Taron Tunawa Da Shahid Aliyu; MUNYI BABBAN RASHI MAI WUYAR CIKE WA.



Daga shafin Ma'asumah Nigerian News Updates,
Tare da -Idishia Jos.

Shahid Aliyu Sulaiman Rinji yana daga cikin wanda 'Yan Sanda Nigeriya suka shekar da jinanen su a wakiyan da ya faru a garin Abuja. Bayan dirar mikiya da tawagan 'Yan Sanda suka musu a lokacin da ake Muzaharar Lumana na FreeZakzaky. A jiya aka gudanar da Addu'a na cikar su kwanaki Bakwai da Shahadansu, bayan an kammala addu'oi sannan kuma aka yi Jawabai na Zikiran Tunawa da shahadansa. Manyan baki daga garuruwa da dama ne suka samu zuwa wajen zikiran kuma al'umma gari da ma sauran 'yan uwa daga fannoni daban-daban ne suka zo wajen wannan taro da aka yi.

Biyo bayan 'yan uwansa da mahaifiyarsa da suka yi magana a wajen taro akan rayuwan Sidi Aliyu Rinji, abokansa ma sun yi bayani irin yadda yake nuna shaukin shahada a kowanne lokaci. Daga cikin manyan baki da suka gabatar da jawabi a wajen  Sheikh Adamu Tsoho Jos shine ya gabatar da jawabi na musamman akan Sidi Aliyu dama Harka Islamiyya baki daya. A cikin Jawabinsa yace Ita Shahada Baiwa Ce Kuma Zabi Ne A Wajen Allah (T)! Allah madaukakin sarki yana fada a cikin littafin sa mai sarki Alqur'an yana cewa: " karku kira wa yanda aka kashe a tafarkin sa matattatu, Aa su rayayyayu ne a wajen Ubangijin su."

Shehin malamin ya kara da cewa Nan ga yan Niger Delta suma yanzu biyansu akeyi, ga yan kidnapping suma an kyale su suna abunda sukaga dama, ga kungiyoyin ta'addanci nan da dama gwamnati taki ta dauki mataki akansu. Amma kunga shi Malam Zakzaky (H) an zalunce shi an kashe masa yayansa shida da almajirai da yan'uwa. Sannan aka kama shi tareda raunukan dake jikinsa shi da mai dakinsa Malama Zeenatuddin aka tsaresu, tsawon shekaru hudu kenan yanzu.

Kuma kusani tsakanin mu da ku sedai sakayyar Ubangiji, sannan ku gayawa iyayen gidanku duk abunda suka aikata zasu fada a gaban Allah (swa). Kuma duk abunda mukeyi bazamu fasa ba saboda mu addini mukeyi ba duniya mukasa agaba yardar Allah muke nema. Allah ya tarwatsa wannan gwamnati ta Buhari da magoya bayansa, yakuma bawa su Malam (H) lafiya ya kwato mana su daga hannun Azzalumai.

Bayan Sheikh Adamu Tsoho ya kammala jawabin sa, an samu isowan manyan baki Sheikh Abdulhhameed Bello Zariya da Sayyid Badamasi Yakub 'Dan uwa ga Sayyid Zakzaky (H). Sheikh Abdulhameed Bello shima yayi jawabi a wajen bayan isowansu inda yake cewa; Inna lillahi wa Inna Ilaihirraji'un yana mika ta'aziyya ga 'yan uwa da iyaye akan rashin da aka yi, lallai muna cikin jarrabawa mai tsananyi amma mun san duk abinda aka mana Allah zai daukan mana fansa akai. Tabbas shahidan mu sun samu daukaka kuma da jinanensu addinin Allah zai tabbata.

Sayyid Badamasi Yakub shima yayi jawabi a wajen harma yake cewa daman yana da masaniya kotu Kaduna Ba zasu bar malam ya fita a jiya ba, Fatan mu dai Allah ya basu lafiya. Shahidan mu Allah ya daukaka ladan shahadansu, daman haka hanyar take. Bayan kammala dukkan jawabai da aka yi a wajen sannan aka wuce ziyarar makabarta inda makwancin Shahid Aliyu yake. A lokacin aka is a makabartan Sheikh Abdulhameed Bello yayi addu'a sannan ya ce Sayyid Badamasi ya kammala rufe Addu'a, inda yayi addu'a aka koma gidan su Shahid Aliyu.

  --Idishia Jos.

#FreeZakzaky.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post