TARIHIN SHAHID SIDI ALIYU HAIDAR IBRAHIM SULAIMAN A TAKAICHE.

TARIHIN SHAHID SIDI ALIYU HAIDAR IBRAHIM SULAIMAN A TAKAICHE.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.
Tare da --Idishia Jos.

Wannan kadan ne daga cikin tarihin Rayuwan Gwarzon shahidin Yankin Jos Sidi Aliyu Sulaiman Rinji, wanda kanin sa Ahmad Ibrahim Sulaiman Jahun ya ambato a yi karatu Lafiya.

HAIHUWARSA da TASOWARSA

Shahid Haidar an haife sa ne ranan 10 ga Rajab 1418 wanda yayi  daidai da ranan haihuwar Imam Muhammad Jawad(AS), a garin Rinji, karamar hukumar Toro dake jahar Bauchi. Sunan Mahaifinsa Dr Ibrahim Sulaiman Jahun, sunan Mahaifiyarsa Mal. Baraka  Aliyu.

Ya taso ne a gaban mahaifan sa tare da so da kauna, wanda ya fara karatun Primary School dinsa ne a makarantan fudiyya primary school da ke nan garin rinji, inda aka haifesa kenan, a chikin daliban ajinsu ya kasanche me kwazo ne da hazaqa wanda kusan ko wani karshen term yakan dauki 1st position ne a ajinsu. Ya zamo a lokachin ko makarantan fudiyya za taje gasan karatu ne ya na daga cikin farkon daliban da ake fara dauka a tafi dasu, dan bana mantawa akwai lokachin da makarantan namu mu kaje  gasan karatu a garin saminaka, wanda ya zamo yana da ga cikin wanda suka chiyo mana na daya a fannin gasan karatu da yashafi addini,  haka zalikata fannin fareti in ana tache wanda suka fi iya fareti a tashin farko shi ake fara cirowa, toh a lokachin se yazamo kaman wani madubi a makarantanmu saboda gashi na da ilimi gashi kuma yafi kowa iya fareti.

Bayan ya gama primary a shekarar 2010 se yasamu daman shiga fudiyya Na tahfiz da yake garin laru itama a nan karamar hukumar toro wanda anan ma haka ya chi gaba da karatunsa a matsayin dalibi da yafi kowa hazaka, saboda rashin lapiya da ya dameshi da ga karshe dai tasa dole se aka chanza masa makaranta izuwa makarantan gida wato day school kenan, wanda a haka ne har ya kammala secondary nasa a makaranta me suna Community Day Secondary School Toro.

 Bayan ya gama secondary din ya samu daman shiga makarantan health tech da yake garin ningi jahar bauchi wanda ko kammala makarantan beyi ba tasa ze tafi iran karatun Addini, lokachin da naji labarin zeje karatun addini a iran nayi farin ciki sosai, har nake cewa yanxu mahaifinmu ze samu magaji na gaskiya dan dama ba wanda yafi chachanta fiye dashi kuma gashi a lokachin ze fara karatun addini. 

A takaiche tarihin haihuwarsa kenan da yanda ya taso.

WAYE SHAHID HAIDAR ?

Toh innache zan tsaya nayi cikakken bayani ne akansa  zan iya kare ini da dare ban rubuta komi akan sa ba saboda yawan kyawawan dabi,unsa.

Haidar mutum ne da ya kasanche me son ibada,  son mutane,  barkwanchi,  kama daga dangin mahaifi har zuwa dangin mahaifiya ba wanda za kaji ya na kushesa, kowa zakaji ya na Allah-Allah yaje gurinsu. Dan tsananin son ibadansa yana zuwa ya ke be kansa shi kadai a wani guri daban na tsahon sati ko ma fiye da haka yana bauta wa Allah dare da rana tare da yin Azumi a kowache rana, haka zalika yakasanche mesan tsayuwan dare a rayuwarsa, dan baya yiwu wa a che rana tazo ta wuche be tashi da dare ya bauta wa mahaliccinsa ba. Ya zamo ko lokachin da matasa sukeyin lailatul tarbiyya ne kana ganin kiran shi ya shigo wayarka da dare ranan Alhamis toh kasan tuni ze maka.

