KA GUJI AIKATA ABINDA ZA KAYI UZURI A KANSA !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Yin uzuri ga wani abune mai matuqar muhinmanci a rayuwa da kuma inganta zamantakewa. Idan ka kasance mai yiwa mutane uzuri, to, za ka dade ba kaga laifinsu ba, kuma zuciyarka za ta kubuta.
Wannan dalili yasa Imam Ali (A.S) ke cewa;
" UZURI TUSHEN MASLAHA."
To, wannan yana magana ne akan yiwa wani don kubutar dashi, amma kuma yin uzuri don kubutar da kanka abin zargi ne.
Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa;
" NA HANEKA GAME DA (aikata) ABINDA ZA KAYI UZURI A KANSA, DOMIN MUMINI BA YA SABON ALLAH KUMA BA YA UZURI. AMMA MUNAFUQI A KULLUM YANA SABON ALLAH KUMA YANA UZURI."
SHARHI
________
Abinda wannan hadisi ke karantar damu shine, idan kaji mutum na qoqarin kawo uzuri, to, so yake ya kubutar da kansa daga wani abinda ya aikata ko kuma ya kasa aikata. Shine za kaji yana kawo uzuri don a gaskata shi ko kuma a yarda dashi.
To, shi mumini ba ya sabawa Allah ko kuma aikata abinda zai kawo uzurinsa akai.
Misali:-
Saba alqawari,
Aikata laifi,
Cin amana,
D.S
Idan muka kalli wadannan misalai da idon basira za muga duk wanda ya aikata daya daga cikinsu zai yi qoqarin kawo uzuri don a gaskata shi kan hujjar da zai kawo wacce ta hana shi ko sa shi aikata wannan abin. Lalle za muga cewa mumini ba ya aikata irin wadannan abubuwa da za su sa ya kawo uzuri. Saboda haka kawo uzuri abin zargi ne.
Shi kuma munafuqi za ka tarar a kullum mai sabawa Allah ne, sannan kuma za ka sa me shi da yawan kawo uzuri.
Saboda haka abinda yafi dacewa gare ka shine ka kasance a kullum mai yiwa wasu uzuri ba mai kawo uzurinsa ga wasu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925044
Tags:
Tunatarwa