AUREN IMAM ALIYU DA SAYYIDA FATIMA AKWAI DARASI MAI GIRMA A CIKIN AUREN.

Sheikh Zakzaky yana ganawa da Sharif a gidansa kafin wakiyan Gyellesu.


Daga shafin Ma'asumah Nigerian News Updates,
Tare da ---Idishia Jos.

Aure ne mafi girma da daukaka, wanda Allah (T) ne ya daura. A ranar 1 ga Zulhajji ya zama daidai da irin ranar da aka daura Auren Sayyida Fatima da Mijin ta Zakin Allah Imam Aliyu (As). Sayyida Fatima ga ta nan tana matashiya mai cike da annuri, wadda ta tattaro daraja, kyau da daukakar matsayi, ta rayu a hannun mahaifinta a Madina. Sai hankula suka fara kowama gare ta, wasu Sahabbai suka fara tunanin samun dacewar aurenta, da samun daukakar nasaba ta hanyar samun dangantaka da babanta. Wanda dai ya fara zuwa neman auren ta shi ne halifa Abubakar, sannan sai Umar bin Khaddab, wasunsu kuma suka biyo baya.

Sai dai Manzo (S) ya yi ta ba su uzurin rashin amsa bukatunsu da cewa: "Hukunci bai sauko ba tukuna". Daga nan sai Ali ya yi tunanin neman auren Fatima, don haka sai ya tashi ya yi wanka sannan ya yi alwala ya kuma yafa mayafinsa ya yi nafila raka'a biyu, sannan ya sa takalmansa ya doshi Annabi (S) a lokacin yana dakin Ummu Salama. Ya yi sallama, Manzo ya amsa masa, sai Imam ya zauna a gaban Manzo ya dukar da kai kasa; sai Manzo ya ce masa: "Ka zo da wata bukata ne?" sai Imam ya ce: "Na'am, na zo neman auren 'yarka Fatima ne; ko za ka aurar min da ita ya Manzon Allah?" Sai Ummu Salama ta ce:"sai na ga fuskar Manzon Allah ta cika da annuri na farin ciki da murna, sannan ya kalli Ali ya yi masa murmushi.

Daga nan sai Manzo (S) ya shiga wajen Fatima ya ce mata: "Ali bin Abi Dalib, wannan da kika san kusancinsa da darajarsa aMusulunci, ya zo yana zance a kan al'amarinki (wato yana neman auren ki). Hakika kuwa da ma ni na roki Ubangijina da ya aurar da ke ga mafi alherin talikanSa kuma wanda Ya fi so daga cikinsu. To me kike gani?" Sai ta yi shiru. Sai Manzo (S) ya fita yana cewa: "Allahu Akbar! Shirunta yardarta ne". Sannan ya cewa Imam Ali (aA.s.): "Ya Ali, shin kana da wani abu da zan daura maka aure da shi (sadaki)?".
'Yan uwa Sharif ai da suka je ziyarar Sheikh Zakzaky 

Sai Imam Ali (a.s.) ya ce: "Sai takobina da garkuwata, sai kuma rakumina na ban ruwa ", (a wata ruwayar an ce doki ne maimakon rakumin). Sai Manzo (S) ya ce: "Amma takobinka kana da bukatarsa, kana yaki da shi a tafarkin Allah kuma kana kashe makiya Allah da shi. rakuminka kuma kana shayar da (gonar) dabinonka da shi, haka kana daukar kaya da shi, kuma yana daukarka a tafiye-tafiyenka. Don haka je ka yi yadda za ka yi da garkuwarka".
Sai Imam Ali (As.) ya je ya sayarwa Usman bin Affan da garkuwarsa a kan farashin dirhami 480, sai ya kawo wa Manzo .

