-Muhammad Auwal Husainiyya
Sojojin Nigerian sun shafe akalla awa 48 suna kashe fararen hula fiye da mutum dubu (1000+) a garin Zaria dake jihar Kaduna a Shekarar 2015 shugabanni dakuma wadanda ake kira manya a kasar nan sunyi gum da bakinsu ba su ce komai ba dashike akwai Hannunsu a cikin wannan ta'addancin to me zai sa a ga laifin yan bindigar da ke kashe - kashen kare-dangi a yankunan kasar nan musamman a jihohi irin su Zamfara, Sokoto, Katsina, ds. tunda dama da hannun duk Wadanda ake kira manya a kasarnan tun daga kan Shugaban kasa.
Su fa Sojoji da rana tsaka suka fara kashe almajiran Shaikh Zakzaky, Duniya na kallo, har ma Gwamnan Kaduna, Elrufa'i ya zo wajen da suke harbe-harben ya yi magana da su sannan ya wuce suka cigaba da kashe-kashen, suka ma je gidan Shaikh Zakzaky da daddare suka kwana har safiya suna harbi a unguwar, suka kashe daruruwa a wajen gidan, suka jera su a kan layi suka ba mutane dama su sace kayan jikinsu, ashe hakan ba koyawa yan kasa cewa kisa abin kirki bane, tunda ga shi jami'in tsaro kan iya kashe wanda Bai dauke da makami Kuma ya bar kayansa ganima a wajen sauran yan kasa?
Wannan wata ma nuniyace cewa Kisan-kiyashin Zariya shi ya budewa yan bindiga da masu Satan mutane babban kofar cigaba da yin kashe-kashen su tun bayan hawan Buhari.
KARANTA: Laifin Yan Shi'a a Nigeria
Ita rai rai ce, ko wa aka kashe, kuma ko wa ya kashe, ballantana Kuma ya zama kisan nan an yi shi ne a salo iri daya. Da soja da dan fashi duk kisan kai suka yi idan suka kashe yan kasa marasa dauke da makami. Kai wane ma jayayya kake da shi kan cewa masu kashe mutane a Zamfara da Birnin-Gwari su ne suka kashe Musulmi 1000+ a garin Zariya a watan Disambar 2015?,
Kaga wannan yanuna cewa duk wata barna da ta'addancin da akeyi a kasar nan to da hannun gwamnati koma ince gwamnati ce ke sawa ayi shiyasa kullum ayyuka na ta'addanci ke kara ta'azzara a kasar nan sai dai gwamnati tazo tana ta sharara-kare rayi a kafafen yada labarai dasunan suna samar da tsaro.
Allah ya gaggauta kawo mana karshen duk wani tsinannen Azzalumi dake fadin wannan Duniyar.
*Muhammad Auwal Husainiyya*
-30/07/2019.
Tags:
Tunatarwa