"Yan Shi'a a garin Shinkafi sun Aika da Manyan makaman da suka Rika ga Azzaluman da suke tsare da jagoran su.


Daga Ma'asumah Nigeria News Updates


A yau Lahadi ne Mabiya mazhabar Shi'a a garin Shinkafi ta jihar Zamfara sun gabatar da zafafan Addu'o'in ga Wadanda suka Cutar da jagoran su tare da yiwa jagoran nasu Shekh Ibrahim zakzaky (h) Addu'ar neman lafiya wadda yake fama da ita tun bayan da harin da sojoji Nigeria Yan Ina da kisa suka Kai masa a gidansa inda suka kashe masa 'yar yar 3, da kashe masa Mabiya fiye da Dubu tare da jikkata daruruwa da Kama Wasu da ransu, daga ciki akwai Jagoran nasu Sheik Ibraheemm zakzaky da Mai dakinshi malama zeenatudeen Ibraheemm da take dauke da harsasai  da raunika ajikinta har yanzu.

Inda a yanzu malamin  yake fuskanta jinya Mai tsanani a inda yake tsare.

 A Satin da yawuce ne Mabiyansa sukayi fira da manema labarai suka  fitar da Sanarwa akwai guba Mai tsanani ajikinsa, tun bayan da kotu ta bada umurnin likitoci su taho Daga waje su duba, bayan dubasu suka sanar da ayi gaggawar fita dasu a waje domin nema masu lafiya, Amma gwamnatin Nigeria tayi shiru taki ko inkula Akan wannan lamari.
Mlm Qaseem shehu Shinkafi Kennan Wakilin Yan uwan na garin Shinkafi

A lokacin da Wakilin Yan Uwa musulmi na Shinkafi yake jawabin a wajen Addu'o'in da suke gabatarwa din yake cewa:- Dole NE mudauki makaman Add'a Kuma muyi aiki sai Allah ta'alah ya tausaya Mana , domin  nema NE muke a wajen Allah (t) Kuma Mai nema baya gajiyawa Akan wannan bawon Allah na Allah da girmanshi da daukaka shi a wajen Allah (t)) aka jarabtashi da manyan-manyan jarabawar da akayiwa Annabawa da mursilan bayi,  kuma Allah ya jarabci su mlm da wannan fir'auna Mai tsananin Taurin Kai dai rashin rabo Duniya da lahira. Dukkan abunda yai farko lazeem ne yayi karshe, akwai bukatar muci gaba da juri'a muci gaba da dakewa hanyar Kenan koda hidimar neman Duniya mutun zaiyi sai yasha wahala da bakin ciki da sauran abubuwa kala-kala, Balantana ma mutun hanyar Zuwa lahira domin neman tsira a wajen Allah (t)..........

Kuma akwai Sanarwar da kingin 'Dan Shehin Malamin da ya rage a Duniya ya fitar A yau a social media inda take cewa:-


Daga Mohammed Ibraheem Zakzaky

A wannan Asabar din 6 ga watan Yulin 2019, na samu haduwa da Mahaifina da Mahaifiyata. Kamar dai yadda a ka bayyanawa mutane, rayuwar Mahaifina na fuskantar barazana daga gubar da ta tasirantu a cikin jininsa. A sanadin wannan, dukkan kwararrun da muka tuntuba dangane da rashin lafiyan sun bayar da shawarar dole a gaggauta kwantar da Mahaifina a asibitin da ke da wadatattun kayan aiki domin a iya ceton ransa. Wannan a na maganar sama da wata guda da ya shige, amma har yanzu din nan shiru ka ke ji, ba abin da a ka yi a kai.

Mahaifiyata kuwa, wacce tun da dadewa an san irin cututtukan da ke damunta, har wa yau babu wata kulawa da ta samu kamar yadda kwararru suka yi bayani. Irin radadin da ta ke fama da shi daga cututtukan a bayan duk wata, ya dawo yana addabarta a kowacce rana. Kuma fa har yanzu ba a dauki hanyar magance ko daya cikin wadannan cututtuka ba.
Da muka hadu, bayan irin tabarbarewar rashin lafiyar mahaifina da muka iya lura da shi kamar yadda hakoransa suka sauya suka yi bakikkirin, ya sanar da ni cewa, lamarin jikinsa ya sake tabarbarewa ne fiye da lokutan baya da muka ziyarce shi. Abin ban tsoron shi ne, jikinsa ya fara yin yanayi sak da lokacin da ya kamu da matsalar shanyewar barin jiki a watan Janairun 2017. Wanda a baya, sai lokacin bayan lokaci ne yake fama da matsanancin radadi, amma yanzu kusan kullum ne.

Duk da dai bana son cire tsammani, amma a irin halin da a ke ciki, ina tunanin zai yi min wahala na iya ceton rayuwar Mahaifina, saboda duk wata hanya da muka bi wurin ganin an ceci rayuwarsa sai an dakusheta ko an haifar mata da matsala da gangan. A shekarun baya na fadi cewa, akwai shirin kashe Mahaifana ta hanyar yin biris da lamarin tabarbarewa rashin lafiyarsu, duk da a wancan lokacin ban san irin tsanantar cutar nasu ba. Kawowarsu yanzu a raye, abin al’ajabi ne wannan daga Allah.

Daga bayanan da na tattara daga wurin qwararru a makonnin da suka gabata.

Wadannan sune jawabin da Dan sheik zakzaky na farko da ya rage a Duniya yayi a shafinsa a social media.


Da hakan Yan shi'ar ke Kira da gwamnatin Nigeria akan ta sakar musu Malamin su Sheik Ibraheemm zakzaky (h)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post