Shari'ar Sayyid Zakzaky HUKUNCIN KOTU NASARA CE GA HARKA ISLAMIYYA.



Daga shafin Ma'asumah Nigerian News Updates,
Tare da --Idishia Jos. 

Dukkan 'yan uwa na cikin gida nigeriya damage kasashen waje suna cikin farin ciki da murna da jin wannan Umarni na kotu akan shari'ar da aka yi yau. Shekaru 3 da watanni 8 kenan ana tsare da Sheikh Zakzaky cikin tsanani na rashin lafiya tare da harsashi a jikinsa. Tun bayan kama Sheikh Zakzaky a mummunan yana yin da yake ciki suka hana ko kallon sa sai shekarar 2018 ne aka fara bayya Sheikh Zakzaky a inda ake tsare dasu har gidajen "Television" da 'Jaridu' suka nuna da abin karayan wuya a jikinsa.

Tun daga wannan lokaci basu sake bari an kara kallonsa ba suna cigaba da tsare shi. Kotu a Abuja ta bayar da daman a sake shi a bashi kulawa har ma a biyashi wasu kudade da gina mai gida a duk inda yake so, amma duk da wannan umarni na kotu da sukayi bai sa Gwamnatin Buhari ta bi umarnin kotu ba. Har tsawon shekaru sannan aka ce ana tuhumansa da wasu laifukan na daban inda suka damka Sayyid din a hannun gwamnan Bihar Kaduna shekara 1 da ya wuce kenan.

Gwamnatin Kaduna karkashin Gwamnatin El-Rufa'i suka cigaba da tsare Sheikh Zakzaky na tsawon wannan lokaci, suna kai shi kotu lokaci bayan lokaci da sunan tuhuma. Almajiran Sheikh Zakzaky kuwa basu bar fitowa ba suna Muzaharar FreeZakzaky ta lumana akan rashin jin dadin su akan cigaba da rike Sheikh din, sabida yana fama da rashin lafiya shi da matar sa. Abinda yake daga hankulan 'yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky shine duk lokacin da aka ziyarci su Sheikh a inda ake tsare dasu suna samun sune cikin matsanaicin rashin lafiya.

Ko a sati biyu da ya gabata an kai Sheikh Zakzaky asibiti a garin Kaduna a lokacin da jikinsa ya tashi, ana cikin gwada shi aka tarar da harshashi a cikin kwakwalwansa tun Harbin da aka mai shekaru 3 da suka shude.

Watanni biyu da suka wuce Sayyid Muhammad 'Dan Sheikh Zakzaky a duk ziyarar da ya je sai ya tarar da jikin mahaifinsa ya tashi har ma ya tabbatar mana cewa lallai Sheikh Zakzaky ana shayar dashi da guba a inda ake tsare dashi, a lokacin da kuma jikin nashi ya kara tsanan ta na rashin lafiya. Baya ga labarin da likitoci suka fada cewa da yuwuwar Sheikh din ya rasa idon sa guda daya saboda Harbin da aka mai a idon. Biyo bayan kuma shenyewar barin jiki da yake fuskanta.

A ranar alhamis 18 ga watan 7 aka kara kai Sheikh Zakzaky kotu har anyi tunanin a ranar za'a kawo karshen komai, a bada daman sheikh din ya fita waje don kula da lafiyan sa, kotu ta dage shari'ar baki daya inda tace sai ranar 29 ga wata 7 din. Bayan kotu ta zauna a a ranar 29  ga wata 7 lauyoyi duka bangare biyu wanda yake kare Gwamnatin Kaduna da wanda yake kare su Malam (H) duka sun yi magana a gaban kotu inda alkali kuma yace zai yanke hukunci wannan sati.

A yau kuma 5 ga watan 8 aka koma kotu domin sauraren abinda alkali zai ce Darius Khobo ta yanke hukunci kan barin a fita da Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky zuwa Kasar Indiya domin neman magani. "Daga karshe Kotu ta amince da bukatun Lauyoyin Shaikh Ibraheem Zakzaky inda, ta amince a fita da shi zuwa wani babban Asibiti da Mandeta, Kasar Indiya".

Sai dai Kotun ta amince da a fita da Shehin Malamin ne bisa sharadda kamar aka:
- Zai kasance karkashin kulawar jami'an tsaron 'yan Sanda na DSS.
- Idan ya samu lafiya ya dawo, za a dawo Kotu domin ci gaba da wannan Shari'a.

Abinda har yanzu yake ciwa al'umma tuwo a zuciyarsu shine gwamnati Buhari bata bin umarnin Kotu, ga kuma kalaman Nasiru El-Rufa'i da yayi a ranar 18 ga watan 7 wanda yaje cewa in har yana da rai ba zai bar Sheikh Zakzaky ya fita kasar waje ba domin jinya, kuma yayi wannan maganan ne bayan an fito daga saurarem karar da ake yi kotu na Kaduna. Ganin haka muna masu kira ga al'umma su zama shaida Kotun Tarayya na Abuja ta umarci a saki Sayyid Buhari yaki, sannan yanzu gashi kotun da ke Kaduna ita ma tace a saki Sayyid don yaje neman magani a kasar Indiya.

Mu masu bin doka kasa ne, kuma kotun su da alkalansu ne suka yanke wannan hukunci don haka muna masu kira ga gwamnati data gaggauta bin umarnin kotu don Sayyid ya fita neman lafiya tare da matarsa Malama Zeenatudeen.

    -Idishia Jos.

#FreeZakzaky.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post