IRIN WANNAN IZGILANCI AKA YIWA ANNABAWA (A S) !!!

IRIN WANNAN IZGILANCI AKA YIWA ANNABAWA (A S) !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
A kowanne zamani za kaga tarihi na maimaita kansa ne cikin al'umma. Wannan tarihi yakan zama kala-kala, domin ayyuka ne irin na magabata ke faruwa cikin qarnonin dake biye da su har ranar tashin alqiyama.
Ba akan kowa hakan ke faruwa ba face akan bayin Allah salihai masu riqo da koyarwar Manzon Allah (S.A.W W). Su kuma masu koyi da shaidan ba za ka samu ana yi musu irin wannan izgilanci a kansu ba, domin ba sa kan hanyar wadanda aka yiwa izgilanci gabaninsu.
Batun tafiyar Sayyid Zakzaky (H) zuwa India da kuma abinda ya faru tsakaninsa da azzalumai kuma qazaman mutane.
Ganin abinda ya faru yasa Sayyid (H) yayi wasu bayanai wadanda wasu ma daga cikin ku sun rigani ji da fahintar bayanin nasa.
Amma da shike dole sai Sunnah ta maimaita kanta, sai naji wasu mutane na yin izgilanci gare shi da cewa;
- " 3 million ba wasa bane, ai dole yace yana son dawowa don ya cigaba da cinsu.
- " Jinyar tasa ba ta gaskiya bace, domin isarsa India ke da wuya sai ya warware."
- " Son guduwa yake yi, amma rashin ganin hanya tasa shi dawowar dole."
Irin wannan izgilanci yasa na tuno da wadannan ayoyi da Allah ke magana a kansu;
" KUMA WANI MANZO BA YA ZUWA GARE SU FACE SUN KASANCE SUNA MASU IZGILI A GARE SHI."
(HIJRI:11)
To, ku sani, izgilanci ba ya zama alkhairi ga masu yinsa.
Allah ya qara da cewa;
" YAA NADAMA (hasara) AKAN BAYINA! WANI MANZO BA YA ZUWA GARE SU FACE SUN KASANCE SUNA MASU YI MAI IZGILI GARE SHI."
(Y.S:30)
KA QARA HAQURI YAA SAYYID
" HAQIQA TABBAS, ANYI IZGILI GA MANZANNI GABANINKA, SAI WADANDA SU KAYI IZGILIN, ABINDA SUKA KASANCE SUNA IZGILI DA SHI YA FADA MUSU."
(AN'AM:10)

Saboda haka, ku saurari sakamakon Allah irin wanda yake yi ga masu izgili irin ku.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034
Foton limamin masallacin sultan bello dake garin Kaduna tareda wasu yan agajin qungiyar izala

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post