HUKUNCIN ZUBAR DA CIKI.
Daga Fatawoyin Syed Ali Khamnaie (Dz)
Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Muh'd Suleman
T54 - shin ya halatta a zubar da ciki Saboda matsalolin yau da gobe na tattalin arziki?
A:- sam bai halatta a zubar da ciki ba, dan matsalolin yau da gobe na Abinda za'a ci.
T55 - farkon ɗaukan ciki sai likita ya gaya wa mai ciki bayan bincike da yayi cewa akwai hatsari atare da ita muddun ta bar cikin, kana ma za'a haifi yaron da illa dan haka likita sai yasa a zub da cikin, Shin yin hakan ya Halatta? Shin kuma dai yana halatta a zubar da ciki kafin Busa masa rai?
A:- Dan gudun a haifi ɗa da illa bai halatta a zub da ciki a shari'a koda kuwa ba'a Busa masa rai ba, amma tsaron lafiyar uwa da cigaban rayuwarta sanadiyyar ciki in har likita yayi nuni da hakan wanda yake amintacce kuna ƙwararre to ba laifi in har ba'a Busa masa rai ba.
T56 - shin ya halatta a zub da maniyyin da ya shiga cikin mahaifa kafin ya zama jini, wanda hakan ya kan kai kamar kwana arba'in, kana wane Maniyyi ne ya haramta a zubar dashi? Lokacin da ya shiga mahaifa ne ko lokacin da ya zama gudan jini ne? Ko lokacin da ya zama tsoka ko lokacin da ya zama ƙashi kafin Busa rai?
A:- bai halatta a zubar da maniyyi ba bayan ya shiga mahaifa ko zubar da ciki dukkan waɗannan halaye be bai halatta.
T57 - menene Hukuncin zubar da ciki akan kansa? Kana kuma menene Hukuncin zubar dashi lokacin da ya zama haɗari cikin Rayuwar uwa? Idan ya halatta shin akwai bambanci da wanda aka Busa wa rai da wanda ba'a Busa ba?
A:- zub da cikin haram ne a shari'ance bai kuma halatta sai in har ya kasance haɗari cikin rayuwar uwa to, ba laifi a irin wannan hali a zubar dashi kafin shigar rai, amma bayan shigar rai bai halatta ba koda kuwa haɗari ne ga rayuwar uwa sai dai idan kuma rashin zub dashi ɗin zai kawo ƙarshen rayuwar su ga baki ɗaya, kuma ba zai yiwu Yaron ya rayu ba ko ƙaƙa, sai dai uwar ta rayu Saboda dalilin zubar da cikin.
T58- mace ce ta zubar da cikinta na zina wanda ya kai wata bakwai da umarnin babanta shin zata biya diyya? In har za'a biya waye zai biya daga cikinsu? Kana ga waye za'a bada diyyar? Sannan nawa ne Abinda za'a biya a daidai wannan lokacin bisa fatawar ka?
A:- haram ne a zubar da ciki koda kuwa na zina ne, umarnin uba bai kau da laifin zubar da shi dan haka idan ta aikata ko ta taimaka aka aikata dole ne ta biya diyya, Amma akwai maganganu kan yawan adadin Abinda za'a bayar illa Ihtiyat anan Shine yin sulhu, kana diyyar tana kasancewa cikin Hukuncin dukiyar Gadon mutumin da bai da magada.
T59- nawa ne diyyar cikin wata biyu da rabi wanda aka zubar da gangan? Kuma waye ya kamata abawa diyyar?
A:- idan ciki ya zamo gudan jini aka zub dashi diyyarsa dinari arba'in ne idan kuma har ya zama tsoka dinari sittin ne, idan kuma yayi ƙashi wanda ba nama dinari tamanin, Kana wannan diyyar ana bada ita ne ga wanda zai gaji jinjirin bisa matsalolin gado sai dai wanda ya zubar da cikin bai Gadon komai a cikinta.
Ma'asumah Nigeria News Update
Tare da Ishaq
Wakilin Mu na sokoto
Tags:
Taskar Ma'aurata
Allah kara hasken makaranta dady muna godiya Amman sai ankoyaman blogger
ReplyDelete