Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates tare da -Idishia Jos.
Motar Jami:an tsaro kafin su fara harbi akan 'yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky yau a Abuja. |
A wannan shekarar gidan rediyo na BBC suka tafka sharri wai mun yi arangama da jami'an tsaro shiyasa suka kashe mabiya Sheikh Zakzaky a garin Zariya. A yau Talata sun kara yin wata sharrin da nufin jingina wa Harka Islamiyya ta'addanci da Makamai. Sanin kowa ne ba yau muka fara Muzaharar lumana a garin na Abuja ba, wanda aka shafe sama da shekara ana yi kullu yaumin don ganin an saki Sheikh Zakzaky da iyalinsa.
Gidajen Jaridu na Yanar Gizo musamman Jaridar Punch da Premium Times sun rawaito cewa " 'Yan Shi'ah sun harbe masu gadin Majalisan Kasa har sun harbi mutane Uku, sun kashe mutum Daya ya mutu sauran kuma an garzaya dasu Asibiti domin kula da lafiyansu." Wannan kuma ba gaskiya bane saboda hujjoji da dalilai ya gabatar da cewa sune suka kashe mana mutane kuma sune suka harbe mu ga "Video" ga hotuna nan duniya ta gani.
Idan gaskiga ne 'yan Shi'a sun harbe masu gadin Majalisan Kasa, ina abinda za'a nunawa mutane su yarda alhali mutane sun tabbatar 'yan Shi'a aka harba kuma aka raunata. Daman sun tabbatar cewa zasu kashe mutane musamman masu rubuta Animal Buhari FreeZakzaky a jikin gini. Sau da dama sun sha afka mana a lokacin da ake gudanar da muzaharar FreeZakzaky a cikin Abuja, a rana tsaka a yayin tattakin Yaumul Arba'een sun kashe mana mutane Almajiran Sheikh Zakzaky sama da 40.
To muna kara fada wa duniya cewa, muna nisanta kammu da wannan ta'addanci da suke jingina mana. Ai zanga-zangan lumana muke kuma a doka da Shari'aya yin zanga-zanga bisa ka'ida ba haramtaccen abu bane a dokokin kasar nan, don haka idan mun yi zanga-zanga na lumana kuma aka bude mana wuta aka kashe mu wannan shine dokar da gwamnati ta tanadar kenan akan hakkin 'yan Kasa??? Su gidajen jaridun da suke ce mun harbi masu gadin Majalisan Kasa in dai haka ne me yasa basu nuna duniya hotunan wanda aka harba na daga jami'an tsaro ba sai namu da aka harba ???.
Dole ne muyi magana mu tsaya akan 'yancin mu mu fadawa duniya abinda aka mana na zalunci da danniya, tun na Zariya har na Abuja. A matsayin mu na 'yan Adam wanda kasa ta basu 'yancinsu zanga-zanga lumana da muke yi ba zamu daina ba har sai an saki jagoranmu Sheikh Zakzaky (H). Duk abinda zasu mana sai dai suyi amma kiran asaki Zakzaky da iyalinsa wajibi ne mu cigaba dai dai su karar damu baki daya.
Muna sanar da Gwamnatin Buhari azzalumi, Gwamanatin Buhari wanda yake Criminal, Gwamanatin Buhari wanda yake tauye hakkin bayi a wannan kasa muna sanar dasu cewa lallai ba zamu ja da Baya ba akan al'amarin Malam. Dukiyan mu da 'ya'yan mu gaba daya fansane ga rayuwan Malam da mutuncin Malam, don haka akan Malam kada kuyi tsammanin zamuyi sassaucin abinda ya same shi. Don haka zamu fito ba dare ba rana insha Allahu zamu cigaba da gwagwarmaya da fafatawa har sai munga abinda zai kasance na fitowan Malam daga hannun wannan Azzalumai.
--Idishia Jos.
#FreeZakzaky.
Tags:
#FREE_ZAKZAKY