Kotu ta amince a fita da Malamin zuwa Kasar India domin neman magani ; sai dai ta bada sharudda .......
A yau Litinin ne 5/8/2019, wata babbar Kotun jihar Kaduna mai suna lamba 4( Court IV), Ibrahim Taiwo road karkashin mai shari'a Darius Khobo ta yanke hukunci kan barin a fita da Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky zuwa Kasar Indiya domin neman magani.
A zantawar manema labarai da daya daga cikin Lauyoyin dake kare Shehin Malamin a Kotu sun shaidawa manema labaran cewa, "Lauyoyin Shaikh Ibraheem Zakzaky sun gabatarwa da Kotu hujjoji 18 na bukatar a bar wanda ake tuhuma ya fita waje domin neman magani, sakamakon rashin lafiyar jikinsa da ya yi tsanani, a sa'ilin da kuma Lauyoyin gwamnati ba su iya bada hujja ko kwara daya ba daga Likitoci wanda ya iya gamsar da Kotu na yiwuwar barinsa a Asibiti a nan Najeriya".
"Daga karshe Kotu ta amince da bukatun Lauyoyin Shaikh Ibraheem Zakzaky inda, ta amince a fita da shi zuwa wani babban Asibiti da Mandeta, Kasar Indiya".
Sai dai Kotun ta amince da a fita da Shehin Malamin ne bisa sharadda kamar aka:
- Zai kasance karkashin kulawar jami'an tsaron 'yan Sanda na DSS.
- Idan ya samu lafiya ya dawo, za a dawo Kotu domin ci gaba da wannan Shari'a.
Shaikh Ibraheem Ibraheem Yaqoub Zakzaky ya kasance a tsare a hannun hukumomin gwamnatin Najeriya yau kimanin shekaru 3 watanni 8, tun bayan mummunar ta'annutin Sojijin Kasar a gidansa dake Gyallesu, Zariya, da kuma babban muhallin taron addini da ke Husainiyyah a ranar 12 zuwa 14 ga watan Disambar 2015, wanda suka kashe mabiyansa fiye da 1000, ciki harda 'ya'yansa maza 3, suka kona gidansa, Husainiyyah da duk abinda ya mallaka dama sauran gine-gine da dama mallakin Harkar Musulunci wadda Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) kema jagoranci.
Hakanan, gamayyar jami'an tsaro a lokuta dabam-dabam sun kashe daruruwan mabiya Shehin Malamin a kuma garuruwa dabam-dabam inda suka rika bude wuta kan 'yan 'uwa almajiran Malam Ibraheem Zakzaky a mafiya yawan loktutan da suke fitowa muzaharorin lumana domin neman hakkinsu na a saki Malaminsu da mai dakinsa da sauran daruruwan 'yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky da ake ci gaba da tsare su a Kurkuru.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Update, Tare da -Idishia Jos

Tags:
#FREE_ZAKZAKY