Rohoton BBC; Ban hana 'yan Shi'a yin shi'arsu ba Inji Buhari. Me hakan Yake Nufi ???



Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce umarnin da kotu ta bayar na dakatar da kungiyar IMN bai hana mabiya Shi'a su gudanar da addininsu ba a kasar. Kalaman shugaban na zuwa ne bayan hukuncin wata kotu a Abuja, ranar Juma'a, da ya bayar da umarnin haramta Kungiyar IMN ta mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky kamar yadda gwamnati ta nema.

Bayanan kotun sun nuna cewa gwamnati ta nemi a haramta kungiyar ta IMN bayan ayyana ta a matsayin ta 'yan ta'adda, inda ta zarge ta da haifar da asarar rayuka da dukiyoyi. Mai magana da yawun kungiyar Ibrahim Musa ya yi watsi da zargin cewa suna tayar da husuma, sannan ya shaida wa BBC lauyoyi da jagororinsu na nazari kan umarnin kotun domin fitar da matsaya. Tashin hankali ya kazanta a baya-bayan nan tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan kungiyar, wadanda ke zanga-zanga akai-akai tun bayan tsare shugabansu da gwamnati ta yi a shekarar 2015.

Sai dai mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa za a aiwatar da wannan hukunci na kotu domin haramta kungiyar ta IMN, amma ya ce hakan ba yana nufin haramta Shi'a ba. "Akwai miliyoyin 'yan Shi'a a kasar nan wadanda suke zaune lafiya kuma gwamnati ba ta da matsala da su, ba wanda zai tsangwama musu kaa yadda suke harkokinsu... Ba mu hana kowa yin Shi'arsa ba," in ji malam Garba. Ya kara da cewa gwamnati ta nemi wannan hukunci ne domin "haramta ayyukan kungiyar IMN karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky".

Bayanan kotu.

Takardar ta ce kotun da mai shari'a Nkeonye Maha ta jagoranci zamanta ta yanke cewa "Daga yanzu babu wani dalilin da zai sa a amince wa wasu mutane ko gungun mutane da kiran kansu da suna 'Yan Shi'a." Takardar ta kara da cewa kotun ta bayar da umarnin ne bayan da ta samu 'takardar bukatar' haramta kungiyar daga gwamnatin tarayya. "Domin tabbatar da an haramata kungiyar, kotun ta umarci ministan Shari'a da ya bayyana hukuncin haramta kungiyar a kundin gwamnati da kuma manyan jaridun Najeriya guda biyu," in ji takardar.
Ci gaba da zanga-zangar da 'ya'yan kungiyar ke yi na neman a saki jagoransu da ke tsare a hannun gwamnati tun 2015, a Abuja da sauran
sassan kasar na ci gaba da janyo asarar rayuka.
Ko a makon da ya gabata sai da 'yan sanda suka 'kashe' 'yan kungiyar 11 a Abuja a irin wannan zanga-zanga, inda su kuma 'yan sanda suka yi zargin 'yan kungiyar sun kashe babban jami'n 'yan sanda. Ana sa ran cewa fadar gwamnati ko kuma ma'aikatar Shari'a ce za ta
sanar da wannan hukuncin na 'haramta' ayyukan kungiyar ta IMN. Idan har haramcin ya faru, to IMN za ta zama kungiya ta biyu bayan
IPOB da Shugaba Muhammadu Buhari ya haramta a mulkinsa.
A shekarar 2017 ne gwamnatin Buhari ya haramta ayyukan kungiyar masu fafutukar neman ballewar yankin kudu maso gabas na Najeriya daga kasar wato IPOB. To sai dai kungiyar IMN na da hurumin daukaka kara kasancewar ba su da wakilici lokacin da aka fitar da wannan hukunci.

