Rushe Masallaci A Jihar Rivers________ Yan Shi'a Mabiya Malam Zakzaky Sun Ayyana Aikin Gwamnan Jihar Rivers 'Nyesom Wikem' Na Rushe Masallaci Amatsayin Zalinci Kuma Iri Daya Dana Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-rufa'i A Shekarar 2015.

Daga Ma'asumah Nigerian News Update. A satin daya gabata ne, gwamnan jihar Rivers 'Nyesom Wikem' a zargesa da rushe wajen bautar musulmi (Masallaci),
dukda shi gwamnan ya fito ya musanta zargin da al’umma ke masa na rusa masallacin. Wannan rushe Masallaci da ake zargin gwamnan jihar Rivers da aikatawa, ya kawo cece-kuce tsakanin al’ummar musulmi da kirista, 



Inda wasu ke aibata gwamnan da jifansa da munanan maganganu tare da bayyana aikinsa a matsayin rashin adalci a tsakanin al’umma. Wanda wannan ya saɓawa dokar ƙasa (Constitution).



A gefe guda kuma, kiristoci da wasu musulman na ganin cewa lallai ba'ayiwa wannan gwamna adalci ba, na munanan maganganu da aketa jifansa dasu, sakamakon a jihar Kaduna ma irin wannan ya taɓa faruwa inda a sami wani gwamna ya rushe wani babban wajen bauta na kiristoci 'Church' (Chochi),



amma al'umma basu fito sun nuna damuwa a bisa wancan ƙazamin aikin kamar wannan ba. Wannan yana alamta rashin son gaskiya da son kai. A ɗayan bangaren kuma, yan Shi'a mabiya Malam Zakzaky sun kamanta aikin gwamnan jihar Rivers da aikin gwamnan jihar Kaduna 'Nasiru El-rufa'i'.



Sun kuma nuna cewa gwamnan jihar Rivers ya kwaikwayane daga wajan dan uwansa gwamnan jihar Kaduna, domin shaikaru uku da ƴan watanni da suka wuce Nasiru El-rufa'i ya rushe wani masallaci mallakin yan Shi'a dake Dambo-Zaria,:
wanda Malam Zakzaky ya gina da kuɗinsa a filinsa na gado. Ƴan Shi'an sun ƙalubalanci al'ummar dake tada jijiyar wuya akan rushe Masallacin jihar Rivers da cewa, shin mai yasa a shaikarun baya basu zargi El-rufa'i da aibantasa akan mummunan aikinsa na rushe Masallaci da sauran wuraren bautan su da yayi kamar yadda suke zargin gwamnan jihar Rivers ba? Ta'addanci sunansa ta'addanci, koda waye ya aikata. -


Daga  Wakilunmu
Abbakar Ibraheem Kudan. 31/08/2019.
ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post