LADUBBAN JIMA'I DON SAMUN KAMMALALLEN YARO!
Na (1)
Ma'asumah Nigeria News Update
Insha Muh'd Suleman
Ladubba anan muna nufin lokuta tare da yanayi, kamala kuma muna nufin na hali dana halitta, Saboda haka zamu waiwayi gidan Annabci, domin mu samo wannan haske. Kuma kada dai a manta duk wannan shimfiɗa ne na zuwan nagartaccen yaro.
Yazo cikin wani hadisi mai tsawo daga cikin littafin Makarim na Allamah Ɗabrisy cewa, Manzon Allah (saw) yayi waɗansu Wasiyyoyi yana mai faɗa wa Imam Ali (As) daga ciki yana cewa, Ya Ali kada Kayi Jima'i da matarka a farkon wata ko tsakiyar sa ko ƙarshen sa, domin hauka da kuturta da ɓacin gaɓɓai dana hankali zasu yi sauƙin kama uwar ko Ɗan da ta haifa. Ka daina yin magana yayin Jima'i domin in Allah ya baka ɗa a wannan kwanciyar, tana iya yiwuwa ya zama bebe, kuma banda kallon farjin mace yayin da ake Jima'i, domin hakan yana gadar da makanta, wato ga Yaron da za'a samu, kada Kayi Jima'i da matarka a tsaye, don hakan aiki ne na jaki, kuma idan an sami ciki a hakan Yaron yana iya zama mai fitsarin kwance.
Kada Kayi Jima'i da matarka daren Sallah (wato ana gobe ƙaramar Sallah) domin in ta sami ciki, Yaron zai iya zama mai yawan sharri, idan ka sadu da matarka daren Sallar Layya, in ta sami ciki Yaron yana iya zama mai yatsu shida ko huɗu, kada Kayi Jima'i da matarka ƙarƙashin bishiya mai ƴaƴa don in ta sami ciki Yaron zai zama mai yawan dukan mutane, ko mai yawan kinsan kai, ko kuma boka.
Kada ka sadu da matarka a inda hasken rana ke hasko ku kai tsaye, sai in kasa wani abu ka rufe shi, don in Kayi haka baka rufe ba, in ta sami ciki, to Yaron da zata haifa, zai yi ta rayuwa ne cikin damuwa da talauci har mutuwar sa,
Kada Kayi Jima'i da matarka tsakanin Iƙama da kiran Sallah, yana sa yaro ya zama mai yawan sha'awar zubar da jini, idan kayi Jima'i da matarka cikin halin rashin alwala, yana sa Yaron ya zama mai makauniyar zuciya, ga kuma rowa, kada Kayi Jima'i da matarka a daren Nisfus Sha'aban: in ta sami ciki, Yaron zai zama mai nakasa Akai ko fuska ko duk biyun, kada Kayi Jima'i bisa soro, yana sa yaro ya zama munafuki mai riya,
Manzon Allah (saw) Yace :- lalle in Kayi Jima'i da matarka daren Litinin, to Yaron zai sami mutuwar Shahada, kuma zai zama mai tausayi da kyauta, marar giba, marar ƙarya, marar kage.
In ka sadu da matarka a daren Alhamis, in ka sami yaro, zai zama wani shugaba ko kuma wani babban Malami daga cikin Malamai,
In ka sadu da matarka ranar Alhamis a daidai lokacin da rana take yin zawali, in ta sami ciki, to Yaron Shaiɗan bazai kusance shi ba, kuma zai samu aminci aduniyarsa da Addinin sa.
Ka sadu da ita daren Juma'a, in an sami ɗa, zai zama mai wa'azi, mai iya magana, idan kuma ranar Juma'a ne bayan la'asar, Yaron zai zama sanannen mutum, Mashashuri ko kuma Malami.
Kuma ana ruwaito daga Imam Sadiƙ (As) yana cewa kada Kayi Jima'i a farkon wata tsakiyar sa ko ƙarshen sa, don yana sa yaro ya zama Mahaukaci ko kuma kafa Anyi ɓarinsa.
Yace baka ga koda mai farfaɗiya yafi faɗuwa a farkon wata ko tsakiya ko ƙarshe ba?
Amma yazo daga Imam Sadiƙ (As) cewa an so mutum yayi Jima'i da matarsa a farkon watan Ramadan, wanda wannan ya nuna wancan hani banda farkon watan Ramadan don shi yana cikin lokuta ne ma da ake so.
An ruwaito wani mutum ya tambayi Imam Baƙir (As) shin tana iya yiwuwa ya zama ba'a so mutum yayi Jima'i a wani lokaci duk da cewa halal ne? Yace masa ƙwarai kuwa, daga fitowar alfijir zuwa fitowar rana, da kuma ɓuyar rana zuwa ɓacewar shafaƙi, da kuma lokacin da ake kisfewar rana, da kuma lokacin husufin wata da kuma lokacin da ake baƙar iska ko kuma jar iska, ko kuma Koriya iska da kuma lokacin da akayi girgizar ƙasa.
Waɗannan wasu ne daga cikin Ladubba.
