Ku Isar da Wannan Saƙon Ga Ƴan Uwa Na Qasa Baki Daya Domin Ba Ina Magana Da Ƴan Uwa Na Sokoto, Kebbi Zamfara Bane

Ku Isar da Wannan Saƙon Ga Ƴan Uwa Na Qasa Baki Daya Domin Ba Ina Magana Da Ƴan Uwa Na Sokoto, Kebbi Zamfara Bane


      MA'ASUMAH NIGERIA NEW UPDATE
Ishaq Muh'd Suleman 08132933333

Ku shigo Abuja Muyita Muzaharoru Har se sun saki Malam, Ƴan Uwa mu muka bari Jahiliyya tana yiwa Malam rainin wayo, satin da ya wuce duka-duka da bayin Allah mutum dudu huɗu muka tayarwa majalisa hankali, hakan tasa su da kansu suka rufe Majalisa suka fasa zaman su, sannan bayan sun dawo suka ce dole a saki Malam ko hankalin su ze kwanta su zamu iya gabatar da ayyukan su,
Akayi Matsaya aka ɗauki matakai amma kaga da yake dama su kafirai basu da amana, (Allah Yace : kar ku basu Amana) amma yanzu bayan an zo kotu, da gani kasan ba gaskiya wai magana daga haka lauyan gwabnati yace (Allah ya tsine masa) kai kaga Yadda ake hira dashi kasan beda gaskiya, wai zasu bincika takardu zasu yi me zasu yi me,

To dama abun ɓangare biyu ne, saboda haka su Jahiliyya ku sani mun riga mun gano ƙarfinku Wallahi Wallahi gwamnatin Nigeria bata I-mana (bata iyawa damu) daga garemu ne yanzu ya rage daga Ƴan Uwa in mun shirya Allah zai taimake mu, kamar yadda Allah Ta'ala Yace: - "Inna Izzati Lillahi Wali Rasulihi Walil Mu'umineen Wala Kinnal Munafiqina Laya Alamun" idan Ƴan Uwa sun shirya Nigeria rauni gareta ba Abuja ne Hasama ɗinta ba can ne matsara to mun gane gano Asirin su Ƴan Uwa su taho mu tafi, Yini guda yayi yawa Wallahi se sun saki Jagoranmu, dama daga Ƴan Uwa Ne, saboda haka Abinda nake tabbatar wa Jahiliyya naga wai sunyi sanarwa cewa sun hana duk wata Muzahara a Abuja, jiya ma An fara yi ana karya wannan dokar banzar tasu sema ranar Monday zasu gane damu suke zancen, saboda duk wanda ke iya tafiya kai hadda ma wanda ɓe iya tafiya amma yana da wata kadara to kuzo mu tare Abuja, kar mubari su ɓata mana lokaci su riƙe mana bawan Allah da guba jikinsa tana ƙara yi masa illa a jiki, saboda haka muna kira ga Ƴan Uwa, su Jahiliyya dama Allah yace rauni garesu, Allah ya kwatanta raunin su da yanar gizo-gizo (mafi raunin gida shine gidan gizo gizo) ba wani ƙarfi garesu ba saboda haka mu daure mu dake kamar yadda Allah Yace (zai ɗauki wasu su zama Shahidai) to kamata Musa Zulla ga Kan mu ba yazan Jagoranmu na hannun Buhari cikin wani hali ba, saboda haka yana da tsananin Muhimmanci mu ƙara azma, su kuma Jahiliyya tun farkon waqi'a cikin kure suke kuma har yanzu ƙarshenta kan  kuskure suke,

Mufa ba muna cewa akai Malam kotu tayi hukunci ta sake shi bane a'a muna cewa ne Sakin Malam Da kutun Kolawale tayi shekaru biyu da suka gabata to a aiwatar da wannan Umarnin Kotun a gaggauta Sakin Jagoranmu yaje Neman Lafiyarsa, a daina yawo da hankalin Ƴan Nijeriya dan naga da Ƴan majalisa da dattawan Nigeria da kuma Arewa Consultative Forum sunata cewa wai a saki Malam to wane saki kuma bayan kotu ta daɗe da Sakin Malam?
Kotun ku wacce kukayi Imani da ita ce ta saki Malam adan haka bamuda bukatar mu sake zuwa wata kotu yanzu, ku aiwatar da Abinda ke hannun ku na umarnin Kotun ku cewa asaki Malam idan ko ba haka Aya zata yabawa kanta zaƙi, wasu suna cewa ba'a barazana be kamata ayi barazana ba, to ba barazana ce muke ba, da gaske muke wallahi,
Mutane muke suna Jahiliyya dukan dukansu Ƴan sandan Nigeria ko satin nan da akayi hira Bulasan ya faɗa mana su duba 300 ne kuma ba dukansu ne a Abuja ba wasu na Sokoto yanzu haka ma wasu na hanyar goronyo dan yau an kashe mutum 26 kar muji tsoro,
Idan muka tafi gaba ɗaya da ƙarfin mu ba wani ƙarfi da zai iya Tsaida mu, saboda haka Ya rage namu Ƴan Uwa kuna ba sako ne ga Ƴan Uwan Sokoto, Kebbi, Zamfara ba ina magana ne da Ƴan Uwa Na duk ƙasa baki daya muji Tsoron Allah mu sauke Haƙƙin Jagora.


Sheikh Sidi Manir Sokoto
Jawabin Rufe Muzahara Jiya

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post