HUJJAR MU TA KARANTA BISIMILLA FARKON FATIHA DA SURAH A CIKIN SALLAH
Ma'asumah Nigeria New Update
Tare Da Ishaq
Bisimillah itace ayar Farko ta Fatiha kamar yadda Abu Humaira ya ruwaito cewa Manzon Allah (saw) Yace:- idan zaku karanta Fatiha (acikin Sallah) to ku karanta Bismillahi Rahmanir Rahim, domin itace farkon ayar Fatiha (47 bulagul Miram, shafi na 57, ƙarƙashin babus Sallati Nabiy hadisi na 302 bugun darul fikri)
Kuma an ruwaito cewa Ummul Salma (Ra) tace Manzon Allah (S) ya karanta Bismillahi Rahmanir Rahim acikin Sallah amatsayin Ayar Farko sannan Alhamdulillahi Rabbil Alamin aya ta biyu, Arrahamanir Rahim aya ta uku, haka haka har ƙarshen Fatiha
(48 Nail Al-awtar na Shaukani Juzu'i na 2 shafi na 562 hadisi na 588 ƙarƙashin babu man ja'a fi Bismillahir Rahmanir Rahim,)
An kuma ruwaito cewa Ibn Abbas Yace : Fatihatul Kitab itace Bismillahir Rahmanir Rahim, sai Ibn Juraish Yace Mahaifina Sa'id ya baka labarin cewa Ibn Abbas Yace Bismillah Aya ce? Sai yace Eh, Mustadrak Na Hakim Kitabut Tafsir A Tafsirin Suratul Fatiha.
Ibn Abbas Yace Manzon Allah (saw) ya kasance yana fara Sallahrsa ne da faɗin Bismillahir Rahmanir Rahim (Tirmizi Juzu'i na2 shafi na 40, hadisi na 245, a ƙarƙashin babu man ra'al jahru bi Bismillahir Rahmanir Rahim babi na 81)
Sannan Imam Shaukani ya ruwaito hadisai da suka nuna Manzon Allah (saw) ya karanta Bismillah a bayyane acikin Sallah, ga yadda ya ruwaito su, Nana Aisha (Ra) tace Manzon Allah (S) ya kasance yana bayyana Bismillah a Sallah,
Shima Anas Bn Malik Yace- Naji Manzon Allah yana Bayyana Bismillah a Sallah (51 Nail Al- Awtar na Shaukani Juzu'i na 2 shafi na557 da 562 babun Man Ra'al Jahra fi Bismillahir Rahmanir Rahim, bugun darul hadis)
Wannan ne Sahabbai da dama suka kasance suna karanta Bismillah a farkon Fatiha da Surah acikin Sallah,
Misali, Na'imu Almuhajir Yace nayi Sallah a bayan Abu Huraira (Ra) sai ya karanta Bismillahi Rahmanir Rahim sannan ya karanta Fatiha har ya iso Waladdhaleen sai muka ce Amin, yayin da yayi Sallama sai Yace: na rantse da Allah da Allah, lalle na fiku iya Sallah irinta Manzon Allah (saw) Bulugul Miram shafi na 57 hadisi na 302 303 ƙarƙashin babus Siffatus Sallatin Nabiy da Mustadrak na Hakim ƙarƙashin Kitabus Salat
An ruwaito daga Anas Bn Malik Yace Mu'awiyya yayi Sallah a Madina sai ya karanta Bismillah da Fatiha a bayyana bai a Surah ba har ya gama karatun, yayin da yayi Sallama sai Muhajir da Ansar suka kira shi suka ce "Ya Mu'awiyya shin ka san Sallah ko ka manta ne? Daya sake yin Sallah sai ya karanta Bismillah a bayyane ( Al- Awtar na Shaukani Juzu'i na2 Shafi 556)
A wani hadisi kuma Muhammad bin Suriyyul Askalani Yace :- nayi Sallahr Asuba da Magariba waɗanda ba zasu Irgu ba abayan Mu'utamir bin Sulaiman, ya kasance yana bayyana Bismillah kafin Fatiha da kuma bayanta (kafin Surah) kuma Naji Mu'utamir yana cewa bazan kau daga koyi da Sallahr Babana ba, kuma Babana yace bazan kau daga koyi daga Sallahr Anas Bin Malik ba, kuma Anas Bn Malik Yace bazan kau daga koyi da Sallahr Manzon Allah ba, Mustadrak na Hakim Juzu'i na1 shafi na 234 ƙarkashin Kitabut Salat,
Shaukani shima ya kawo cewa wasu Tabi'ai da suka tafi akan karanta Bismillah a bayyane kafin Fatiha da bayan Fatiha acikin Sallah. Ga Abinda yake cewa
Khaɗib Yace lallai Tabi'ai da suka ce a bayyana Bismillah (acikin Sallah) sunfi ƙarfin a irga su, daga cikin su akwai Sa'id Bn Musayyib, Ɗawus, Aɗɗa'u, Mujahid, Abu Wa'il, Sa'id Bn Jubair, Bn Sirrin, Ikrama, Aliyu Zainul Abidin Baƙir, bayan ya irgo su, da yawa sai yaci gaba da cewa Baihaƙi yace Iyalan Gidan Manzon Allah (saw) duk sun tafi akan bayyana Bismillah acikin Sallah, haka ma Shafi'i da Jama'arsa (Nail Al-awtar Juzu'i na 2 shafi 557)
Baka haka ba, Imam Fakhruz Razi cewa yayi, amma cewa Ali (Ra) ya kasance yana bayyana Bismillah acikin Sallolin da ake ɓoye karatunsu, wannan ya tabbata ta hanyoyi da yawa, Imam Fakhruz Razi bai tsaya nan ba sai ya cigaba da cewa kuma duk wanda yayi koyi da Addininsa da Imam Ali (AS) to Haƙiƙa ya shiryu, dalilin hakan shine Faɗin Manzon Allah (saw) cewa "Ya Allah ka Jujjuya Gaskiya da Ali duk inda ya Juya
(Tafsirul Kabir na Fakhruz Razi Ƙarƙashin Tafsirin Basmala.
Ma'asumah Nigeria News Update
Tare Da Ishaq
Wakilin Mu Na Sokoto
Tags:
Taskar ilimi