Waɗanda zasu kai ga samun yaro nagari, lafiyayye, kuma idan muka lura zamu ga cewa Waɗannan lokuta da aka yi hani, ba wai fa yana nufin idan mutum ya sadu da matarsa acikin su haramun bane, a'a halal ne. Sai dai kamar faɗakarwa ce gareshi, musamman idan ya damu da yadda yake so ɗansa ya zama, kuma wannan har wala yau zai nuna masa yadda musulunci ya damu da Ɗan Adam. Zaka ga babu wani Addini da yake tattalin ɗan Adam kafin a haife shi kamar yadda Addinin musulunci yake yi.
Da yawa daga abubuwan da musulunci yazo dasu cikin Al-ƙur'ani da Sunnar Manzo (S) da Iyalan Gidansa, zaka ga yanzu ne hatta yammacin Turai suka kai ga kaɗan daga cikin su.
Har wala yau, baya ga lokuta da yanayi, Waɗanda suke da tasiri dangane da lafiya da nagartar yaro, to akwai kuma tasiri na Abinda aka ci ko aka sha lokacin da za'a fara Jima'i, Waɗanda suma zamu yi Ɗan nuni zuwa ga wasu kaɗan daga cikin su, don mu zaɓa wa kan mu, ko kuma aƙalla muyi iya ƙoƙarin mu wajen kiyaye Ƴaƴan mu, tunda kaga wajen kiyaye Ladubban nan, ko kuma rashin kiyayewa muna iya sanin me zai biyo baya, kuma in muka yi nazarin al'ummar da muke ciki, zamu iya ganin wasu darusa akan hakan.
Kuma kada hakan ya baka mamaki, duba Suratu Nuh Aya ta 27, zaka ga Annabi Nuhu (As) yana cewa, "idan kabar su (Ya Allah) zasu ɓatar da Bayinka ne, kuma ba zasu haifi kowa ba, sai fajiri mai yawan kafirci"
Wannan kaga Annabi Nuhu (As) yana magana akan mutanen sa ne, har yana faɗar ga irin Waɗanda zasu haifa. Kaga bai tsaya an haife su ya gani ba, amma har ya Faɗi siffofinsu, ta yiwu kenan akwai wani abu da san cewa suna yi, kuma duk mai yin wannan abun kaga irin Ɗan da zai haifa.
Musulunci ya tarbiyyantar damu akan cewa idan mutum zai yi Jima'i da matarsa ya kamata ya samu abubuwa masu gina jiki, kuma su zama na halal, ya ci su, ko ya sha su kafin ya fara, domin kasanyuwar sinadarai na gina jiki da abincin ke ɗauke dasu, yana taimakawa kyau da lafiyar gangar jiki na yaron da za'a samu, haka nan halasci ko haramci na abinda aka ci kafin Jima'i, in an samu ɗa yakan shafi halayya da ɗabi'ar da yaro zai tashi dasu, Malamai sun ce kafin Jima'i ya kamata a ci ko asha Abinda yake ɗauke da vitamin A.
An ruwaito daga Imam Sadiƙ (As) cewa Manzon Allah (saw) yaga wani yaro kyakkyawa. Sai ya ambaci wani nau'in abinci, yace daga gani uban wannan yaro yaci wannan abincin a daren Jima'in da aka sami Yaron, (Makarim shafi na 172)
Wannan hadisi shaida ne akan Abinda muka yi bayani, kuma haka idan aka ci wani abu, wanda bashida wani sinadari na gina jiki kafin jima'i, yana kawo tawaya ga halittar yaro. Kuma ka lura da yawa zaka ga da yawa wadansu Iyayensu ba wasu kyawawa bane amma su sai ka gansu kyawawa, musamman idan Iyayensu nada Ɗan wadata don suna samun abinci mai gina jiki, ko ma da talakawa ne, in akayi dace bisa hatsari a ranar ko a daren da zasu sadu da matar, uban yaci wani abu mai tasiri, to irin wannan yakan faru, wannan ciye ciyen fa suna da alaƙa da Uba ne ba Uwa ba.
Kuma yazo a hadisi cewa kada ku aurar wa Ɗan giya ƴarku kuma yazo cewa duk matar da ta yarda da mijinta, wato ta bashi kanta yana cikin giya, to zunubinta ya kai yawan taurarin da ke sama, kuma duk Yaron da aka haifa a cikin wannan hali, shi najasa ne (daga littafin La'aliyal Akhbar juzu'i na 5) kuma kamar yadda ya zo cikin wani littafi "Aɗɗiflu Bainal Wirasa Wattarbiyya" cewa binciken wani likita kirista ya fahimci cewa kashi tamanin bisa ɗari na Ƴaƴan kiristoci, Waɗanda aka sami cikinsu a Kirsimeti, sukan zama masu tawayar halittarsu wannan kuma yana faruwa ne Saboda kiristoci a dare da kuma ranar Kirsimeti sunfi yawan shaye shayen giyoyi.
ZAMU CIGABA A KASHI NA2
Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Muh'd Suleman
08132933333

Wakilin Mu na Sokoto
Tags:
Taskar Ma'aurata