No title

MUTANE SUKA JA MA KANSU ƘUNCIN ARZIKI

Nigeria Ina Mafita Na Sheikh Zakzaky
Ma'asumah Nigeria News update
Ishaq Muh'd Suleiman


Abinda nake ƙoƙarin in nuna anan shine halin da muka riga muka shiga ayyuka ne na hannuwan mu, kuma anan babban laifin da ya janyo wannan bai wuce kangare wa Allah Ta'ala da aka yi ba. Domin ta yiwu mutum yace, to yaya mu zamu sha wahala saboda  fanɗara daga tafarkin Allah, su ƙasashen kafirai suna jindaɗi sai muce ai su (kafirai) basu yi ma Allah ƙarya ba, su basu ce suna son Al-Jannah ba, ballantana ma su sa rai da ita, basu kuma yiwa Allah ƙaryan Musulunci ba, kafirai suke, sun kafirce wa Allah kuma duniyar tayi musu, Al-Jannahrsu suke ci, tsakanin su da wuta mutuwa, saboda haka ko an sakar musu (duniyar) wannan yayi daidai,
kamar yadda akace duk lokacin da Allah Ta'ala ya aiko Manzo yakan takura mutane, har idan sun wa'aztu shikenan, idan kuma basu wa'aztu ba akan yi musu Istidraji har kamun ƙarshe,

To muna iya cewa su ƙasashen kafirai Anyi musu Istidraji, an saka musu, su duniyar suka sani, basu da sauran su koma wa Allah, tunda dai basu yi masa ƙarya ba.

To amma ina ga mutumin da ya buɗe bakinsa yace shi yayi Imani da Allah, ya kuma ce yayi Imani da Manzon Allah, ya kuma ce yayi Imani da abinda Allah ya saukar wa Manzonsa, amma ayyukansa da zantukansa ya kangare wa Allah da kuma littafinsa, Alokaci guda kuma yana neman taimako daga wajen waɗanda suka yiwa Allah tawaye?
Anan wanene babba? Da wanda yayi Imani da Allah da Manzonsa da littafinsa, amma ya kangare, yake neman taimako wajen Iblis, dashi da Iblis wanne yafi cigaba? Kaga dama Iblis ɗan tawaye ne, to ko dole wanda ya fanɗare ya kuma je wajen fanɗararru yana neman gudummawa matsayinsu yafi wulaƙantuwa,
Dole ne Musulmin da yasa kansa cikin wannan hali, kafiri ya fishi, don shi kafiri bai yiwa Allah ƙarya ba, don haka ba mamaki irin ƙasashen da ake cewa nun cigaba, suke take ƙasashe suna murjewa kuma suna tatse arziki suyi waje dashi, ana biye dasu tare da kyakkyawan Ikhlasi da bauta don su zo ciyar da ƙasa gaba.

Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Muh'd Suleiman 08132933333
09/07/2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post