ABIN DA YA JANYO AKA TSANI YAN NIJERIYA A AFRIKA

ABIN DA YA JANYO AKA TSANI YAN NIJERIYA A AFRIKA


Yadda Yan'daba suke cin karansu a south Africa. 

Tare da Aliyu Dahiru Aliyu.

Magana ta gaskiya abu uku shi ne yake janyowa a tsani dan Nijeriya a wasu kasashen na Afirka. Na farko dai duk inda ka je an dauka dan Nijeriya matsafi ne saboda fina-finan da yan kasashen waje suke kallo na "Nigerian Films" juju yayi yawa a ciki. Akwai wata yarinya da mukai wasa da ita a Uganda ta dinga taba rigata a hankali wai tsoro take kada ta zama tabarya. Ni kuma da na ganta sai na mika mata hannu  da nufin mu gaisa sai ta gudu wai zan mayar da ita tukunya da "juju". Kuma fa wannan sosai da gaske wasu suke dauka!

Abu na biyu kuma shi ne, mazan South Africa da na East Africa mafi yawansu yan giya ne da yan caca. Sana'a bata damesu ba. Shi kam dan Nijeriya da yaje can zaka ga ko dai iyayensa sun turashi karatu suna tura masa kudi, ko scholarship yaje yi yana samun kudin gwamnati ko babu sana'a, ko kuma neman kudi yaje yi sai yake aiki tukuru. Wannan tasa wasu yan kasar suke ganin kamar yan Nijeriya ne suke kwashe kudin kasar amma su basu da kudi. Basa la'akari da su yan giya ne kawai da yan caca da basa aikin fari bare na baki sai yawon kulob da gidan giya.

Abu na uku kuma, su matan kasashen zaka ga basu saba da kudi ba. Shi kuma dan Nijeriya ya saba kashewa mata kudi. Da ya hadu da budurwa zai fara yawo da ita yana kaita cin Pizza da Shawarma a KFC da McDonals. Daga nan sai kaga yarinya tana wulakanta yan kasarta tana bin yan Nijeriya. A Kampala a misali, indai kai dan Nijeriya ne to yiwuwar samun budurwa kyakkyawa abu ne mai sauki. Yan Somalia kuwa idan suka ga budurwa a cikinsu ta bi dan Nijeriya to duka suke mata tun da ba zasu iya taba dan Nijeriyan ba.

Wadannan abubuwa guda uku su suke haduwa guri guda su sanya a tsani dan Nijeriya. Sai mazan su dinga ganin kamar dan Nijeriya tsafi yake yi yana tara kudi yana kwace musu yan mata. Don haka za ka ji yan South Africa suna cewa yan Nijeriya suna kwashe kudi suna kwace yan mata. Fim yana da matukar tasiri a yadda ake kallon Nijeriya da kuma fassara aiyukanta.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post