- SHARI'A NA SA ALBARKA A ƘASA
Nigeria Ina Mafita Na Sheikh Zakzaky
Ma'asumah Nigeria News update
Ishaq Muh'd Suleiman
Kamar yadda yazo cewa idan Annabi Isah (As) Ya dawo bayan ƙasa (duniya) zai tabbatar da Shari'ar musulunci, wanda a Sanadiyyar wannan, mutane da yawa zasu iya ci daga itace ruman guda, in ka taɓa ganin itacen ruman bai yi tsawon mutum guda ba, ba kuma yana da tsawo ne ba, kuma yana iya yin Ƴaƴa kamar guda goma zuwa sha biyar, to aka ce kamar mutum arba'in zasu sha inuwar itacen ruman ƙwara ɗaya, kuma zasu ci su ƙoshi.
Kuma mutum arba'in zasu iya shan nono daga tunkiya guda ko akuya, wannan kuma akace ba wani abu bane illa (sakamakon) tabbatar da shari'ar Addinin Musulunci, wanda yake sai Allah Ta'ala ya yalwata arziki ya yaɗu, àci kaji da ƙwayaye, kuma Ƴaƴan itatuwa, mutum idan yayi yawo da kwandonsa aƙasan itaciya sai ya cika kwandon da Ƴaƴan itaciya, saboda Albarkacin tabbatar Shari'a.
Kuma yazo a hadisi cewa, duk ran da fajiri ya mutu, to da mutune da dabbobi da tsire tsire suna hutawa, domin fajirci yana sa albarka arziki ya ragu, wato in wannan fasiƙi ne yake ta fasiƙanci, to wannan fasiƙancin nasa na cutar mutane, tunda yake cutar tana rage tsatso na haihuwa, kuma tana sa Ƴaƴan itatuwa su daina Ƴaƴa, ko kuma su daina albarka, kuma yana sa shanu su daina nono mai yawa, sai kaji su daina ƙwai, in fajirci yayi yawa sai arziki ya rinƙa raguwa, kamar yadda in adalci yayi yawa sai arziki ya ƙaru,
Wannan ya nuna ashe yalwatan arziki da ƙuntatuwansa ɗamfare yake da Ibada ta Allah Ta'ala, wato kenan kar mutum yaga cewa mutane sun shiga wani mawuyacin hali ya ɗauka cewa kamar ko rashin iya sanin tattalin arziki ne ko ma menene, a'a ba wannan bane, Al'amari ne daman na Allah wanda yake shi ke yalwatawa, ya kuma takura.
Kamar yadda yake cewa:- duk abinda ya shafe ku na musiba, to abinda Hannuwanku ne suka aikata, "Da kowanne abinda kuke yi zai kama ku, to da ba'a ji daɗi ba, da ko kofin ruwa bazaku samu ba, amma don yana afuwa da dama ne har kukan samu.
Ma'asumah Nigeria News Update
- Ishaq Muh'd Suleiman 08132933333
Tags:
Taskar ilimi