Haka ta fannin ziyaran makabarta kafin shahadarsa ya zamo wanda kullum ko wache juma,a yake jagorantan daliban fudiyyah zuwa wannan kyakkywan aiki, ko da kuwa wani irin uzuri yake dashi ze bari ya taho a tafi ziyaran makabartan dashi, har se anyi ziyaran makabartan angama lapiya, yawanchin adduansa bayan angama ziyaran shine ALLAH KA BAMU SHAHADA BIhaqqi sayyid Ahmad, Hamid wa Mahmud,  gashi Allah ya karbi adduan shi.

Bangaren fita muzahara kuwa da bada chaji ba se na gaya maka ba dan tun a farko na gaya muku shine me zuwa na daya a screening na fareti wanda yasa a kowache muzahara in an fita zaka sameshi ne a gaba yana commanding na daliban fudiyya ko kuma ka same shi ta fannin matasa yana bada slogan.

Akwai lokachin da yake ce mun sidi, yaushe zaka shiga Abuja ne, nache masa yasan yanayin makarantan mu (ATBU)  ba na wasa bane, amma in allah ya yarda duk lokachin da  na samu dama da zan shiga,  se yake cemun ko kaifah, a matakin yanxu yancin jagora shine fiye da komi dan ko kayi karatun ma in ba sayyid ba tada amfani, toh kusan kowa a garinmu in ka kaji yana ma maganan zamu tafi a Abuja to za kasamu Shaheed Haidar ne ya karfafa masa  gwiwa alhali duk da baya kasan tamu yana chan kasar iran yin karatu.

 SHAHADARSA!

Shaheed Haidar yayi shahada ne Ranan 22 ga watan july a shekar 2019 a secretariat dake abuja bisa zalunchin sojojin Nigeria wanda uban gidansu criminal Buhari yke basu umarni, yayi shahada akan kwatan ma jagora yancinsa da ake tsare dashi ba bisa ka,ida wajen shekara hudu kenan tun bayan wakian zariya bayan an kashe masa akalla dubu daya da kuma yaransa guda uku a gaban idonsa. 

Daf kafin dawowansa daga makaranta muna hira da shi se yace mun ze dawo gida fah, na ce masa gida kuma ko shekara baka yi ba a makarantan, har nake zolayqnsa nache masa ko dai anti ze mana ne yake son dawowa, se yache mun wa ya gaya maka ni SHAHADA zan dawo yi, se nake che masa aishi maganan ka wo mana aunty wani abu ne da zaka tsara shi wa kanka kqche zuwa lokachi kaza zaka yishi,  shikuma shahada ba asan takamammen lokachi in lokachi yayi kawai ana tafiya ne,   se yache mun waya gaya ma, ni nasan shahada zan dawo yi, se nache masa toh Allah ya tabbatar mana da haka dan abun farinciki ne a garemu,  se yache mun yauwa ko kaifah ayi ta tayamu da addua yafi ai,  nache masa in sha Allah muma kar ana mantawa damu a adduoi,n.  yanda muka yi dashi knan. Haka wasu abokansa ma za kaji suna gaya ma dan akwai ma wanda yace masa shi halan ma in ya diro Nigeria 🇳🇬  ko gida ba zai je ba ze tsaya a Abuja ne wajen struggle toh be sauka ta Abuja.

 Da yazo gida kwatakwata kwana uku yayi ya tafi Abuja din dan ko dan gin mahaifiya da mahaifnmu be samu daman zuwa gaishesu ba ya tafi abuja din.

Daga karshe yabar mana wasiyya da chewa yan, uwa da abokaina wanda ake wannan harka tare dasu ina muku wasilchi da cewa ku kara kaimi ku kara dagewa kuma duk rintsi duk wuya kar ku taba juya wa jagora baya.

Takaitacchen tarihin Shaheed Sidi  Aliyu Haidar Ibrahim Sulaiman kenan.

Aminchin Allah su tabbata a gareka ranar da aka haifeka, ranar da kayi shahada har zuwa ranan da za, a tashe ka kana mazloomi.

Ga wasu daga cikin hotunan Rakiyan Jana'izar da aka yi har zuwa bnne shi.










# FREE ZAKZAKY
#WE ARE ALL ZAKZAKY
#WE WILL NEVER SURRENDER

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post