NAGARTA DA LAFIYAR YARO

NAGARTA DA LAFIYAR YARO

Ma'asumah Nigeria News Update
Tare da Ishaq


Alal haƙiƙa duk wani abu da kaga mai hankali yana so, ko kuma yana buƙata, to zaka cewa dole akwai dalilin da yasa yake buƙata ɗin, yana da wata Manufa dangane da abin, wanda kuma ita wannan Manufa itace sirrin soyayyar da yake wa wannan abin, kuma koda mene ne wannan abin, kuma in har aka ce maka an wayi gari wata rana an rasa wannan hadari da wannan Manufa tattare da abinda ake so, to shi Abinda ake so zai dawo ba'a son sa, don ya zama shi so ɗin beda amfani, wannan shiyasa zaka ga wani lokaci ga Abinda a hankalce mutum ya kamata ya so shi, amma sai kaga baya so, kamar Ɗan da mutum ya haifa, zaka ga wani lokaci gaba yake da Ɗan nasa, wanda ya sabawa Abinda aka sani na ɗabi'a, wanda muka ce ko dabba tana bin wannan ɗabi'ar na son ɗanta, haka ne,
To kasan ba zai yiwu Ɗan Adam yaso, ko ya ƙi abu daidai da dabba ba, kamar yadda ba Manufar mu anan itace mu saka yin hakan ba, don Ɗan Adam yana da abinda ya bambanta shi da dabba, Shine hankali, wanda da shine yake tantance abubuwa, kuma shi hankali ɗin shine yake Shiryar dashi akan duk Abinda zai so, ya zamo akwai dalili, ba wai kawai don kasantuwar abin Shine shi kawai ba, wato kamar Ɗa, hankali yana nuna cewa kada kaso ɗanka don kawai shi ɗanka ne, don yin hakan bai ɗara son da dabba ke yiwa ɗanta ba, maimakon haka akwai yadda mutum yake son ɗansa ya zama, wanda in bai zama, hakan ba sai kaga dole yana ƙyamar sa,

Don haka Manufar duk mai hankali dangane da yaro Shine ya zama nagartacce, wato nagari ya kuma zama lafiyayye, duk da cewa zamowar yaro nagari Shine babban abin buƙata na farko, amma kasan in bai zama mai cikakkiyar lafiya ba, ko kuna aƙalla mai lafiya ba, ba zai yiwu ya zama nagari ba, tunda kasan tana iya yiwuwa ya zama mai taɓin hankali, kaga ba zai zama yadda ake so ba kenan, ballantana ma rashin zamowarsa nagari, wato marar tarbiyya, shi ma wani nau'i ne na rashin lafiya,

To kamar yadda muka nuna, za'a iya fahimtar cewa zamowarsa yaro lafiyayye da kuma zamowarsa nagari, wasu buƙatu ne da suke rataye da hankali, wanda hakan ya nuna yana da alaƙa da fiɗira, wanda kuma mun nuna duk wata buƙata da ta zama haka, to ta halitta ce, ba wai buƙata ce da mutum ya jajibo wa kansa ba, balle Ace yaji da kansa, buƙata ce wadda Mahalicci ya sanya, don haka shi yakan ɗauki nauyin baka mafita cikin sauki, kamar ƙishin ruwa misali, buƙata ce ta fiɗira, ta halitta, kaga baza kace wa mai jin ƙishi ahaf ai kai ka jajibo wa kanka ƙishi ba, kuma kaga da yake buƙata ce ta fiɗira, shi Ɗan Adam daya zo duniya, yazo da ƙishi ɗin ne kawai, amma bai zo da ruwa ba, kawai cikin sauki se ga ruwa nan mahalicci ya tanadar masa, to haka al'adar Allah take ga irin waɗannan buƙatu, don haka kar mu ƙara nisa a ƙoƙarin kauce wa maudu'i,

