RABON DUKIYA NA ALLAH NE

RABON DUKIYA NA ALLAH NE

Nigeria Ina Mafita Na Sheikh Zakzaky
Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Muh'd Suleiman


Allah Ta'ala baya ya halicci mutane da dabbobi ya zuba arzikin daji da na ruwa yace:- to gashi nan kuje ku raba yadda yayi muku ba ne, A'a halitta da tafi da Al'amarinta nasa ne, har wala yau Yace ga yadda za'ayi rabon, saboda haka sai Allah Ta'ala ya ɗauki wa kansa rabon dukiyar, bai ba sarakai ko alƙalai ba ballantana suyi zalunci,
Muna iya ganin misali a wajen rabon dukiya (gado) wadda in mutum ya rasu,
Akace Iyayensa suna da kaza idan mutumin ba shi da Ƴaƴa in kuma yana da Ƴaƴa, suna da kaza, Maza na da kaza, mata na da kaza, da dai sauran su, Allah Ta'ala ya raba gado, in mutum ya rasu dukiyarsa ba haƙƙin Sarki bane, ba kuma na Alƙali bane, in ma aka aka raba, mutum bazai ce an cuce shi ba, domin rabo ne daga Allah Ta'ala, in ko har kaga Anyi rabo, wani yaga an cuce shi, to imma dai Anyi masa adalci, yana ganin bai yi adalci ba, Wa imma dai Alƙali ne yayi masa zalunci, amma in dai rabo ne na Allah Ta'ala, to babu wanda yafi Allah adalci.

To haka kuma Allah Ta'ala ya sanya zakka, bayan sanya zakka ta zama wajibi, ya kuma sanya wani wajibci, adalci na ihsani wanda ya bari a hannun mutum yayi daidai gwargwado. In yayi da yawa ya sami lada mai yawa, in kuma yayi kaɗan ya sami ladansa kaɗan, in kuma yaƙi yi, ya sami azaba, sannan bayan wannan, ya kuma sanya Zakkar nafila domin ya zama rabo da Adalci.

To Allah ya ɗamfara arzikin nan nasa da biyayya gareshi, zamu ga cewa kamar yadda Allah Ta'ala yake cewa "Ban Halicci Mutane da Aljanu ba, face don su bauta mani, bana neman arziki daga garesu kuma bana neman su ciyar dani" dama ya za'ace anba Allah abinci Yaci, wannan Mustahili ne, domin Allah shine Mahaliccin mutum kuma shine Mahaliccin abinci. Shi ba mabuƙaci ne ga abinci ba, saboda haka ma Malamai sun fahimci cewa inda Allah Ta'ala yake cewa, "bana son ku Azurta ni, kuma bana son ku bani abinci" ba  yana nufin zaku tattaro dukiya ne kuce gashi mun ba Allah ba, wanda ya halicci abu, kaje kana bashi? Mene zaka bashi? Kayi noma ne kaci Alhali kuwa Allah Shine yayi ruwa da tsiro, da yawan Malamai sun tafi da Fassarar cewa abinda Allah yake nufi shine, ya ɗaukarwa kansa raba arziki da abinci, Allah bai ce suyi wannan ba.

Kuma yazo cewa in aka bi dokarsa, Allah Ta'ala yana yalwata arziki, kamar yadda Allah Ta'ala yake cewa acikin littafinsa ga bani Isra'ila "Da ace Yahudu da Nasara sun tsaida Attaura da Injila, da sun  ci Arziki daga samansu da ƙarƙashin ƙafafuwansu, Misali Allah ya saukar da ruwa daga sama, kuma ya fitar da tsiro daga ƙasa.

Yanzu mutane sun ɗauka cewa su rabon arziki kayansu ne, ai sun san arziki na Allah ne, in aka nemi ruwa aka rasa, ai sun san inda sukan nemi ruwa, ba wani wanda zai je ƙaramar hukuma (local government) ya nemi ayi ruwa, tunda ba'ayi ruwa ba (Yace) to ciyaman kasan yadda zakayi kayi ruwan sama, ko kuma gwamnatin jiha (state) Kuyi ruwan sama, ba wanda zai iya wannan, ko kuma ace kogi babu kifaye, to lallai ƙaramar hukuma ta san abin yi, ko kuma itatuwa ba su yi Ƴaƴa ba, saboda haka gwamnati tayi wani abu, ko ta kafa doka, duk mangwarorin ƙasar nan su riƙa yi da kyau. Kuma in kaji basu yin ƙwai babu wanda zai je wajen hukuma yace, to kaji su riƙa yin ƙwai, wannan Allah ke yinsa, kuma ɗamfare yake har wala yau da dokar sa.

Ishaq Muh'd Suleiman 08132933333

Ma'asumah Nigeria News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post