FAƊIN HAYYA ALA KHAIRIL AMAL

FAƊIN HAYYA ALA KHAIRIL AMAL 


Ma'asumah Nigeria News Update
Tare da Ishaq

Faɗin Hayya Ala Khairul Amal acikin kiran Sallah ya kasance tun zamanin Manzon Allah (saw) sai a lokacin Khalifancin Umar Bin Khaddab (Ra) ya hana don tsoron kar Musulmi su ƙi fita Yaƙi, idan suka sakankance cewa lallai Sallah ce "Khairul Amal" ba jihadin da shi Umar ya sanya a gaba ba,

Misali Imam Shaukani ya  ruwaito a littafinsa Nail Al-Antar cewa "Ya tabbata a garemu kalmar Hayya Ala Khairil Amal ana karanta ta a cikin kiran Sallah a lokacin Manzon Allah (saw) har lokacin da aka hanata a zamanin Umar, kuma wannan Shine Hassan bin Yahaya shima ya tafi akai,

Baihaƙi ya ruwaito ta hanyoyi ingatattu cewa Abdullahi Bin Umar (Ra) wani lokaci ya kan karanta Hayya Ala Khairul Amal a kiran Sallah, kuma an ruwaito daga Ali Bin Hussain cewa wannan Shine farkon kiran Sallah a musulunci,
(Nail Al-Antar na Imam Shaukani Juzu'i na 2 shafi na 41)

An Ruwaito a kanzul Ummal cewa Bilal ya Kasance yana Faɗin Hayya Ala Khairil Amal acikin kiran Sallah na Assubah,
(kanzul Ummal Juzu'i na 8 shafi na 342)

Sannan Baihaƙi ya ruwaito daga Jabir Bin Muhammad daga Babansa cewa Ali bin Hussain ya kasance a cikin kiran Sallah yana faɗin Hayya Ala Khairil Amal, Hayya Ala Falah, kuma yace wannan Shine farkon kiran Sallah.
(Sunanul Kubra na Baihaƙi Juzu'i na 1 shafi na 793 hadisi na 1993 ƙarƙashin Babin Ma Ruwawi Fi Hayya Ala Khairul Amal)

Ma'asumah Nigeria News Update
Tare da Ishaq

Wakilin Mu Na Sokoto

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post