Dalilin kin sakin Zakzaky

Wannan takarda dai na zuwa ne a ranar da tsohon ministan Shari'ar kasar, Abubakar Malami ya bayyana gaban majalisar dokokin kasar domin a sake tantance a matsayin minista a gwamnatin Buhari. An tambayi tsohon ministan na shari'a dalilin da ya sa ya ki amincewa a saki tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Sambo Dasuki da kuma jagoran 'yan Shi'a a Najeriya Malam Ibrahim Zakzaky duk da kotu ta bayar da belinsu, sai ya ce hakkin ofishinsa ne ya kare hakkin 'yan Najeriya ba na wani mutum daya ba.
Ya ce Kundin mulki na Najeriya sashi na 174, ya bayyana cewa hakkin ofishin ministan shari'a ne shi bada kariya da kuma shawara kan
hakkin al'umma. "Dole minista ya kula da hakkin 'yan kasa ba hakkin mutum daya tilo
ba," in ji shi. Ana dai zargin gwamnatin Najeriya da kin mutunta hukuncin wasu kotuna da suka bayar da belin Sambo Dasuki da kuma Malam Zakzaky. Amma Malami ya ce idan mutum daya ko biyu ko uku suka yi kokarin tayar da hankalin 'yan kasa wajibi ne a yi maganinsu ta hanyar daukar mataki na shari'a. Har wa yau, ita wannan takarda na zuwa ne kwana uku kafin sake bayyanar shugaban kungiyar ta IMN, Sheikh Ibrahim Elzakzaky a kotu da ke zama a jihar Kaduna.

El-zakzaky da mai dakinsa dai na neman samun beli domin fita kasar waje neman lafiya kasancewar suna cikin 'matsanancin' hali na rashin lafiya. Kotun ce ta dage sauraren bukatar neman belin a zamanta na ranar 18 ga watan Yuli har zuwa 29. Tana iya yiwuwa gwamnati ta nemi a haramta kungiyar ne domin yin amfani da hakan a gaban kotu. Watakila kuma an samu hukuncin haramta ayyukan kungiyar domin yin
kandagarki na abin da zai je ya zo a ranar Litinin din, ranar da ake sa ran kotun ta Kaduna za ta yanke wannan hukunci.

Menene ra'ayin ku akan wannan Rohoton ???
Martani !!

Daga --Idishia Jos.

Da sunan Allah mai rusa azzalumi mai tallafawa wanda aka zalunta, muna masu kira da fadawa duniya cewa lallai wannan magana da Buhari yayi yayi tane kawai don wata manufansa, saboda tun kafin wannan lokacin mun san suna son Haramta Harkan musulunci a kasar, sabida tun kafin gwamnatin Buhari sun sha fadan cewa zasu mai da Harka a matsayin kungikiya na ta'addanci. Sheikh Zakzaky tun a shekarun baya yayi bayani akan wannan wannan kuduri nasu na haramta Harka Islamiyya Allah bai basu nasara ba sai yanzu da suke tsare dashi shine suke cewa sun Haramta ita Harka din.

Sanin kowa ne 'Yan Shi'a ba 'yan Ta'adda bane saboda mu mutane ne da muke rayuwa a cikin al'umma, kuma kowa ya shaida cewa ba'a taba ganin mu da Makami ba bil hasani ma a duk lokacin da muka fita muzahara ne ma ake afkama har a kashe wasu daga cikin mu. Duk da yake wannan kudiri na Buhari tun ba yau ba kusan shekara kenan King Salman na saudiya ya shaidawa duniya cewa su suka sa Buhari ya kawar da Sheikh Zakzaky da Harkan musulunci saboda wata mamufarsu. Har yana ikirarin cewa Sheikh Zakzaky yana son kada kasar musulunci ne irin na kasar Iran a Afirika.

A lokacin da aka afkawa almajiran Sheikh Zakzaky a Zariya cewa suka yi wai 'Yan Shi'a sun tarewa Hafsan Sojin Nigeriya  Tukur Buratai hanya ne, yasa aka mana wannan mummunan kisa na kiyashi. Sai gashi ta bayyana su da Kansu suka fito duniya suka nunawa al'umma wannan abinda aka wa Sheikh Zakzaky kwangilane Saudi Arebiya ta bawa Buhari akan ya share Malam daga duniya ya share Harkan musulunci a NIGERIYA baki daya. Cewa da suke sun haramta Harka Islamiyya duk a cikin kwangilanda Buhari ya karba ne daga hannun Saudiya domin ya gama cimma hadafinsa.

Idan muka wai ga baya, zamu ga cewa ai kotu Abuja ta bada Umarnin a sake Sheikh Zakzaky amma Buhari yaki bin umarnin kotu, shima Malami Abubakar din sunyi Burus da wannan umarni na kotu domin suna son su cika alkawarin da suka wa Saudiya na Karban Kwangilanda suk ayi a hannun su.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates,
Tare dani --Idishia Jos.

#FreeZakzaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post