ABUBUWAN DA AKE YI DON NEMAN HAIHUWA
Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Muh'd Suleman
Duk da kwaɗaitarwar da Addinin Musulunci yayi mana dangane da neman haihuwa, to kuma Allah ya san tana iya yiwuwa ya zama ka kwaɗaitu ka gamsu da hakan, kana kuma buƙata, amma ya zama wani dalili ya hana ka samun haihuwa to anan ma Musulunci bai barka haka cikin ƙunci da damuwa ba, domin akwai hanyoyi da dama da Addini ya tanadar maka don nema ko samun haihuwa, waɗansu suna da dangantaka da Abinda zaka ci ko sha, waɗansu kuma Addu'o'i ne, waɗansu kuma Salloli ne, kuma Manzon Allah (saw) da Iyalan Gidansa (As) duk sunyi bayanin waɗannan hanyoyi dalla-dalla.
An ruwaito cewa Imam Ali (As) yana cewa "wani Annabi daga cikin Annabawa ya koka kan ƙarancin Haihuwar Al'ummarsa ga Allah Ta'ala sai Allah ya umarce shi da ya umarce su da riƙa cin ƙwai. Sai suka yi hakan, sai haihuwa ta yawaita a cikin su" (bihar juzu'i na 104 shafi na 79, hadisi na 7)
Kuma an ruwaito
Imam Sadiƙ (As) cewa " wani Annabi daga cikin Annabawa ya koka ma Allah ƙarancin haihuwa, sai Yace masa ka yawaita cin ƙwai (bihar, juzu'i na 104 shafi na 79 hadisi na 8).
Kuma yakan kasance wani lokaci rashin ƙarfin jima'i shike kawo matsalar rashin haihuwa. To idan ya zama haka ɗin ne ma Imaman Ahlul-Baytee (As) waɗanda magadan Manzo (saw) basu bar mu haka ba, domin an ruwaito daga Imam Ridha (As) cewa "wanda yake cin ƙwai da albasa da mai, ƙarfin Jima'insa zai ƙaru" (bihar juzu'i na 104, shafi na 84, hadisi na 14)
Kuma an ruwaito daga Imam Sadiƙ na cewa "kwalli (tozali) yana ƙara ƙarfin kwanciya (bihar juzu'i na 104)
Wani mutum ya tambayi Imam Sadiƙ (As) Yace " Allah ya azurta ni da kuyangi, ina so ka sanar dani wani abu da zan samu ƙarfi akansu, sai yace ka sami farar albasa ka yayyanka ta, sannan ka gauraya ta da mai, sai ka sami ƙwai ka fasa a cikinsu ka kawo Ɗan gishiri ka zuba, sai ka dafa su, ko ka soya su, sai kaci" Ishaƙ yace sai na aikata haka, sai ya zama ba Abinda zan nema awajensu face na same shi, (bihar juzu'i na 104, shafi na 83 hadisi na 33)
Kuma daga gareshi (As) cewa "madara tana amfani ga wanda shi bashi da yawan Maniyyi (bihar juzu'i na 104, shafi na 83 hadisi na 36)
Kuma daga gareshi (As) daga Imam Ali (As) cewa " Gashin namiji ba zai yi yawa ba, face sha'awarsa ta ragu ( bihar juzu'i na 104 shafi na 87 hadisi na 52)
Kuma an ruwaito cewa Imam Baƙir (As) yaje ganin Hisham Ibn Abdulmalik, bai samu ganinsa da wuri ba har ya damu, to a cikin masu tsaron Hisham ɗin akwai wani mai dukiya, amma bai taɓa haihuwa ba, sai Imam yaje kusa dashi yace shin bazaka bani dama in gan shi ba? In sanar dakai wata Addu'a da zaka sami haihuwa? Sai mai tsaron yace na yarda. Bayan ya shiga ya fito, sai mutumin yace Ya Shugabana, Addu'ar da kace zaka bani fa? Sai Imam yace haka ne kullum safe da yamma kace Subhanallah 70, Istigfari 10, sai ka sake yin tasbihi 9, sai ka cika na goman da waɗannan ayoyin na suratu Nuh Aya ta 9 zuwa ta 11, sai wannan mutumin yayi hakan, sai Allah ya azurta shi da zuriya mai yawa. ( bihar juzu'i n'a 104 shafi 5 hadisi 46)
Kuma wani mutum yace wa Imam Sadiƙ (As) ban sami haihuwa ba, sai yace "ka riƙa Istigfari ga Allah.
Kuma Imam Sadiƙ (As) ya gaya wa wani mutum da yake son haihuwa "idan ka zo Jima'i da matarka ka karanta wannan aya ta Suratul Anbiya aya ta 87 ƙafa uku (Makarimul Aklaƙ shafi na 225)
Wani ya koka wa Imam Ridha (As) wani ciwo dake damunsa, kuka gashi baya haihuwa, sai ya umarce shi daya ƙwala kiran Sallah a tsakar gidansa, sai yayi hakan, sai ciwon ya warke, kuma ya sami haihuwa, (wasa'il juzu'i na 15, shafi na 109, hadisi na 1)..
waɗannan kaɗan ne daga cikin abubuwan da aka ruwaito dangane da magance matsalar Haihuwa.
Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Muh'd Suleman
08132933333
Tags:
Taskar Ma'aurata