MUTANE SUN HARZUƘA

MUTANE SUN HARZUƘA

Nigeria Ina Mafita Na Sheikh Zakzaky
Ma'asumah Nigeria News Update

to bani da lokaci kamar yadda naso in ɗan yi mana ishara kan dalilan waɗannan da maganinsu, don ahalin yanzu mutane sun shiga wani matsanancin hali na ruɗu da cewa sun riga sun harzuƙa, kowane irin abu na iya faruwa,
Muna iya ganin abinda muka ji ya faru a wasu sassa na kudancin ƙasar nan, wanda ɗazun ma wani ke gaya min yana aukuwa a Maiduguri.
Jiya cikin tsakar dare ɗaliban Jami'a sunyi buge-bugen garwa, musamman waɗanda suka zo daga kudu cewa "Babangida ya tafi! Sai kuma yau da safe ma aka ce an rufe Jami'a ɗin.
To tana iya yiwuwa irn wannan harzuƙa ɗin ya zama yau ko gobe. Kawai ka gansu akan titi su ƙarawa Mazalumi zalunci don menene?
Don yadda ake yi ɗin, masu motocin haya su ake kama su a lallasa, su kuma ake ƙona musu mota, aje kanti afasa a kwashe musu kaya, shi kansa mai mota, an zalunce shi,
Yaje ya kwana uku alayin mai, sannan kuma shima yana da iyalin da zai ciyar, kazo ka lallasa shi ka ƙona motar, ko kuma mai kantin da shima yake ɗan jujjuyawa ya ɗan samu yaci, to kenan ka ƙona masa jari, alhali bashi ne ya zalunce ka ba, da kai da shi duk zaluntar ku akayi, in da gaske ne a nemi azzaluman mana.
Ko dama ace mun harzuƙa, to kuma yana nufin mu ma sai mu zama azzalumai?
Ya zama daga zaluntarmu, sai muje mu zalunci Ƴa Uwan mu, waɗanda su ma zaluntar su ake yi? (Haka bai dace ba)

Ya kamata mu sani cewa wannan ba shi ne zai kai mu ga gyara ba, kuma koda za'ace misali mutane duk suce wai Babangida ya sauka, in ya sauka wani wanda ya fishi zalunci ne zai hau.
Tunda haka al'amarin ya kasance, lokacin shagari, mutane suna ta cewa ya sauka, yana sauka Buhari yazo, kuka ce kayya-kayya ai gara shagari, to bayan an kau da Buhari, to yanzu kuma ana cewa gara Buhari, to idan ma yanzu Babangida ya kau, sai ance Ina Babangida?
Kamar mota ce ta rigaya ta lalace, sai kace ai direban ne bai iya ba, ka cire wannan ka sanya wancan,
To in baka gyara motar bane babu yadda za'ayi ta koma dai-dai, saboda ainihin lamarin ba direban bane, motar ce don mu gane, dole se tsari na adalci ne zai iya tsayar mana mana da Shugabanni masu adalci,
Saboda haka ya zama ƙoƙarin mu shine mu tabbatar da tsari mai adalci, dole kuma tsari mai adalci sai shugabanni masu adalci, (babu kuma wani adalci idan ba'a cikin Musulunci ba)


Ma'asumah Nigeria News Update

Wakilin mu Na Sokoto 08132933333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post