(MARUBUTAN MU; Mu Juya Alƙalumanmu Zuwa Kaifi Ɗaya)

MARUBUTAN MU; Mu Juya Alƙalumanmu Zuwa Kaifi Ɗaya.
Daga Ma'asuma Nigeria News Update.



Kamar yadda Sayyid Hafizahullah Ya sha kamanta wannan Harka, da 'Jinka' ma'ana kowa akwai inda zai tallafa wajan bada tasa gudummawar har zuwa ga cimma hadafi. Malam Hafizahullah yasha faɗi cewa, ko wane Ɗan uwa ko Ƴar uwa yaga irin gudummawar da zai bada tasa ta ƙashin kansa a wannan harka domin samun uzuri a wajan Allah, ta hanyar baiwar da Allah Yayi masa.





Kowa da irin baiwar da Allah Yayi masa, wacce zai iya amfanar wannan harka da ita. Ga wasunmu da Allah Ya yiwa baiwar hikima da iya zance a wannan harka, musamman ta fuskacin rubutu domin ilimantarwa, tunatarwa da wa'azantarwa ga al'umma, ya kamata ace yanzu ko wannen mu ya juya da tsinin alƙalaminsa ne zuwa ɓangare guda, ina nufin mufi muhimmantar da rubutunmu zuwa al'amarin Jagoranmu, musamman a wannan yanayi da muke ciki na ƙara taɓarɓarewar lafiyarsa da mai ɗakinsa, da kuma ƙoƙarin kisansa da wannan azzalumar gwamnati ke yi.




Haƙiƙa rubututtukan da ake, suna matuƙar tasiri ga al’umma, domin suna ƙara fahimtar mu da kuma manufar Jagoranmu. Haka kuma su azzalaman da suka zalumcemu suna ji kuma suna ganin dukkanin motsinmu, wannan kuma yana matuƙar sosa zukatansu.





Idan da za'ace suga cewa munyi rubdugu akan al'amari daya, dukkanin wani motsinmu ya kasance yana da alaƙane da al'amarin Jagoranmu, to haƙiƙa zasu ƙara tsorata, kuma su san cewa bamu ɗauki abin da wasa ba, wannan dalilin zai taimaka matuƙa wajan biyan buƙatarmu na kuɓutarsa daga dukkanin mugun shirin su.




Ga sauran Ƴan uwa, ya kamata ace kuma kuna bada taku gudummawar wajan isar da saƙonnin zuwa inda ya dace, ba lallai sai ka zama marubuci ba, abu mai muhimmanci shine idan wani yayi rubutun to ya ɗauke maka wannan nauyin, kai kuma sai ka taimaka wajan isar dashi inda zai tasirantar ta kowace hanyar da kake da iko, domin zai iya kasancewa shi marubucin bashi da ikon isar da saƙon zuwa muhallinsa. Idan kai kuwa kayi hakan, kaga an tabbatar da kamalar aikin kenan.




Daga Wakilinmu; Abbakar Ibraheem Kudan.
08/07/2019.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post