Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates,
Tare da --Idishia Jos.
Da farko yace ya haramta Shi'a baki daya, sai kuma ya dawo yace Bai hana 'Yan Shi'a yin Shi'ar su ba, a kotu kuma ance an haramta Shi'a har da bugawa a Jaridu. Ta bangaren Jami'an tsaron 'Yan Sanda su kuma suka ce duk 'Dan Shi'an da suka gani zasu harbe shi, yanzu kuma suka kara cewa zasu fara kama duk wani 'Dan Shi'a. To menene laifin Shi'a nan ? Laifin su shine don sun ce Allah za su bi, dokokin Allah za'a bi, Hukuncin Allah da Manzon sa za'ayi.
Littafin Allah ya zama mai hukunci, Manzon Allah (S) shine abin riko da iyalan gidansa. Jagoranmu Sayyid Zakzaky (H) yace babu hukuma sai ta Allah, tsarin 'Constitution' tsarin kafirci ne, bama Sheikh Zakzaky kadai ya fada ba, akwai 'Dan Majalisan da ya fada cewa; Wannan 'Constitution' din ba shi bane mafita kuma ba zai taba kawo mana canji ba a kasar. Da'awar Sheikh Zakzaky kuma yana kira ne adawo da koyarwa na Musulunci irin na Annabi Muhammad Rasulallah (S) wanda ya zo dashi ya bar mana. To idan wannan laifi ne har za'a ce an haramta Shi'a domin suna bin koyarwan hakikanin addini musulunci ashe fada ake da addini musulunci ba da Shi'a ba.
Bayan faruwan ta'addanci kisan kiyashi da sojojin Nigeriaya suka yi a Zariya, shekaru Uku da wannan aika-aikan sai gashi abu ya fito balo-balo Buhari kwangila ya karba daga Saudi Arebiya. King Salman da bakinsa ya fito ya shaidawa duniya su suka sa a kashe Sheikh Zakzaky da mabiyansa saboda Sheikh Zakzaky yana yin Shi'a. Abu ne karara da duniya tayi shaida akan haka, su kuma musulmai har yanzu basu farka ba a baccin sa suke. Hakikatan Buhari so yake ya rusa musulunci ne kuma ya hau wannan mulkin ne abisa yarjejeniyarsu na share musulunci a nigeriya kuma yana amfani ne da wanda suka amsa sunan musulunci yake yakar musulunci.
Sheikh Zakzaky yasha fada ko tashe-tashen hankula da yakici yaki cinyewa a Arewacin Nigeriya nan, shima kwangila ne na na share musulmai a wajen. Sheikh Zakzaky ya fada Turawane suke kwasan arzikin Arewa amma kafin su zo sai su sa a kashe duk mutane wasu suyi gudun hijira a bar wajen ba kowa, su kuma daga baya su zo su kwashi arziki. To idan haka ne me zai hana su bar mutane da rayukansu su zo ayi cinkanya a tsakani amma mu su bar mu kuma su bar mu muyi addinin mu! Mu sani duk abinda ake yi a yankin Arewa fada ne ake yi da addini kuma zai shafi kowa in har bamu tsahi mun yaki zalunci ba.
Akan haka Sheikh Zakzaky da Almajiransa suka tashi tsaye don kare addini musulunci da kare martaba da daraja na addini. Abin lura su wanda ake kashewa a Zamfara Birnin Gwari da sauran garuruwa kunga su bama addinin suka ce suna yi ba, haka siddan ake diran musu. To ina kuma ace addinin zakayi kunga ba za su taba barin mu ba. Muna kara shaidawa al'umma cewa Buhari ba mai kishin addini bane bilhasani na Buhari bai damu da musulunci ba. Mu dawo mubi koyarwa na addinin Musulunci domin tsiran mu a duniyan mu da lahiran mu baki daya.
--Idishia Jos.
#FreeZakzaky.
Tags:
Yanar gizo