JAMI'AN 'YAN SANDA SUN AUKAWA MABIYA SHEIKH ZAKZAKY A GARIN ABUJA.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates,

 --Idishia Jos.


A yau Talata Jami'an 'Yan Sanda sun kara dira akan 'Yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky (H) wanda suka fito Muzaharar Lumana A Banex Plaza domin Fafutukan neman Asaki Sheikh Zakzaky domin yaje yayi jinya. Sun harbi mutane maza da mata a lokacin da suka dira kan masu Muzaharar. Wannan abin ya biyo bayan diran da suka yi jiya a Federal Secretariat na kasa inda suka kashe mutane sama da 11 a lokaci guda.

A yau daga fara Muzaharar FreeZakzaky nai wuce da 'yan mintuna ba sai ga tawagan Jami'an tsaron Hadin gwiwar jami'an soja, 'yan Sanda da DSS suka bude wuta akan masu  Muzahara. Duk da yake 'Yan uwan sun dake da samun juriya suka raka su da gudu. Mutanen da basa dauke da komai hatta allura don cutar da wasu amma a hakan ake kashe su ake raunatasu.

Daga cikin wadanda aka harba akwai Abokin aikin mu AliAssajjad Ibn Taheer da Sumayya Lamara da dai sauransu. FreeZakzaky ba fashi in har basu saki jagoranmu ba Sheikh Zakzaky.tanks Allah ka kwato mana Sayyid

Ga wasu daga cikin Hotunan WAKIYAN da ya faru


#FreeZakzaky.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post