Mungano Wani photon yadda aka Kama Wakilin mu Mahadi Tukur Almizan.

Dubi yadda aka Kama Wakilinmu batare da wani Abu dake nuna shi Mai laifine ba.

Ma'asumah Nigeria News Updates


Yau kusan sati guda Kenan Tun ranar Talata 23-7-2019 Wakilanmu na shafin Ma'asumah Nigeria News Updates  guda biyu ke hannun jami'an  tsaron Nigeria (D s s)  tun bayan Bude wutar da sukayiwa Mabiya Allamah Sherik Ibraheem Zakzaky (h) a lokacin da suka Fiti Muzaharar Lumana Domin a gaggauta sako masu Jagoran su ya nemi lafiyar sa Wanda suke tsare dashi tun 2015 batare da ya aikata wani laifi ba.

A ranar talatar ne a yayin da Jami'an tsaron Nigeria suka watsa ciyagas tare da harbi kan Mai uwa da wabi da masu fafutikar ansaki shehin malamin ne Sukayi awon gaba da Wakilan mu biyu a yayin da suke dauko Mana Rahoton abubuwan dake faruwa,  A inda tun bayan Abun muke bibiyar lamarin Bamusan ko wane  hali suke cikiba  Zuwa yanzu Ba abari muka gana dasuba.


A Yau ne mukayi kicibus da photon Daya daga cikin Wakilan namu mahadi Tukur Almizan a yayin da Jami'an tsaron suka Kama shi.

Da haka muke Kira da gwamnatin Nigeria tare da Jami'an tsaron Nigeria su  gagauta sako Mana wakilanmu tare da sauran Yan uwan da aka Kama batare da sun aikata laifin komai ba.

Sannan su gaggauta Sakin Jagoranmu Sherik Ibraheem Zakzaky (h) Domin neman lafiyar shi.
#Free_zakzaky (h)
#Free_Mahadi_Tukur_Almizan
#Free_Jibril_Usman_Sarki
#Free_Our_Brothes and Sisters

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post