'YAN-IZALA SUNA KAFIRTA MAHAIFAN ANNABI MUHAMMADU (S) NE SABODA TSABAR JAHILTAR DA SUKA YIWA AL-QUR'ANI MAI GIRMA !

'YAN-IZALA SUNA KAFIRTA MAHAIFAN ANNABI MUHAMMADU (S) NE SABODA TSABAR JAHILTAR DA SUKA YIWA AL-QUR'ANI MAI GIRMA !
MA'ASUMIYYA NIGERIA NEWS UPDATE  DAGA WAKILINMU
SHARHABIL USMAN PANDOSS



Idan ka ta'ba 'Yan-izala, sai su nemi kafa maka hujja da cewa wai ai ba a kan Annabi Muhammadu (S) aka fara samun haka ba, sai su nemi kafa maka hujja da cewa WAI mahaifin Annabi Ibrahim (A) ma mushriki ne !
Wanda wannan yake dad'a tabbatar da jahilcin 'yan-izala, domin kuwa sun kasa sanin cewa mahaifan Annabi Ibrahim muminai ne fa, Malamai sun tabbatar da cewa MAHAIFIN ANNABI IBRAHIM SUNANSA TARUKH KUMA MUMINI NE !




.
Ayar da ta dad'a tabbatar da hakan ta hanyar addu'ar da Ibrahim (A) ya yiwa Mahaifansa (WALIDAIHI) ba 'Dan-uwan babansa Aazara (ABIHI) ba !
.
Ga ayar:
،
ﺎَﻨَّﺑَﺭ ْﺮِﻔْﻏﺍ ﻲِﻟ َّﻱَﺪِﻟﺍَﻮِﻟَﻭ َﻥﻲِﻨِﻣْﺆُﻤْﻠِﻟَﻭ َﻡْﻮَﻳ ُﻡﻮُﻘَﻳ ،ُﺏﺎَﺴِﺤْﻟﺍ
،
Fassarar wannan aya ta Suratu Ibrahim aya ta:
41. "YA UBANGIJINMU KA YI GAFARA GARE NI, KUMA GA MAHAIFANA, KUMA DA MUMINAI, A RANAR DA HISABI YAKE TSAYUWA"




.
'Yan-izala basa ganin wannan addu'ar da Annabi Ibrahim (AS) ya yiwa Mahaifansa Muminai, da haka suke ganin cewa ai Mahaifan nasa kafirai ne.
.
Kawai don 'YAN-IZALAR SUNA SON KAFA HUJJA DA HAKA SU KAFIRTA MAHAIFAN ANNABI MUHAMMADU (S) !



.
A inda 'Yan-izalar suke ganin cewa ai wannan addu'ar ta Annabi Ibrahim (A) ya yi ne kafin a hana Shi yiwa mushrikai addu'a ko da kuwa makusanta ne !
To, su dai mushrikan da aka hana yiwa addu'a, to lalle ba mahaifan Annabi Ibrahim (A) bane su, lalle 'Dan-uwan mahaifin Annabi Ibrahim ne mai suna Aazara wanda Annabi Ibrahim d'in ya dinga yi mar wa'azi, amma Aazara ya nuna fushi, sai Ibrahim (A) ya lallashe shi a inda Allah yace
،
ﻝﺎﻗ ﻡﻼﺳ ﻚﻴﻠﻋ ﻚﻟ ﺮﻔﻐﺘﺳﺄﺳ ﻲﺑﺭ ﻪﻧﺇ ﻥﺎﻛ ﻲﺑ ﺎﻴﻔﺧ
،
Fassarar wannan aya ta cikin Suratu Maryam aya ta:
47. "(Annabi Ibrahim) Yace, 'Aminci ya tabbata a gare ka ! Zan nemi Ubangiji Ya gafarta maka. Lalle Shi Ya kasance Mai girmamawa gare ni'.




Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post