Ranar Litinin Mai Zuwa Za'a Yanke Hukunci. ZAMAN KOTUN KADUNA KAN SHARI'AR MALLAM ZAKZAKY



Yau an shiga kotu don gabatar da neman a ba su Mallam Zakzaky da Malama Zeenah dama su fita kasar waje neman magani saboda tsananin rashin lafiya.

*Alhamdu lillahi* Allah Ya nufa duk da makarkashiyar azzalumai, an gabatar da wannan nema. Babban Lauya kuma mafi shahara a fagen 'yancin bil adama a Nahiyar Afirka Ta Yamma Mr Femi Falana SAN ne ya gabatar da neman a kotun. Baba Falana ya kwashe kamar awa daya da rabi yana jawabai na shari'a. Ya gabatar da takardun likita (Medical Report) guda 8. Su kuwa bangaren masu adawa ko katin asibiti basu kawo ba balle rahoton likita.

Bayan zaman Falana sai Babban Lauyan Gwamnati DPP Bayero Dari ya mike don ya yi martani ga jawaban Falana. *Alhamdu lillahi* a nan muka ga tasirin addu'o'in 'yan uwa. Don kuwa duk sai ya daburce ya rika kame kame, ya kasa kawo wata magana mai kwari. Har sai da yan uwan sa suka rika tallafa masa. A karshe dai ya buge da debo maganganun su Garba Shehu yace suna tsoron wai in aka bar Mallam ya fita ba zai dawo ba.

Sai Falana ya sake mikewa ya kacaccala 'yan jawaban Bayero Dari. Yace a yadda aka tsaya kamar ba a yi wani martani ga neman da yayi ba.

Daga nan sai Alkalin yayi magana, yace duk inda aka ce an share awa kusan 3 ana mai da jawabai, ba zai yiwu ya iya yin hukunci nan take ba. Saboda dole a hukuncin nasa sai ya tsettsefe duk batun da kowane bangare yayi. Don haka yace manyan Lauyoyi suyi hakuri su dawo ranar Litinin don karbar hukuncin sa. Sannan yayi alkawarin yin adalci.

Yanzu dai yan uwa kar a gaza da addu'a. A yi tayi har mu samu hukuncin da muke bukata. Musamman ma da yake zuwa yanzu har ofishin Falana sun fara shirya takardun da zasu kalubalanci haramtacciyar dokar nan ta wai haramta Harka Islamiyya.

*Barrister Haruna Magashi*
_*290719*_

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post