Hujja Takobin Shi'a. HADISAI AKAN IMAM ALIYU BIN MUSA ARRIDHA (AS).


Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates, tare da -Idishia Jos. 

Wiladan Imam na 8 wato Imam Aliyu Bin Musa Arridha (S), wanda mun kawo kulasa na nasaba din shi. Kuma mukan gabatar da jalsa na A'imma na Manzon Allah (S) domin tana daga cikin hakkokin Manzon Allah akan dukkan musulmi kamar yadda Allah yake cewa " Manzon Allah ya fada mana baya bukatan wani lada na kawo mana wannan shiriya na musulunci illa mu nuna muwadda ga zurkurba din sa".

kuma yazo a hadisi na Manzon Allah cewa " Bawa ba zai taba imani ba, har sai na fi soyuwa gareshi da kan sa, wato babu mutum da imamin sa zai kammala sai yafi son Manzon Allah fiye da kanshi, kuma ya kasance tsarkakan zuriyar Annabi sufi girma da matsayi a wurin mutum fiye da zuriyarsa, kuna ya kasance iyalan gidan Annabi sune masu soyuwa gareshi da iyalinsa, kuma ya kasance zatin Annabi shine mafi soyuwa fiye da zatin kansa, sai mutum ya hada wannan kafin imanin mai imani ya cika.

A wani ruwaya Manzon Allah yana cewa "Kuso Allah sabida abinda yake cigar da ku daga ni'imominsa, ku so ni sabida Allah yana so na, sannan kuso iyalan gidana saboda saboda ni ina son su. Sannan Manzon Allah (S) yana cewa; " Duk wanda ya so mu 'Ahlulbait' to ya gode wa Allah a farkon ni'ima da Allah ya mishi, sai aka tambayeshi menene farkon Ni'ima da Allah ya mishi yake cewa 'Tsarkakan' haihuwa. 

Domin ba Wanda zai so mu Sai wanda yake an haifeshi ta hanyar tsarki ne wato an haifeshi ta hanyar aure. Kaga wannan yana nuna mana cewa masoya Manzon Allah da Ahlulbait dan halal ne, duk wanda yake kin Manzon Allah ko iyalansa to yana nuni cewa ba dan Halal ba ne. Manzon Allah yake cewa a wani ruwaya " Duk wanda Allah ya mishi baiwa da sanin Iyalan gidana Ahlulbait bai dina, sannan yayi wulaya garesu 'Wato ya jibinci al'amarin shi garesu to hakika Allah ya taramai dukkan alkhairi na duniya da lahira'. 

To wannan yana daga cikin dalilai da yasa mukan yi irin wannan jalsa wanda kuma munsha bayani tun lokacin da su malam suka fadakar damu raya irin wannan munasabobibna wilada ne ko na jimami mukan raya tun daga kan na Manzon Allah (S) dana diyarsa dana 'Ya'yansu.

Imam Aliyu Arridha (As) duk abinda ya fada maganar hukunci ne, sannan maganan sa hikima in yayi shiru ilimi ne, duk abinda mutane suka yi sabani akai in anzo wajen shi zai sanar inane mafita. Mafi shaharan lakabobi shine da ake kiran sa shine Imam Ridha, shi a zamanin da makiya da masoya sun tabbata babu mafi alkhairi kamar Imam Aliyu Arridha sabanin sauran A'immai zaka ga makiya suna nuna adawan su garesu. To amma shi Imam Ridha Allah ya mai baiwa a zamanin sa Allah ya mai baiwa da makiya da masoya sun sunyi ittifakin cewa babu wani mafi daukaka mafi tsarkakan daraja, da matsayi da kyawawan dabi'u da halaye irin na Annabawa kamar shi Imam Ridha (As), don haka sai ya zasa  aka ambace shi da Imam Arridha.

Kamar yadda yazo a ruwaya cewa shi babban Imam Ridha wato Imam Musa Alkhazeem koda yaushe yana kiran sunan dansa Ridha ne, kuma in zai yi magana sai yace na fadawa dana Ridha na fada mishi abu kaza amma idan yana a gaban sa, zai ce Abul Hassan alkunyanda yake kiransa dashi.

Daga Hussainiyatu Zakzaky (H) Jos tare da Sheikh Adamu Tsoho Jos.

#FreeZakzaky



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post