Addinin musulunci musamman a tafarkin Ahlul-Baytee (As) babu abinda ba'a fayyace mana ba, a cikin wannan babi, kafin mu fita in Allah ya so zaka ga Ƴan wasu abubuwa kaɗan da muka kawo waɗanda suka shafi lafiyar yaro da kyawun dabi'ar yaro, musamman kafin a haife shi, ko kuma kafin ma ayi cikin, a yayin da mafiya yawa muke rafkane, akwai abubuwa da dama waɗanda suke da tasiri cikin kyau ko muni na hali ko na halittar Ƴaƴan mu, na farko kai kanka ya kamata ka zama nagari, mai tsoron Allah, mai kyawawan ɗabi'u sai kuma ka auri mace tagari, kasan an ruwaito Manzon Allah (saw) Yace "kua zaɓi ga maniyyinka shine ɗanka, don haka a ƙoƙarin gyara ɗabi'ar ɗanka, sai ka nemi mace saliha, kuma abinda yasa muka fara cewa ka zama nagari daga farko tukun shine, kasan yadda ka zama, shi yake nuna irin matar da zata dace da kai,
Allah Ta'ala Yace:- mazinaci ba zai aura ba Se mazinaciya ko mushirika, kuma mazinaciya ba mai aurenta se mazinaci ko mushiriki, kuma an ruwaito wannan bisa ga Muminai, (Suratu Nuh aya 3) ka ga duk da dai ba ayar tana umarni ne cewa mazinaci yaje ya auri mazinaciya ko mushirika ba, wato ba wai Hukunci ne da aka basu ba, amma zaka ga haka ɗinne abinda yafi yawan faruwa, da wuya kaga tantagaryar Ɗan iska, matarsa kuma ba hakan take ba, kuma da wuya kaga mace mumina mai kyan hali, ka dubi wani niga (Ɗan iska) take shi take so, da wuya don haka kowace ƙwarya da abokiyar burminta, shiyasa muka ce ka gyara halayenka, don ka dace da abokiyar burmi Saliha, kasan baka tashi tagajen tagajen yadda kake kaje ka sami wata Ustaziya ta haƙiƙa kace ahakan zaka aure ta don kai kana so Ƴaƴan ka kawai su zama Ustazai nagari ba, kaga in kana son haka, to da farko kai ka fara zama Ustaz ɗin,

Kuma akwai abubuwa da yawa daya kamata ka lura dasu dangane da ita matar da zaka aura ɗin, wanda ba zai yiwu mu kawo su cikin waɗannan Ƴan Ɗan rubutu ba, amma idan ka duba tarihi zaka ga akwai waɗanda su Malamai,ne, amma masana ƙabilu, musamman a cikin Larabawa, Waɗanda idan zaka yi aure, idan kaje ja sami ɗaya daga cikin su kana neman shawara, abinda zai fara maka tambaya shine wane irin yaro kake so, kyakkyawa ko jarumi ko mai hakuri ko saurin fushi ko mai tausayi? Duk wanda ka zaɓa sai yace maka, to ina baka shawarar ka auri Ƴar ƙabila kaza, ko Ƴar gida kaza, don sun san kowace ƙabila da kowace zuriya, ga yadda galibi ƴaƴansu suke zama, to wannan ma yanada ɗan muhimmanci, duk da bai kai yadda matar take ba, Yazo cewa lokacin Imam Ali (As) zai yi aure bayan rauwar Sayyida Fatima (As) ya shawarci Ɗan Uwansa Aƙil, wanda shima yana ɗaya daga cikin irin waɗannan masana, sai shi Aƙil ya tambayi Imam Ali (As) wane irin ɗa kake so? Sai Imam yace "ina son jarumin yaro ne" wanda zai taimaki Imam Hussein (As) à Karbala" sai Aƙil yace masa to ya auri Ƴar wata ƙabila da ya ambata masa, Shine Imam ya auro Ummu Banin wacce ta haifi Abbas (As) kuma à yaƙin siffin Imam Ali yace wa ɗansa Muhammad Ibn Hanafiyya yayi yunƙurin shiga sai ya kasa, ya dawo baya, Imam (As) Ya sake ce masa shiga da yayi haka har sau uku, sai Imam Ali ya bugi kafaɗarsa yace wani ruwa na mahaifiyarka ya biyo ka, da ace kai Ɗan Fatima ne, da ba haka ba.

A gurguje bayan ka auri mace, bayan Kayi cikakken la'akari da abubuwan da suka dace, to sai maganar yadda kuma Za'a kusanci juna ta yadda ya dace, duk dai dan samun ɗa nagari, kuma lafiyayye, domin domin yanayi da lokacin yin jima'i suna da tasiri cikin halitta ko kuma hali na yaro, da za'a haifa, don haka ga abubuwan da ya kamata a lura dasu ƙwarai da gaske.


Ma'asumah Nigeria News Update

Wakilin Mu na Sokoto

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post