HAƊA SALLOLIN AZAHAR DA LA'ASAR KO MAGRIBA DA ISHA
Ma'asumah Nigeria News Update
Tare da Ishaq
Daga Mu'azu bn Jabal cewa Annabi (saw) ya haɗa Sallah a tabuka tsakanin Azahar da La'asar da Magrib da Isha'i sai Abu Tufail Yace sai na tambayi Mu'azu Meyasa yayi hakan? Sai yace yaso kada Al'ummarsa ta ɗauki yin haka laifi ne, (Sahihul Muslim Sharhin Nawawi Juzu'i na5 shafi na 219, ƙarƙashin babu Jam'i Salataini fil hadhari hadisi na 705 da 405, 50)
Bukhari shima ya ruwaito daga Abu Umamata Yace, sai yace nayi Sallah tare da Umar bn Abdulaziz (a lokacinta) sannan muka je gidan Anas bn Malik muka sameshi yana Sallar La'asar, sai nace ya Baffa wannan wace Sallah ce Kayi? Sai yace Sallar La'asar kuma wannan itace Sallar Manzon Allah wacce muke yi tare dashi (Sahihul Bukhari Juzu'i na1 shafi na 149 babul Waƙatul Asari kitabu muwaƙitus Salat hadisi na 549 bugun darul fijri) wannan yana nufin Anas bn Malik ya haɗa Azahar da La'asar ne a lokacin Sallar La'asar kuma yace haka Manzon Allah ma yake yi.
Awani wajen Bukhari ya ruwaito daga Ibn Abbas yace Manzon Allah (S) yayi Sallah Raka'a bakwai a haɗe sannan yayi Raka'a takwas a haɗe, (Sahihul Bukhari Juzu'i na1 shafi na 140 ƙarƙashin babu waƙatul Magrib kitabu mawaƙitu Salat hadisi na 562 bugun darul fijri)
Ibn Umar, Abu Ayyub, da Ibn Abbas Sunce Manzon Allah (saw) ya haɗa Sallar Azahar da La'asar da kuma Magrib da Isha, (Sahihul Bukhari Juzu'i na1 shafi na 141 ƙarƙashin babu zikirul Isha kitabu Mawaƙitu Salat hadisi na 549 bugun darul fijri)
Har yau acikin Bukharin Amir Ya ruwaito daga Jabir Ibn Zaid cewa Ibn Abbas Yace Munyi Sallah tare da Manzon Allah Raka'a takwas a lokacin guda (4 na Azahar, 4 na La'asar) sannan munyi Raka'a bakwai a lokacin guda (3 na Magrib, 4 na Isha) Amir yace na faɗawa Abu Al-Shadha, cewa ina tsammanin Manzon Allah (S) ya jinkirta Sallah Azahar ne har zuwa lokacin la'asar kuma ya jinkirta Magrib har zuwa lokacin Isha, sai yace ina tsammanin haka? "Sahihul Bukhari Juzu'i na1 ƙarƙashin kitabul Juma'a hadisi na 1174"
Sannan Ahmad bn Hambal ya ruwaito a Musnad nashi daga Qatada yace naji Jabir Bn Zaid yace daga Ibn Abbas yace Manzon Allah (S) ya haɗa tsakanin Azahar da La'asar da kuma Magrib da Isha ba'a lokacin tsoro ba, kuma ba ana ruwan sama ba, sai akace da Ibn Abbas me yake nufi da yin hakan? Sai yace ya nufin kar ya sanya Al'ummarsa acikin ƙunci.
Ma'asumah Nigeria News Update
Tare da Ishaq
Wakilin Mu na Sokoto
Tags:
Taskar ilimi