KUN YI KADAN KU KAWAR DA MALAM ZAKZAKY HARKAN NAN SAI TA KAFU DARAM A KASAR NAN.



     - Inji Sheikh Yakubu Yahya Katsina.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates, Tare da --Idishia Jos.

Abinda muka fahimta mutanen nan tarko suka mana, kamar suna mana wani tarko ne. Suna kara kwanuka suna kara jan lokaci saboda su biya bukatansu da basu biya a gyallesu nan take ba, suna so ya zamo kenan su haifar da sabuwar 'Boko Haram' to ba dai cikin wannan "Harka ba" insha Allah. Sun Tara 'yan iska a wurare a cikin dajijjika da sunan 'Kidnappers' da sunan masu fashi da makami masu kwatan shanu da sauransu duk saboda wannan Harka ne, abinda suke so Malam ya cika su sako wadan nan mutane su ta kashe-kashe da sunan 'yan Shi'a suna daukan fansa.

Yanzu abinda suke kokari kenan, yanzu hankoronsu shine ya za'a yi su haifar da wannan munakisa. In ba haka ba me yasa Amerika zasu sanar talakawa kada suje Abuja kada suje Legos su guji shiga dandazon mutane kaga sun shirya wani abu kenan, in ba haka ba ina ruwan Amerika da Nigeriya ! Nigeriya jihar Amerika ne ? Me zai sa su sa mana baki cikin lamuranmu? Sabida haka Muzahara kuma da wannan kalma tafi "Bindiga" tafi 'Kifiya'  "Free Free Zakzaky" don abinda basa so suji kenan, to wannan kalma zamu dinga fadanta muzaharori kuma ku kuka ja ayi duk abinda kuka gani kukuka jashi ku kuka haifar dashi.
Sheikh Yakubu Yahya Yana jawabi a wajen rufe Muzaharar ranar Alhamis


Shekaru kusan 30 muna fada akwai lokacin da za'a na fita Muzahara da daddare, za a na Muzahara da rana za a na Muzahara da safe, gashi Allah ya kawo mu lokacin. Wasu na makabarta dazu Kaduna anyi jana'izar dan uwa Karfe Biyu lokacin wasu na kan TiTi kuma muma gashi Yanzu muna kan Titi. Almuhimmu shine 'Yan uwa su iya mallakan kawukansu su kuma yi daidai wanda yake nizamin wanda zasuyi Allah ya basu lada. Wannan abinda muke addini ne Muzahara nan Annabi ne ya fara ta, tare da Annabi (S) aka fara in mutum bai yi karatu ba yaje yayi karatu.

Wani yana fada Tsohon Gwamnane Sanatane kuma yanzu yake fada " Al'amarin Al-Zakzaky ba al'amarin Addini bane Al'amarin Siyasa ne saboda haka dole a dauki mataki saboda kare tsaron kasa." Ni ko nace to kakansu ya riga su fada me Fir'auna yace ? "Haruna da musa sihiri ne ba abinda suke so illa su Kore ku daga kasan su kawar da kyakkyawan tsarin kasan wacce kuke tafiya akan sa" wannan maganar fir'auna ce ka maimaita kai dan karamin Fir'auna. Me suke cewa Annabawa "Wannan mutum ne kawai yana so ya hau kanku ne ya zamo shine sama shi ne mai sawa shine mai hanawa" sabida haka in kun ce siyasa ne Addinin da sunan siyasa kuke fada to Fir'auna ya fada Arnan baya sun fada kuma gashi Yanzu kuna fada.

Mun yi bara'a daga kafirai munyi bara'a daga munafukai, insha Allah ba zamu shiga wuta tare da munafukan Nigeriya ba. Ba zamu shiga wuta tare da kafuran mahukantan Nigeriya ba. Insha Allah (T) wannan Harka sai ta yi nasara, kuma kunyi kadan ku shafe sunan Malam Zakzaky Allah ne ya daga shi, sunan Malam Zakzaky ba zai shafu ba daga nan har duniya ta tashi. Yana nan cikin Computer, yana nan cikin Littafi, yana nan cikin Littafin Mala'iku yana nan cikin kowanne Littafi, sunansa na nan rubuce aikinsa na nan Rubuce. Sannan kuma sai wannan abin ya dire bi'izinillahi ta'ala.

Babu shakka muna da tabbaci da kuma masaniya rike Malam da kuma hana shi  fita neman lafiya wani rami ne da aka haka mana don mu fada. In banda haka ba yadda za'a yi mutanen da ke da hankali suka san abinda ke zuwa kuma suke kishin kasa, kuma suka san amana, sukasan mulki, su kasan zafin rai suka san zafin mutane, suka san zafin amanar su na zaman lafiyan kasa ba yadda za'a yi suyi abinda mutane nan sukayi. A kotun nan da ake je yau tun daga "Registered" har Lauyoyi da duk 'yan kallo harda 'yan sanda yana kuka sabida halinda Malam yake ciki, suna zubar da hawaye. Lauyan Kaduna ne kawai bai zubar da hawaye ba, shi kadai ne bai zubar da hawaye ba. Amma har yanzu sai basu san malam bai da lafiya ba wai sai sun bincika sun tabbatar tukunna.

To shikke nan bismilla in ance muku Allah bakwa ganewa. In ance muku Annabi bakwa ganewa amma kun san abinda ya samu Sadam kun san abinda ya samu Gaddafi, kun san abinda ya samu Mubarak, kun san abinda ya samu ire-iren wadan nan "Dictators", masu kama karya to ku jira naku yana zuwa. Shi El-Rufa'i yana cewa madaman yana Gwamna ba inda za'a fitar da Malam zuwa Asibiti. Wa ya fada maka cewa kai ne gwamna har nan da tsawon shekara hudu ! Wa ya tabbatar maka da haka ? To muna fatan Allah ya kwantar da kai kai ma ya nuna maka malam yaje ya dawo da ransa lafiyansa. Kana kwance baka sani ba ka tambaya yaushe mutumin nan yaje Asibiti kana kwance baka san yaje ya dawo ba.

Ku sani ba zamu dauki makami ba da " Allahu Akbar " zamuyi nasara, amma wannan kalma 'Kalmatullahi Hiyal Uliya' wannan babban kalma da ita zaku kai kasa insha Allah. Da La'ilaha illallah Allahu Akbar da ita zaku kai kasa. In kuma kun dasa "Boom" da sunan mu ba zaku samu nasara ba.
Almajiran Sheikh Zakzaky (H) na garin Katsina na Sauraren Jawabin Sheikh Yakubu Yahya a lokacin da yake jawabi akan halin rashin lafiyan Sayyid Zakzaky ranar alhamis da dare.

Kadan daga cikin jawabin Sheikh Yakub Yahya Katsina wanda yayi shekaran Jiya Alhamis a lokacin da aka zo wajen kammala Muzaharar FreeZakzaky da aka yi ranar Alhamis din da dare bayan an kai su Malam Haramtacciyar Kotun Kaduna

   --Idishia Jos.

#FreeZakzaky.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post