KISA DA ƊAURI; Munyi Sabo Dasu Gabadaya!!!

KISA DA ƊAURI; Munyi Sabo Dasu Gabadaya!!!
 Daga Ma'asuma Nigeria News Update.



A ƙalla kimanin shaikaru arba'in kenan da fara wannan kira na Sayyeed Hafizahullah, kusan dukkanin lokacin da gwamnati tayi niyyar hukumta mu akan abinda take iƙirarin laifi ne muke aikatawa, mataki kala ɗaya take ɗauka, sune; ɗauri, lalata dukiya, illata lafiya mafi iya abinda take iyawa shine kisan kai. Tun daga farkon wannan al'amarin har zuwa yanzu babu wani abu da gwamnati ke iyayi mana daya wuce wannan. Haba Malam!





Ace kimanin shaikaru sama da talatin kana hukumta mutum da horo kala ɗaya, amma bai yi nadama ko nuna gajiya ko alamar tsorata da horon ba, amma dukda haka kaci gaba da yaudarar kanka kana ganin horon nan naka wata rana zaiyi tasiri a kansa? Inda abin na baiwa gwamnati shawara ne, da sai nace, lallai ya kamata su ankara cewa hukumcin kisa ba shine makamin kawar da al'amarin Malam Zakzaky ba, don Ya sha faɗa sauda yawa cewa, kisa baya ƙarawa Harka komi face ƙarfi da ƙwarin gwiwa, kuma wannan shine ke faruwa a aikace,




kunyi iyakan iyawarku ta kowace fuska wajan ganin kun kawar da wannan al'amari, amma haƙarku bata cimma idon ruwa ba, face ma toshe idon ruwan tayi. Zaɓi biyu ne daku, imma ku canja tunani ku nemi wani matakin (Idan kuna da iko) na rushe wannan Harka, amma ba wai da kisa ba, ko kuma ku zubawa al'amarin nan idanu ku hutar da kanku, don Wallahi! wannan ba zai taɓa tasiri a kan mu ba, face ma ƙara mana izza, domin mun riga mun saba da kisanku,



ya zamar mana tamkar ruwan sha. Gareku masu kashe mu; Ku sani lallai mu kam muna da mataki na gaba da zamu iya ɗauka a kanku, matakin da ku san muna ɗauka bai wuce mu kai ƙarar ku wajan Allah, sannan mu fito kan tituna (muzahara) muna shelantawa duniya irin zalumcin da kukayi mana ba, kun sani cewa bamu da wani mataki da muke ɗauka daya wuce wannan. Tunda mun lura kamar kun raina wannan ɗin, to kuyi tunani mai zai faru idan muka ƙara salon ɗaukar mataki a kan ku
Daga Wakilinmu: Abbakar Ibraheem Kudan. 10/07/2019.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post