigeria News Updates

 'Yan uwa Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) na Da'irar Saminaka sun tuna da Jaririn Imam Hussain (AS) wato Abdullahi Radhi a yau Juma'a 7/Muharram/1441.

 An fara gudanar da taron ne da misalin karfe 3:30pm a muhallin Hussainiyatu Shaheed Turi dake cikin garin na Saminaka. Inda Malam Umar Uba ya gabatar da jawabai masu tarin yawa game da jaririn na Imam Hussaini (AS) da kuma tabo bangarori daban-daban na waki'ar Karbala.

 Yan uwa maza da mata ciki har da Jarirai masu dauke da koren kyalle a jikinsu domin alamta shi Jaririn. Daga karshe an rufe taron da addu'a bayan wasu baitoci da aka gabatar game da wannan rana. An kammala lafiya kamar yanda a fara lafiya.

 - M N U 04
 - 7/Muharram/1441

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post