Daga nan Manzon Allah (S) ya sanar da Musulmi zancen auren, ya kuma cewa Ali (As.): " Allah Ya hore ni da in aurar maka Fatima a bisa nauyin miskali dari hudu na azurfa ) in ka yarda da haka". Sai Imam ya amsa da cewa ya yarda, don haka sai Annabi ya yi masu addu'a da cewa:
"Allah Ya hada kanku, kuma Ya ba ku sa'a, Ya kuma albarkace ku, Ya fitar da tsarkaka masu yawa daga gare ku". Anas bin Malik Ya kasance yana cewa: "Hakika kuwa Allah Ya fitar da tsarkaka da yawa daga gare ku ". Manzon Allah (S) ya aurar da Fatima da sadaki madaidaici, ya saya mata kayayyakin da suka yi daidai da wannan sadaki, don zamuna masu zuwa su ga cewa abin duniya fa ba kome ba ne a wajen mutuntaka da daukakar kamala.


Manzo (S) ya karbi madaidaicin sadakin daga Ali bin Abi Dalib (As.), sai ya dauki nauyin shirya 'yarsa da tanajin kayan gidanta wanda ya kunshi 'yan kayayyaki kadan amma cikin daraja da daukaka. Sai ya aiki wasu Sahabbansa kasuwa don sayo mata (Fatima) abubuwan da sabon gidanta ke bukata, da suka kunshi shinfidu da lullubi da sauran bukatun gida da kayan girki tare da wasu 'yan suturu da turare.

Bayan wata daya (da daura aure), sai Manzo (S) ya fahimci bukatar Ali (A.s.) na tarewar Fatima a sabon gidanta, don haka sai ya amsa wannan bukata. Sai himmatuwa da al'amarin Fatima (AS) ya karu a wajen Manzo (A), don ya musanya mata fakuwar mahifiyar nan ta ta mai tausayi (wato Khadija), a wannan sha'ani da uwa ke da matukar muhimmanci.

Don haka sai ya sa hannu da kansa a al'amarin sa Fatima a lalle. Ya nemi matansa da su shirya ta kamar yadda ake shirya 'yan mata a daren tarewa. Bayan nan sai Manzo ya hada walima da sanar da aure, Muhajirai da Ansar sun sami halartar wannan taro na farin ciki. Wannan bai zama wani sabon abu ba, himmatuwar Manzo da al'amarin Fatima bai kasance don kusanci da dangantakarsa da Ali da Fatima ba; a'a wannan bayar da muhimmanci ya samo asali ne
saboda fadadar reshen Annabci da bishiyar Imamanci ta wannan iyali mai albarka. Saboda Allah Ya so aurar da zababbiyar mace kuma tsokar Annabi, Fatima, ga zababben mijinta, Ali.
Don kuwa Ali (a.s.) ne wanda Manzo (s.a.w.a) dangane da shi yake cewa: "Ashe ba ka yarda ka zama a wajena irin yadda Haruna ya kasance a wajen Musa ba, in ban da cewa kawai babu Annabi a bayana ba ".

Fatima kuwa ita ce wannan da Manzo (s.a.w.a) dangane da ita ya ke cewa: "Ashe ba ki yarda ki zama shugabar matan duniya ba". Don haka su biyun sun kasance wadanda Manzo (s.a.w.a) ya fi so daga mutane kuma wadanda suka fi kusa da shi. An taba tambayarA'isha kan mutumin da Manzon (s.a.w.a) ya fi so, sai ta amsa da
cewa: "Fatima". Sai aka ce mata: daga maza fa? Sai ta ce: "mijinta, a iya sanina bai kasance ba face mai yawan salla sa azumi ". Haka Allah Ya so zuriyyar ManzonSa (s.a.w.a) ta fadada ta hanyar Ali da Fatima (a.s.), ya zama sun sami Hasan da Husaini, shuwagabannin samarin gidan aljanna, da sauran tsarkakan Imamai masu shiryar da wannan al'umma.

 Wannan babban sirri ne yasa auren Fatima (a.s.) ya kasance bisa horon Allah Madaukaki, Manzo (s.a.w.a) bai gabatar da shi ba kafin umarnin Ubangijin, bai yi wani abu ba har sai da hukuncin Allah ya sauko, kamar yadda ya tabbatar da haka da kansa.

     --Idishia Jos.

 #FreeZakzaky.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post