YAN SHI'A SUN SAKE GABATAR DA SALLAH A KOFAR MAJALISAR TARAYYA

YAN SHI'A SUN SAKE GABATAR DA SALLAH A KOFAR MAJALISAR TARAYYA
 🇳🇬MA'ASUMA NIGERIAN NEWS UPDATES

 A yau Alhamis 4 ga watan July 'yan uwa almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub Al-Zakzaky (H) sun fita Muzaharar kira ga Azzalumar gwamnatin Nigeria da ta gaggauta sakin Jagoran nasu da ake cigaba da tsare shi tun shekaru hudu da suka wuce.

Akalla Shekaru biyu kenan Mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky din suke gabatar da ita wannan Muzahara a garin na Abuja dama sauran garuruwa. A yau mu kuma Muzaharar an fara ta ne daga Federal Sectarian inda aka yita zaye Eagle Square har sau Uku, sannan daga karshe aka shiga Majalisar Tayyayya.



 Bayan shiga Majalisar kasar ne al'umma suka fusata sosai, matasa  na fadin dole a saki Sheikh Zakzaky. Anan ne 'yan uwa suka gabatar da sallar azhar da la'asar a muhallin na majalisa, daga baya sai wani daga cikin 'yan majalisu mai suna Alhassan Ado Doguwa ya fito domin yaji dalilin zuwa wannan guri.
Kafin fara Jawabin Hon. Alhassan Ado Doguwa an gabatar da wani daga cikin 'yan uwa akan ya fadi makasudin zuwa wannan guri, wanda yayi jawabai sosai da harshen turanci. Bayan hakan ne Dan majalisar ya karbi abin magana yayi yi wasu jawabai. Daga karshe aka rufe Muzaharar lafiya kamar yanda aka fara lafiya.
Daga wakilanmu:
- Ammar Umar Udawa
- Ibrahim Almustapha Saminaka
- Mudassir Bara'a Malumfashi
- Marwan Habibu Isah

 — 4/July/2019
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post