Duniya ta wayi gari a ranar Asabar 26-07-2019 da babban labarin cewa wai wata Kotu a birnin Abuja ta HARAMTA Harka Islamiyyah bisa bukatar da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta shigar mata na yin hakan.
Wannan labarin babban abin dariya ne da kuma ban takaici da mamaki a lokaci guda. Domin abun ya zama tamkar Fim din wasan kwaikwayo!!
Na'am, tabbas da gaske Gwamnatin take yi bisa haramtawar tata, kuma bisa ga dukkan alamu za ta zafafa ta'addancin da take yi akan ma'abota Harkar, Amma abin tambayar shi ne, me gwamnatin za ta yi fiye da wanda take yi???
Da a ce a baya gwamnatin Nijeriya mai hankali ce, tana amfani da hankali da lissafi da bin doka da oda game da mu, ba ta kisa sai ta kai kotu an yi shari'a an tabbatar da laifinmu kafin ta kashe, to da sai mu ji tsoron wanna haramtawar tata.
Amma tun asalin asali da ma gwamnati ba ruwanta da doka ko umurnin kotu a kanmu, ta halastawa kanta kashe mu a duk ranar da ta so, a lokacin da ta so, a inda ta so, kuma iya adadin da ta so!!!
Ta kashe mu a titi, ta kashe mu muna kwance a cikin gidajenmu, ta kashe mu a wuraren kasuwancinmu, ta kashe mazanmu, da matanmu, da yara har da jariranmu, kuma tana ci gaba da yin hakan ba tare da tsayawa ko daga kafa ba!!
To meye na fakewa a cikin rigar wata Kotu don ta halasta mata fadada ta'addancin da ta saba yi?? Meye sai ta je kotu?? Tana so ne ta nunawa duniya cewa ita mai bin doka ce?? Ina makomar hukunce-hukuncen kotuna irin wannan da har yau ta take ba ta bi ba???
Da alama har yanzu gwamnatin Nijeriya jahila ce game da mu, ba ku kashe mana Mutum Dubu a kwana biyu kacal ba??? Sai muka dena abin da muke yi?? Sai muka razana muka koma biyayya gareku??
Shin kuna tunanin za ku iya shafemu daga samuwa ne, alhali Allah Ta'ala ya kaddarawa kowace rai adadin tsawon rayuwarta? Ko kuna tunanin za ku iya anfani da mummunan karfin da zai sa mu dena abin da muke yi sarmadan ne?? In kuna wannan tunanin, kun yi kuskure!!
Na'am, ba cewa muke ba za ku iya mummunan kisa na ta'addanci a kanmu ba, za ku iya!! Ba cewa muke ba za ku iya rusa muhallanmu ba za ku iya!! Ba cewa muke mun fi karfinku ba! Lala-lala!!
Abin da muke cewa shi ne, ba ku isa ku karar da mu ba, tunda ba ku kuka halicce mu ba!! Ba ku isa mu yi maku saranda ba! Tunda ba ku muke bautawa ba!! Ba ku isa ku hana Allah zartar da kudurarsa ba, tunda ba ku fi karfinsa ba!! Ba ku isa ku dakile Harka Islamiyyah ta dakilu ba, tunda ba ku kuka samar da ita tun asali ba!!
Tabbace, za mu ci gaba da abin da muke yi iya iyawarmu, kun yi kadan ku canza mu akan haka, ku ma sai ku ci gaba da abinda ku ke yi, wanda shi ku ka iya! Mu zuba mu ga Ni, waye me Nasara a karshe!!? Wa Allah zai kunyata ya tozarta burinsa??
Ya ke gwamnatin Nijeriya bari in tuna miki in kin manta, mu fa 'ya'yan Ashura da Karbala ne!! Jikokin Aliyu Haidar da Sayyid Hamza ne!! Kashe mu bai taba zama kawo karshenmu ba!!
Kun San yadda ruwan sanyi yake dafa Moda?? Kun san yakin da Jini yake Nasara akan Takobi? Kun taba jin inda Kabbara (Allahu Akbar) ke galaba akan Harsashi? Kun taba sanin cewa Ba a Kauda Gaskiya da Bakin Bindiga!!??
Ku binciki tarihi za ku gani, in ba ku iya samu ba, to za ku ga faruwar hakan akan kanku!!
Billahil'Azeem Harka Islamiyyah yanzu aka fara ta a Nijeriya! Ba ku halasta mu tun farko ba, ba ku isa ku haramta mu mu haramtu ba!!
"Kafaa Billahi Wakeelan! Wa Hasbunallahu Wani'imal Wakeel!!!
#FreeZakzaky
Tags:
#FREE_ZAKZAKY