SAQON SU SAYYED ZAKZAKY DAGA INDA




Bismillahir Rahmanir Raheem!
Wasallahu Ala Sayyedina Wa Nabiyyena Muhammadin Wa Aalihid dayyebinad Daheereenal Ma'asumeen!

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta'ala Wa Barakatuhu.

Yanzu muna birnin Delhi ne a India. Kamar yadda dai aka sani an yi shiri na a zo nan domin, bidar lafiya na wasu matsaloli da muke tare da su, ni da Malama Zeenah. Ita Malama Zeenah akwai cikakken harsashi a jikinta, sannan kuma bayan haka nan akwai bukatar canjin qoqon gwiwowinta guda biyu da kuma wasu matsaloli. Ni kuma akwai 6araguzan harsasai wanda suka farfashe. 'Yan qanana a idanuna, da kuma wasu a hannuna, da kuma wasu a cinyata ta dama wanda sune suka rinqa yin aman guba, wanda ya sabbaba matsaloli wanda daga baya muka gano sune suka sabbaba mini wannan "stroke" na farko da na biyu. To muna tunanim abin da ya kamata a yi na farko kwashe wadannan harsasai, wanda wa'yansu yin wannan aikin ba za a iya yi a gida ba, kuma likitoci suka ce a je waje inda ya kamata a yi.
Sannan na biyu a kwashe gubar da suka amayar wanda wadansu aka ce suna zaune a qashi ne ma, da wasu a tsoka kuma yakan dauki lokaci kafin a gama kwashe su.
Sannan kuma ina da matsalar ido, wanda shi ma har wala yau tuntuni likitocin da suka duba mu tun bayan da aka yi man operation na biyu ganina yai rauni, suka bada shawarar shi ma a je inda ya kamata domin ai aiki.
Sheikh zakzaky a yayin da suka isa qasar india

To, wannan duk muna murnan cewa in mun zo nan Delhi za mu samu asibitin da ya dace domin, ai wannan aiki. To, kuma cikin likitocin da suka zo wajenmu, ko in ce suka je tunda ba muna a Najeriya ba ne. Suka je wajenmu a Najeriya sune suka bamu shawarar wannan asibiti da ake ce ma MEDANTA. To, kuma shi ya sa ma mu muka bid'i a kawo mu nan asibitin din. 

To, tun kafin a kawo mu wanda kuma muna gida muka ji labarin cewa, ofishin jakadancin Amerika ya sa tsama a kan wannan asbiti, kan cewa kada su kar6e mu in mun zo, kuma har sun ce baza su kar6e mu ba.

To, sai muna tunanin a je wani wuri, in aka zo din. To, daga baya sai aka ce mana an warware wannan  matsalan yanzu sun yarda. Shi ke nan sai muka kamo hanya.

To, muna isowa muka samu tariya na su ma'aikatan asibitin,  tun daga filin jirgin sama har zuwa asibiti din. Tun muna cikin ambulance suka bamu labari na cewa, ainihin akwai mutanen da sukai dafifi a filin jirgin sama domin, ko da su ganmu a lokacin da za mu shiga ambulance.  Amma sai suka yaudare su, suka ajiye ambulance guda biyu a gabansu da cewa a nan za mu shiga, amma sai suka dauke mu a wani ambulance suka fita da mu. Saboda haka mutanen da sukai dafifin sam ba wanda ko da ya hango mu ma.

Sannan kuma suka ce har walayau mutane a asibiti sun yi dafifi don suma suga shigar mu asibiti. Shi ma sai suka ce, amma in muka je za a shiga ta qofar baya ne. Suka ce sun yi haka ne saboda yawan mutanen nan mai yiwuwa sui abin da suka ce da Ingilishi sui "mobbing" dinmu, shi ne mutane suna qoqarin ko  su taba mutum, ko sauransu ya zama wani abu, haka dai suka ce.

Bayan da muka zo sai muka fahimci cewa, a wannan asibiti, ko ma mu ce wannan a sarari wani ma'aikacin ofishin jakadancin Nijeriya ya gaya mana cewa kafin ma mu zo, sun riga sun yi taro da ma'aikatan asibitin nan da su ofishin jakadanci da ma jami'an tsaro a kan ya za a yi in muka zo.

Saboda haka sai muka ga kawai an kawo mu ne wani wurin tsaro wanda ya fi tsanani ma a kan wanda muke ciki a Najeriya. Sai ya zama suka shigo da 'yan sanda da bindigogi, sannan kuma da ma'aikatan ofishin jakadancin Nijeriya da yawa. To, kuma dai sai muka lura cewa ainihin an kawo mu  wani qangi ne, wanda daman asalin abin a kan aminci ne.

Ko a gida Nijeriya sun yarda, inda ake tsare da mu sun yarda ba wanda zai sai likitan da muka za6a, muka yarda. To, amma ga shi a nan mun fahimce cewa su likitocin da suka bamu shawarar a zo nan din sam ba su da ta cewa. Sun ma gaya mana da mukai magana da su, lallai sai dai su zo su bada shawara kawai. Amman wannan asibitin ke da ikoi ya za6i duk abin da ya so. Sai na ce masu to, ai bisa aminci ne muka zo, ba zai yiwu kuma mu ga wani likitan da ba mu sani ba, ba mu amince da shi ba ya zo. Kuma wadanda muka aminta ba su gaya mana wani abu game da shi ba ya ta6a mana jiki, don kada a yi abin da aka so a yi wanda harsashi bai yi ba, a yi shi ta wata hanya.

Saboda haka, muna ganin dai gaskiya abubuwan da muka gani a nan ya nuna mana cewa ba mu cikin aminci sam. Kawai an kawo mu wani wuri ne aka tsare.

Ni an tsare ni shekara yau goma sha uku (13) amma ban ta6a ganin tsaro irin wanda akai man a nan ba. Hatta a qofar dakin 'yan sanda ne da bindigogi. Hatta kuma ko daki zuwa daki ba a yadda ma mu je ba. Sai na ga cewa to, ni koma a inda nake, duk tsarewar da ake min a Nijeriya ban ta6a ganin wannan ba. In an tsare ni a gidan kurkuku akan kulle mu ne qarfe tara, a bude mi qarfe bakwai na safe, sannan kuma muna iya zuwa duk inda muka ga dama aqalla a eriyar da muke tsare din.

To, amma sai nan na ga ko kirikiri bai kai tsanani a kaina irin wannan ba. To, sai nake ganin cewa to lallai ba zai yiwu mu fito wani qangi domin, mu samu lafiya a dora mu a wani qangi, a kuma miqa jikkunanmu ga wa'yanda bamu aminta ba. Saboda haka muna tunanin Insha Allahu dai gaskiyar magana ita ce akwai bukatar mu koma gida tunda  dai an yarda mu je wani wuri a waje domin magani tunda India lallai ba ta zam wurin aminci ba yanzu. Sai dai mu koma gida, daman akwai wadansu kasashe da suka yi tayi na cewa za su kar6e mu in mun je. Daga ciki akwai Malaysia da Indonesia da Turkiyua, sai mu je mu tattauna a za6i daya daga ciki sai mu je Insha Allahul azeem. 

Wasallalahu Ala Muhammadin wa Alihid dqyyebeenad Daheereen.
Wassalamu alaikum Warahmatullah
14-08-2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post