MINENE DALILIN DA ZAISA NIGERIA TA ZAUNA LAFIYA? BAYAN AN'KI LAFIYAR

MINENE DALILIN DA ZAISA NIGERIA TA ZAUNA LAFIYA? BAYAN AN'KI LAFIYAR.
MA'ASUMAH NG NEWS UPDATE
  Daga  Wakili @Shana islam.

Wannan bawan Allah shi ne Malam Ibraheem Zakzaky Mutumin da tun tashin sa bai san ko mai ba sai bautar Allah A kullun gurin sa yaga an'kiyaye dokokin Allah kullun hankuron sa yaga an daga martabar Iyalan gidan Annabi Muhammad Ahalul bait (as) Bawan Allah Malam Zakzaky baka taba ganin bacin ransa sai idan Allah aka taba da Annabi (s) da iyalan gidan sa (as).



Malam Zakzaky a'dilin bawa ne hatta makiyan sa nayi masa shedar hakan saboda sun fuskanci a'dalcin sa a zaman takewar rayuwa ta yau da kullum Malamin da baya son ganin ana zalunci baya son mai zalunci baya zama da azzalumi bawan Allah Malam Zakzaky mai son hadin kan Al'umma ne,



saboda hakan a'duk fadin kasar Nigeria shi ne kawai aka samu mai kiran taro domin hadin kan al'umma yakira taron da suna makon hadin kan Musulmi a wannan taro ya kira Dan izala darika khadiriya tujjaniya kur'aniya kai hatta kiristan shehin malamin ya kira dan fahimtar juna da kyautata mu'amilat Baya nuna ban banci gurin sa a'tashi tare a tsira tare.




malam Zakzaky shekaru sama da 40 yana kira al'umma ba dan ko mai ba sai dan Zuwa ga samun Uzurin Ubangiji gurin sa al'umma su samu tsira yau duniya da gobe kiyama Amma duk da hakan  makiya Allah suke ganin ai'abunda malam Zakzaky keyi ba dai dai bane bai kamata a zura masa ido hakan nan kawai ba hakan yasa mahukuntar kasar nan suka dauki tsana da gaba suka dura kan malam Zakzaky duk wani azzalumi da zai hau karagar mulki a Nigeria sai ya nemi kawar da MAlam Zakzaky a duron kasar nan mlm Yasha dauri gidajen yari da ban daban a kasar nan saboda su shuwagabannin Ba Allah ne gaban su ba basu damu da Addini ba.





Har yanzu da nike wannan rubutun Malam Zakzaky (h) ya  fuskantar barazanar barazanar kisa daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari (l) al'umma idan baku manta ba kowa yasan a binda ya faru a shekarar 2015 12/12 a Zaria Da rana tsaka Buhari (l) ya tura tundunar soja a zaria domin su kawar da Malam Zakzaky (h) su shafe kiran da yake daga doron kasa sukayi karyar an'tarema Shugaban sojoji Haiya har suka fitar da wani vedion karya domin su dauke hankalin "yan Nigeria kuma sukayi nasara a kan wasu wawayen al'umma.




Sunyi amfani da wannan damar wajen aiwatar da kisan gilla ga Malam Zakzaky (h) da almajiran sa inda hakan na faruwa suka bude wuta a Husainiyyah Baqiyatullah Zaria suka kashe duk wanda ke cikin Husainiyya sai wanda Allah ya tsiratar Hakan bai ishe suba sukayi gidan Malam Zakzaky dayake daman gurin su kenan kashe malam din isar su anguwar keda wuya suka bude wuta kan kowa da kowa haka suka kwana suna kisan al'umma dan kawai su samu damar isa ga Su malam almajiran malam sun nuna su 'ya yan malam ne inda suka hana a isa ga su malam sai dai idan ba ran su haka kuma a kayi basu samu sun isa ga su malam ba sai bayan da sun kashe kowa da kowa maza da mata yara da manya sun kashe sama da mutum dubu daya  sannan suka isa ga malam Zakzaky Innnalillahi wa inna alaihin raji un😭.





Isar su keda wuya suka budewa su malam Wuta suka hahalbi malam Da malama halbin kisa sukayi a kan su malam kuma sun kashe shi Allah ne ya mai da ran sa Bayan sun tabbatar da sun kashe shi suka dauke sa sukayi bariki da shi sunata risgilanci da mummanan zagi a kan su Malam Zakzaky tsawan kwanan ki su malam suna kwance ba rayuwa sai bayan kwanan ki Allah ya maida rayuwar su mlm A'bunda ya tada hankalin a'duwan Allah tun tashin su malam Zakzaky (h) ake tsare da shi da malam duk da wannan mummunan halsashen dake jikin Malam amma haka ake tsare da shi ba kulawar bashi magani kuma an hana a fitar da shi waje ya neme magana kullun lafiyar sa sai kara yin kasa take.




Amma duk da wannan a'bunda ya faru ga bawan Allah waliyin Allah al'ummar kasar nan wasu na jin dadin a bunda a'kayiwa su malam wasu na fadin ya yi dai dai kuma Allah ya zura masu ido suki shiga bala'i da masifa ina waliyin Allah ne fa ake zalunta a kasar Wallahi bala'i yanzu al'ummar Nigeria ta fara gani matukar ma a saki malam Zakkzaky da neman a fuwan sa ba.




Zan takaita a nan sai kuma wani karon.

#Ma'asumah ng News tare da wakilin shafi @Shana islam kaduna zone.

Criminal Buhari Free Zakzaky dole.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post