DARUSSA DAGA MUNASABAR GHADIR*

DARUSSA DAGA MUNASABAR GHADIR*

Daga shafin ma'asumiyya Nigeria news update

labbaika ya ali bin abutalib [a s]



Alhamdulillah,kasantuwar wannan wata da muke
ciki,wato na zul hijja,a cikin sa ne,kamar yadda aka
sani,18 gare shi,shekara ta goma bayan
hijira,wannan munasaba ta ghadir ta kasance.Kuma
tun daga wancan lokaci har ya zuwa yau dinmu
wato yau shekara sama da shekara 1449m, mabiya Ahlulbaiti [AS] a duk shekara a kuma
sassan duniya daban- daban suke raya wannan rana
ta ghadir ta fuskoki daban daban.Misali raya ranar
tayin wasu ibadodi, kamar azumtar ranar,karanta
wasu addu'oi da ake son karantawa a ranar,dadai
sauran ayyuka na ibadodi da sukazo a hadisai,da
ake son yin su a ranar, sannan kuma mabiya
Ahlulbait [AS] suna rayar da wannan rana, dayin tarurruka domin tunasar da juna dangane da
wannan rana ta ghadir dadai sauran ababe dake da
alaka da ranar,Wanda irin wadannan ayyuka na raya
wannan rana ta ghadir,ba zaka jishi ko ka ganshi ba
a tsakan kanin yan uwanmu musulmi Ahlus Sunnah
ba.Duk da cewa shi wannan al'amari na ghadir,ba
abu bane daya shafi mabiya Ahlulbaiti ba kawai.a'a
abu ne da ya shafi kowa da kowa a wannan
a'umma ta manzon Allah [S],Domin khutbar da
manzon Allah [S] yayi a ranar ghadir,wadda ta
kunshi wadanda zasu kasance khalifofi a
bayansa.abune wanda ya shafi kowane
musulmi.
Baya ga haka kuma shi wannan al'amari
na ranar ghadir mutum zai iya tabbatar dashi sanka
sanka dinsa, a littafan Ahlus Sunnah, kai hatta wasu
ibadodi da akeyi a ranar,sunzo a littafan Ahlus Sunnah. misali anan shine Azumin ranar ghadir,akwai hadisi da yazo a cikin littafan Ahlus Sunnah akan
shi,ga hadisin.An samo daga Abu Huraira yace: Manzon Allah [S] yace:Duk wanda ya azumci ranar sha takwas ga watan zulhijja,za'a rubuta masa
azumin wata sittin itace ranar ghadir khum......wato har ya zuwa karshen hadisin.Mu duba muga
wannan hadisi,gashi dai daga masadir ne na Ahlus
Sunnah, amma da wuya kaji ambaton hadisin tsakan
kanin malaman Ahlus Sunnah, kuma mutum ya kwatanta wannan hadisi da wanda suke yawan kawowa na Azumin Ashura,wanda wannnan ya isa ya nuna ma mutum cewa lalle wani abu ya auku a tarihin wannan al'umma, wato an gina mutane akan abunda akeso a ginasu.An kuma kautar dasu akan
abunda akeso a kautar dasu.Wadanda suka yi riko da wannan al'amari na ghadir,aka dauki matakai akansu daban- daban na cutarwa da gallazawa,mutum ya tambayi tarihi zai bashi amsa.Saboda haka wannan kadai ya isa ya nuna banbancin mahanga tsakanin shi'a da sunna,dangane da al'amarin ranar ghadir.Wato a aikace zaka ga wadannan sun san da zamansa, kuma suna raya shi.Akasin daya bangaren ba zaka ji ambaton haka ba,ballan tana su raya shi, alhali mutum na mutuwa bayan an sa shi a kabari,daga cikin tambayoyin da za'a yi masa akwai abinda yake da alaka da wannan al'amari na ghadir,wato bayan an tambayi mutum waye Ubangijinka? Waye Annabinka? Sa'annan sai a tambayi mutum waye Imaminka? Kuma wani abin lura anan shine,wadannan tambayoyi suna nuna lalle al'amarin
