HUKUNCIN DA YA SHAFI SHAN MAGANI DAN HANA ƊAUKAR CIKI
Daga Fatawoyin Syed Ali Khamnaie (Dz) na (1)
Ma'asuma Nigerian News Updates
Ishaq Muh'd Suleman
T53- Ya halatta mace mai lafiya tayi amfani da magani dan hana ɗaukar ciki zuwa wani lokaci? Kuma menene Hukuncin yin amfani da maganin nan hana hana ɗaukar ciki mai suna (I.U.D) wanda har yanzu kuwa an kasa gane ta yaya ne yake hana ɗaukar ciki, illa kawai an san cewa yana hana shigar maniyyi mahaifa, kana shin matsaloli yau da gobe na tattalin arziki suna halatta asha maganin da zai hana ɗaukar ciki na har abada?
Ko kuwa hakan Yana halatta ne Saboda cuta wacce ake tsorace wa ran mai cikin? Haka kuma dai shin yana halatta mata su ƙi ɗaukan ciki na har abada irin mata waɗanda haihuwar su zata taimaka wajen samar da yaran da suke da cututtuka na gado wanda zai shafi jikin su ko Ruhin su?
Amsa- ta farko dai ba abinda zai hana mace tasha magani dan hana ɗaukar ciki na Ɗan wani lokaci muddun dai da izinin mijin ta,
Amsa ta biyu:- bai halatta ayi amfani da magani ba wanda aikinsa shine zubar da ruwan maniyyi bayan ya riga ya shiga Mahaifa, ko kuma zai janyo a kalli Al'aura ko taɓa ta, irin wanda suka haramta.
Amsa :- rashin abubuwan masarufi na yau da gobe ko yawan Ƴaƴa ko abunda yayi kama da haka bai kamata mutum ya kula da ita ba yanda ta dalilinta zai hana wa kansa ciki na har abada,
Amsa ta huɗu, ba laifi mutum ya hana ciki dan gudun Abinda aka ambata kai yin ciki halatta ba ba in har zai janyo haɗari cikin rayuwar ita uwar jinjiri, sai dai idan ya faru ne bada zaɓi ba.
Amsa ta biyar : ba Abinda zai hana hakan in har akwai Manufa ta masu hankali a ciki kana kuma hakan ba zai jawo cuta sosai ba, sa annan ya kasance da izinin Miji.
Ma'asumah Nigeria News Updates
Ishaq Muh'd Suleman
08132933333
Tags:
Taskar Ma'aurata