SUJADA AKAN TURBA
Ma'asumah Nigeria News Update
Tare Da Ishaq
Turba anan itace kwaɓaɓɓiyar ƙasa da busar don yin sujada akanta, kowa ya sani cewa yin sujada akan ƙasa shi yafi da waninsa, kamar yadda Manzon Allah (saw) Yace an mayar min da ƙasa ya zama wurin Sujada da kuma yin taimama (Sahihul Buhari Juzu'i na 1 shafi na 123 babin faɗin Annabi an sanya min ƙasa ta zamo wurin Sujada hadisi na 335 bugun darul Fikri)
Ahmad bn Hambal ya ruwaito cewa :- wani mutum ya tambayi Manzon Allah akan Sallah, sai Manzon Allah (saw) ya faɗa masa cewa, kuma in kazo yin Sujada ka Ɗora goshinka akan ƙasa ta yadda zaka iya jin ƙanshin ƙasar, (musnad Ahmad bn Hambal ƙarƙashin Musnadu banu Hashim hadisi na 2473)
Kuma hadisai da dama sun nuna Manzon Allah (saw) akan ƙasa ko ciyawa yake yin Sujada, misali an ruwaito daga Abu Sa'idul Khudri a ƙarshen bayaninsa yana cewa "haƙiƙa da idanuna naga Manzon Allah (S) bayan ya idar da Sallah yabar Masallaci da jiƙaƙƙiyar ƙasa (taɓo) a goshinka,
An kuma ruwaito cewa Manzon Allah (saw) Yace wurin da yafi dacewa da yin Sujada shine ƙasa ko Abinda ƙasa ta haifar, (Sahihul Bukhari Juzu'i na1 ƙarƙashin Babin Sujada Alal Anfi Was Sujudu Aladdini, babi na 135, hadisi na 813) da kuma Kanzul Ummal na Muttaki Al-hadi Juzu'i na 4 shafi na 113
Wannan ya nuna cewa wajen da Manzon Allah Yake yin Sujada akai shine ƙasa, baya Sujada akan shimfiɗa, kamar darduma, ko mayafi, kuma ma ai ko ba komai ba Abinda yafi kusa agun Ɗan Adam da Ubangijinsa kamar yayin Sujada, kamar yadda Manzon Allah yake cewa : Abinda yafi kusa ga bawa da Ubangijinsa shine lokacin Sujuda, saboda haka ku yawaita Addu'a yayin Sujjadar ku,
Kuma shima wannan akwai Hadisai da dama da suka nuna Manzon Allah (S) yana da keɓantaccen abin Sujada kaman turba da yake saka kansa daidai wurin Sujada in yazo Sallah, misali an ruwaito cewa Manzon Allah yana da keɓantaccen abin sujada (Sahihul Muslim Juzu'i na3 shafi 213 ƙarƙashin kitabul Hadisi babu Jawzi Gusulul haidhi rasa zaujiya, hadisi na 298)
Kuma an ruwaito cewa Ummul Muminina (Matar Manzon Allah saw) tace Annabi yana Sallah wata rana alhali ni kuma ina haila ina zaune kusa dashi wani lokaci kayan jikinsa na taɓani, in yana Sujada, sai ta ƙara da cewa ne akan Kumrah,
(Sahihul Bukhari Juzu'i na1 shafi na 110, ƙarƙashin babin Salatu Alal Khumra, Hadisi na 379, da Hadisi na 333, 381, 517, da 518, bugun darul fijir alkhaira)
A wata ruwayar Ummul Muminina Aisha (Ra) tace Manzon Allah (saw) Yace min ga Khumran nan, sai nace masa Nifa ina haila, sai yace ai hailarki bata à hannuwanki, (Sahihul Muslim Juzu'i na 3 shafi na 213 hadisi na 298)
Abin tambaya anan shine menene Khumra?
Muslim ya fassara Khumra da cewa shine Ɗan ƙaramin abin Sujada gwargwadon inda Za'a yi Sujada akai, Imamun Nawawi à sharhinsa na Muslim cewa yayi Sheikh Alhariri yace Khumra itace Abinda mutum zai iya Ɗora wani ɓangare na fuskarsa a yayin Sujada,
Sahabbai da dama sun kasance suna Sujada akan turba, misali ɗaya anan Shine Hadisin da Nisa'i ya ruwaito cewa Jabir bn Abdullahi (Ra) yace mun kasance muna Sallahr Azahar (wata rana) tare da Manzon Allah (saw) sai na ɗebi ƙasa na curata in nazo Sujada sai Ɗora goshina akai, ( Sahihul Muslim sharhin Nawawi Juzu'i 3 shafi na 214 bugun Mu'assatul Mukhtar, 67 Sunad Nisa'i Juzu'i na2 shafi 21 ƙarƙashin babin tabridul hasalis Sujudu Alaihi, hadisi na 1077, bugun darul fikir)
Ma'asumah Nigeria News Update
Tare Da Ishaq
Wakilin Mu Na Sokoto
Tags:
Taskar ilimi
Masha Allah
ReplyDelete