Imamanci ko Khalifanci yana da alaka da akidane,ba kamar yadda malaman Ahlus Sunna suka tafi akai cewa baida alaka da akida.Wato baya cikin Usuluddin yana cikin Furu'uddin ne.Kuma ko baya ga wannan mu duba irin su hadisai da suka zo,kan
alamarin imamanci,misali hadisin da ya zo cewa "Wanda ya mutu bai san Imamin zamanin sa ba,to
ya mutu mutuwar jahiliyya"Saboda haka,al-amarin imamanci ko khalifanci babban abune,a wannan addini,shiyasa,amakarantun mabiya ahlulbaity yana cikin
usulid-din ne.kuma shi imamanci ko
khalifanci,shine abu na karshe da Manzon Allah [S]yayi,a sakon da ya isar tsawon shekaru 23.Domin daga shi babu wani abun da ya sauka,mai matsayin wajibi,shiyasa bayan da Manzon Allah ya Nasabta Imam Ali[as]A ranar ghadir,sai ayar Al-yauma akmal-tu lakum-dinakum,ta
sauka.Saboda haka isar da sakon imamanci ko khalifanci,tamkar khatma na sakon da Manzon Allah [S] yazo da shi,Kuma ayyana Imam Ali[as]A matsayin khalifa,a bayan Manzon Allah[S] yakasance a matsayin rasmiyyan domin gabanin haka,a wajaje da dama, akuma lokuta daban-daban Manzon Allah[s]yayi isharori da kuma hannun ka mai sanda,na khalifa a
bayan sa,shiyasa Manzon Allah na cewa zai bayyana khalifan sa,sai wasu fuskoki suka bata rai,saboda sun san ko waye za a bayyana.Kuma baya ga haka,A sahabban Manzon Allah baki daya,babu wani sahabi wanda dajojin sa da fifikon sa,a ka ruwaito
su daga Manzon Allah kamar Imam Ali[S]wannan magana,Ahmad ibn hanbal ya fade ta.Misali ga wasu hadisai na Ahlus sunnah kan haka:- Manzon Allah[s]yace "Bayana fitina zata kasance,idan haka ya faru,to ku lizimci Ali dan Abi Dalib,domin shi mai
rarrabewa ne tsakanin gaskiya da karya"A wani hadisin kuma,Manzon Allah[s] yace ma Ammar dan Yasir, Ya Ammar idan kaga Ali yabi wata hanya,mutane kuma suka bi wata hanyar da Ali bai bi ba,to kabi hanyar da Ali yabi,kabar hanyar da saura mutane suka bi,domin shi ba zai fitar da kai
daga shiriya ba.Har wala yau a wani hadisi kuma,Manzon Allah [s]yace: zai kasan ce tsakanin mutane,za a samu sabani da rarraba,zai kasance wannan (wato imam Ali) da sahabban sa,su ke kan gaskiya.da dai hadisai masu yawa,makamantan wadannan,da suka zo a litafan Ahlus sunna,da suke nuni ga matsayi na Imam Ali[as]Saboda haka kodama ace,kamar yadda Ahlus-sunna,suka tafi a kai,na cewa,wai Manzon Allah[s]bai khalifan tar da kowaba,ya bar al-umma ne ta zaba.To ashe ire-iren wannan matsayi na Imam Ali[AS]wadanda Manzon Allah,ya fadi game da shi,basu isa su can-cantar dashi ba,khalifan Manzon Allah?To ballantana kuma shine Manzon Allah,ya nasabta.Saboda haka Imam Ali[AS] shi ne ka dai ya cika sharuddan da Shi'a da
sunnah suka tafi akai,na zama khalifa,in ka tafi akan nassi,ba zabin mutane ba,to yana da nassi akai,in katafi akan zabin mutane ne,to shi jama'ane suka
zabe shi.

Ku biyo mu bashi don cigaba daga inda muka tsaya.

____________
sakina Ahmad
Seen by Sakina Ahmad at 5:14 AM



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post