SAI TSANANI YAYI TSANANI TAIMAKON ALLAH KE ZUWA !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
A QARA JURIYA 'YAN SHI'AH
Yana daga cikin dabi'a ta Allah, bai cika kawo taimakonsa ga bayinsa muminai ba har sai tsanani yayi tsanani. Wani lokaci kuma har sai sun yanke tsammani sannan ya kawo musu taimakonsa.
Dalilin wannan hikima tasa (T) kuwa shine don ya daukaka darajar muminai bayan jarraba su, kuma ya azabtar da fajirai, azzalumai da 'Dawagitai bayan sunyi dagawarsu.
Allah (T) na cewa;
" (Bamu kai musu taimakonmu ba) HAR (sai) A LOKACIN DA MANZANNI SUKA YANKE TSAMMANI (da zuwan taimakonmu) KUMA SU KAYI ZATON CEWA AN JINGINA SU GA QARYA (an kunyata su), SAI TAIMAKONMU YAJE MUSU, SA'AN NAN MU TSERAR DA WANDA MUKE SO (cikinku muminai), KUMA BA A MAYAR DA AZABAR MU DAGA MUTANE MASU LAIFI."
(Yusuf:110)
(2)- " KUMA WADANDA SUKA KAFIRTA (irin su Buhari da El-Rufa'i) SUKA CEWA MANZANNINMU (masu da'awar tabbatar da tsarin Allah), " LALLE NE MUNA FITAR DA KU DAGA QASARMU, KO KUMA KU KOMA KAN TAFARKINMU (na bin dokar wanin Allah) " SAI UBANGIJINSU YAYI WAHAYI ZUWA GARE SU, " LALLE NE, MUNA HALAKAR DA AZZALUMAI (irin su Buhari da El-Rufa'i) ."
(Ibrahim:13)
Saboda haka, a qara dauriya, haquri da jajircewa.
(3)- " LALLE MU, HAQIQA MUNA TAIMAKON MANZANNINMU DA WADANDA SU KAYI IMANI A CIKIN RAYUWAR DUNIYA DA RANAR DA SHAIDU KE TSAYAWA (ranar alqiyama don bayar da shaida kan ayyukan kowa) ."
(Ghafir:51)
Shin, akwai wani Manzo ko muminan bayi wadanda Allah bai taimake su ba?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tags:
#FREE_ZAKZAKY