KHUDUBAN SALLAR IDI LAYYA NA SAYYID IBRAHIM ZAKZAKY.



Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates,
Tare da  --Idishia Jos.

Na kan ce gaskiyar magana shine, bikin Idi kamar yadda ya zobisa koyarwar Sunnah, to yanzun kam babu shi, sai dai idan Allah ya kawo shi wani lokaci. Shaikh Zakzaky yace: “Yanzu dai abin da muke yi muna kamanta Idi ne, domin Idi yadda ya kamata shine, komai girman gari to, ana yin Idi gwara daya ne. kuma za a hadu ne gaba daya a tsakiyar gari, sannan a kama hanya a fita wajen gari, ana Zikirori. A bi ta wata hanya a je, idan an gama Idi a koma tsakiyan gari ta wata hanyar daban ba wacce aka biyo a farko ba. Sannan daga nan kowa ya tafi gida.

Yace: Wannan da za a yi irin haka a kowane gari ne, to da za a nuna karfin addini. Da ainihin ari sai ya san cewa lallai al’ummar Musulmi suna da karfi. Da wannan garin (Zariya) za mu hadu a tsakiyar gari, mu yi tafiyar kafa zuwa wajen gari, sannan kuma bayan an gama Idi a dawo ta wata hanya daban, a zo tsakiyar gari, da duk garin sai ya ji. To, kuma da ainihin sama ta taimaka” Ya kara da cewa: “Wannan sai randa Allah (T) ya tabbatar da addini. Amma yanzu ‘Raja’an’ domin ‘raja’an’ yanzu a wajenmu hatta mutum daya yana iya yin raka’o’in Idi
shi kadai. Saboda haka ko muma yanzu sallar da muka yi Raja’an ne.

Shaikh Zakzaky ya kuma bayyana ranar Idi a matsayin ranar murna saboda Allah (T) ya sanya ta ta zama haka nan saboda amsa sadaukarwar Annabi Ibraheem (AS) gareShi. Yace a lokaci guda kuma lokaci ne na jaje. “Sallah a wajenmu duk da lokacin murna ne, amma a lokaci guda lokaci ne na jaje da tuna baya da yin bakin ciki da waki’o’i daban-daban da suka auku a irin lokacin.”
Sheikh Zakzaky yana Khuduba a cikin Hussainiyyah Bakiyatullah Zariya a lokacin Sallah Idi a shekarar 2014 

Asalin Idi babban sallah shi ne Allah (T) ne ya jarraba baban mu Annabi Ibrahim (As), da wata jarrabawa mai wahalan ci, bayan ya jarrabce shi da tsawon shekaru ba shi da 'Da to, bayan ance ya shekara 100 har da 'yan kai sai Allah ya bashi 'Da. Sannan sai da 'Dan nan ya kai shekara 12 da Haihuwa ya zamaya fara murna ya samu magaji, sai Allah (T) ya nuna masa ya yanka yaron. Allah (T) ya so ya gwada Ibrahimu ne yaga cewa ibrahimu ashirye yake yayi dukkanin abinda Allah ya umarci shi ? Koma menene! Ibrahimu yaga wannan a mafarki mafarkin annabawa kuma Wahayi ne.

Da ya wayi gari ya kira 'Dan sa yace; Ga fa abiba na gani a mafarki an nuna min ina yanka ka, duba ka gani me kake gani ? Yace "Ya Baba" aikata abinda aka umarce ka zaka sameni insha Allahu cikin masu dauriya 'Ma'ana' zan daure. Ya je dashi mayanka ya kadashi a sashin sa na hagu kamar yadda ake yanka abin yanka, ya rufe idon sa ya dauko 'Wuka', a wani ruwaya kafin ya 'gigara' aka ce; Ya Ibrahim ka gasgata umarni shikke nan jarrabawa ne haka muke gwada bayin mu nagargaru, ya tabbata kai komai in Allah ya saka zaka yi sai ya zamo ba a yanka 'Dan ba.

A wani ruwaya ance yama gigara wukan kuma ya daga kansa sama yana "Allahu Akbar" bayan da ya gama sai ya ga rago ya yanka. Saboda haka da za'a tambaye ka, Ibrahimu ya yanka 'Dan sa? Amsa 'A', amma 'Fi'ilan' bai yanka ba, amma tunda a zuciyarsa  ya sallama akan ya yanka, to za'a iya cewa ya yanka din. Illa iyaka dai Allah bai so a yanka yaron bane ya dai so ne ya gwada shi, ya ga kuma yaci jarrabawa. Wannan yana daga cikin jarrabawowin da aka gwada Ibrahim (As) da shi ya ciccisu wannan daya daga cikin jarrabawowin ne Allah (T) yace; ni zan sa ka zama Jagoran mutane.

Shehin Malamin  Ya kawo yadda a shekara ta 59 ko 60 bayan hijira a daidai 9 ga watan Zulhijja, ranar Arfa, aka kashe dan uwan Imam Husaini kuma Amintacensa, Muslim bin Akil (AS) da mai masaukinsa Hani bin Urwa a Kufa, a masomin fara waki’ar Karbala. Shaikh Zakzaky ya kawo cewa ana son a irin wannan rana ta Idi a karanta wasu addu’o’i daga cikin Sahifa Sajjadiyya, musamman ma addu’a ta 46, da ta 48 da sauran ayyuka da addu’o’i ruwaitattu idan mutum ya koma ga littafan addu’o’I zai gansu.

Mai karatu anan zan saboda gudun rubutun kada ya muku yawa, domin karin karatu ku bincika Jaridar Almizan na wannan Mako An kawo shi baki daya. Ko kuma a manhajan WhatsApp za'a iya ganin Audio mun saka a groups da dama.

    --Idishia Jos. 

#FreeZakzaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post