Falala da girman ranar Ghadeer; LOKACIN GHADEER LOKACI NE NA JADDADA BAI'A GA AMIRUL MUMININ ALIYU BIN ABUDALEED.

Falala da girman ranar Ghadeer;

LOKACIN GHADEER LOKACI NE NA JADDADA BAI'A GA AMIRUL MUMININ ALIYU BIN ABUDALEED.

LABBAIKA YA ALI AMIRUL MUMINI



-Sheikh Adamu Tsoho Jos.

Muna masu godiya ga Allah (T) bisa wannan ni'ima da baiwa da Allah ya mana, wannan ni'ima a irin wannan lokaci wanda ake bikin ranar Ghadeer, ni'imace babba ni'ima ta
"Wulaya". Kuma babu wani kamar ta, ga kuma kasancewan ka musulmi. Ranar Ghadeer Idi ne daga cikin Idoji, lokaci ne na jaddada bai'a ga Imam Aliyu da sauran zuriya na Manzon Allah (S). A wannan lokaci ne Manzon Allah (S) ya nasabtashi Sayyida Aliyu a matsayinsa kalifansa wato magajinsa a bayan sa, wanda kuma wannan rana tana da falala da daraja wanda ya kamata ace mun kiyaye.
Rana ce wanda ya kamata ace an farantawa muminai rai, kuma an ciyar da abinci kamar yadda yazo a ruwaya cewa; shine ana so muminai suyi kwalliya su sanya suturu masu kyau susa turarai su nuna murna da farin ciki suna cewa a wannan rana Allah (T) ya nassaba Imam Aliyu a matsayin Halifa bayan Manzon Allah (S). A irin wannan lokaci mu farantawa muminai rai musamman ma ma'abota wulaya da biya musu bukatun su, kuma lokaci ne na sadar da zumunci, kuma lokaci ne da ya kamata a yalwatawa iyali da dukkan bayin Allah.
Akan yi azumi a ranar 18 ranar Gadheer kenan, sannan yazo a ruwaya ranace ta 'Musabaha' ta kyautata 'Yan uwantaka tsakanin ka da 'yan uwanka muminai, bayan kun yi 'musabaha' sai kuyi addu'a da yin alkawari na ceto da ziyara. Kuma a wannan rana ana so a ziyarci Amirul-Muminin da kuma yawan kyaututtuka da kuma godiya ga Allah a bisa ni'ima babba. Da kuma yawaita salati ga Manzon Allah (S) da iyalan gidansa da kuma kiyaye ibada akwai sallah da wasu addu'oi da ake son ayi su. Kuma ana so ka yawaita 'Infaki' a irin wannan rana. Sannan ciyar da abinci a irin wannan rana kamar ka ciyar da 'Annabawa' su Dari da Bubu Ashirin da Hudu da 'Siddiqai' gaba ki daya da aka yi su a tarihi na 'Dan Adam.
Wannan yana nuna mana wato falala da girma na wannan rana, dan haka wannan ranar rana ce ta farin ciki, kuma rana ce ta jaddada bai'a ga Amirul Muminin Imam Aliyu (As) wanda ya kasance shine shugaba a cikin wannan al'umma bayan Manzon Allah (S). Domin a wannan rana ce Allah (T) ya kammala addininsa ya kuma cika ni'imansa akan mu, kamar yadda Allah ya saukar da aya bayan hadisa da ya faru a Gadheer Khum, 'Alyauma akmatu lakum Dinikum wa atmattu alaikum ni'imati wa radaitu lakum islama Dina" wanna aya, aya ce mai girma a wannan al'umma Allah ya ambata a wannan rana mun kammala muku addinin ku, mun kuma cika muku ni'imar mu, muka yarje musulunci ya zamo shine addini gareku.
-Daga jawabin Sheikh Adamu Tsoho Jos wanda yayi a shekarar 2014 wanda yayi daidai da 1435 a Hussainiyatu Zakzaky (H) Jos. Kada ku manta A yau Litinin Akwai taron Ghadeer da za'ayi a Hussainiyatu Zakzaky (H) dake Unguwan Rogo Jos ana gayyatan kowa da kowa.

--Idishia Jos.

# FreeZakzaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post