DUK WANDA NA ZAMA SHUGABANSA, TO, ALIYU SHUGABANSA NE

DUK WANDA NA ZAMA SHUGABANSA, TO, ALIYU SHUGABANSA NE !!
!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @






A WANNAN RANA KAFIRAI SUKA YANKE TSAMMANI DAGA ADDININ ALLAH
Ranar 18, Zul-Hijja,10 (B.H), ita ce mafi girma cikin ranakun Idodin muslimci, domin rana ce wacce Annabi (S A.W.W) ya nasabta Iman Aliyu (A S) a matsayin jagora a bayansa, a wani guri da ake kira Ghadeer-Khum don jagorantar mu zuwa samun yardar Allah.
A sama ana kiran wannan rana ne da RANAR QULLA ALQAWARI, a qasa kuma ana kiranta RANAR DA AKA KARBI ALQAWARI.
An ambace ta da wannan suna ne domin rana ce da duk wanda ya halarci wannan guri ya karbi alqawarin zai bi Iman Aliyu a matsayin Khalifan Annabi (S) a bayansa.
An kawo ruwayoyi masu yawa kan wannan al'amari, amma ga guda daya (1) wacce aka karbo daga Zaid Bn Arqam yace;
Yayin da Annabi (S) ya dawo daga Hajjin ban kwana akan hanyar sa ya sauka a gurin da ake ce masa GHADEER-KHUM.
Ya tsayar damu gaba daya, ya hau kan wani guri mai tsaho wanda aka shirya masa (kamar yadda kuke gani), yayi Khuduba mai tsaho wanda a ciki yace;
" HAQIQA KIRA YAYI KUSAN BIJIRO MIN NA AMSA. NI INA MAI BAR MUKU NAUYAYAN ABUBUWA BIYU, 'DAYA SHINE MAFI GIRMA LITTAFIN ALLAH, DA 'YA'YAN GIDANA TSATSONA. KUYI NAZARIN YADDA ZA KU SABA MIN A CIKINSU, DOMIN SU BA ZA SU RABU BA HAR SAI SUN RISKE NI A BAKIN TAFKI."
Sannan yace;
" HAQIQA ALLAH NE MAJIBINCIN AL'AMARINA, NINE KUMA MAJIBINCIN DUKKAN MUMINI."
Sannan sai yayi riqo da hannun Ali ya kuma ce;
" DUK WANDA NA ZAMA MAJIBINCINSA, TO, ALIYU MA MAJIBINCIN AL'AMARINSA NE. ALLAH KA WULAQANTA WANDA YA WULAQANTA SHI, KAI ADAWA DA WANDA YAYI ADAWA DA SHI."
-Kanzul-Ummal, J:6, Sh:157
-Al-Mustadrak Hakeem An-Naisaburi, J:3, Sh:129
-Talkisul-Mustadrak, Allama Zahabi, J:3, Sh:109
-Majma'ul Zawa'id, Ali Ibn Abubakar Al-Hatimi, J:9, Sh:163.
Bayan sunyi masa mubaya'ah kamar yadda kuke gani, sai Allah ya saukar da;


" AYAU KAFIRAI SUN YANKE TSAMMANI DAGA ADDINUNKU, KADA KUJI TSORONSU KUJI TSORONA. AYAU MUN KAMMALA MUKA KAMMALA MUKU ADDINI

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post